*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*61*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
_*Sister SAFIYYAH HASSAN (UMMEE) Tsakanin keda A.M INUWA Bansan wayafi ƙaunar Sarfraz ba! Saboda haka bansan wa zan ba kyautar wannan page ɗin ba acikin ku biyun, kawai kuyi hakuri ku raba 50 50 😎*_
Aseey kam duk abinda Nawaz ɗin take yi tana sane da ita, sai dai tayita dariya a fakaice tana ganin wautar Nawaz ɗin a fili, wato so takeyi jikinta ya buɗe shiyasa taketa faman bankar magani, Batasan akasin haka bane zai faru.
A maimakon gyaran sati ɗaya sai mummy tace kawai ayi musu na kwana goma, kenan an ƙara kwana uku akai.
Sosai suka chanza kamar basuba musamman hassu da ada take Ƴar mitsitsiya, ita kanta Nawaz haka zata zauna tayita kallon kanta a mudubi, fatarta har wani milk milk takeyi ga wani taushi da santsi da tayi, kuma kullum cikin kamshi take koda bata shafa turare ba, abin har mamaki yake bata, wai itace ta zama haka.
Ta ɓangaren hassu kuwa jiki ya gama buɗewa sosai domin ta zama wata uwar mata duk wani shape ɗin dazai nuna ita macece ya fito fili, kayan ma da akazo mata dasu tuni sunyi mata kaɗan.Ko sau ɗaya Aayaan be taɓa kiran kowaba, wai shi ala dole yayi fushi musamman da suka ƙara kwana ukun nan, itama mummy ganin be kiraba tasan me yake nufi shiyasa itama bata kirashiba ta shareshi kamar yadda ya sharesu tasan ya kusa shigowa hannu.
Manya manyan kwalaye guda uku Aunty khatoume ta shirya musu kayayyakin su aciki, waɗanda suka kama dasu turaren wuta, humrah, dabulun Dilke, coleccher, zuma, Tsumi, garin magunguna, turaren tsuguno dadai sauransu.
Sosai Mummy tayi mata godia ganin yadda yaran nata suka koma gwanin ban sha'awa, har kuɗi Mummyn ta ƙara mata akan wanda ta buƙata domin nuna jin daɗin ta.Komawa gidan su iyayen riƙon mummy sukayi gaba dayansu suka kwana ɗaya domin su gama shirye shiryen su.
Sosai iyayen mummyn suke nuna farinciki, Saida suka tsaida cewa zasuzo Nigeria bayan su mummy sun koma da Wata uku, bayan sun gama haɗa komai ne Sannan sukayi haramar komawa gida Nigeria.
Babu wanda Mummy ta faɗawa zasu dawo saidai saukar su aka gani kamar daga sama, saboda da suka sauka a Airport ɗin kano bata kira driver ba kawai saita samu mota tayi shata zuwa Zaria.
Sosai Mummyn SARFRAZ taji daɗin dawowarsu domin an tsaida Ranar juma'a za'a ɗaura auren sarfraz da hassu Sannan a haɗa tarewar su data Nawaz da Aayaann, kuma mummyn Aayaan kashe watoyinta tayi sanda suka isa sudan ɗin, koda Mummyn SARFRAZ ɗin sau ɗaya suka taba yin waya.
Duk Mummyn SARFRAZ ɗin ta shiga damuwa kada suƙi dawowa gashi an raba iv card ko ina.Shiyasa data gansu daɗi ya kamata kamar tayi mene don farinciki da murna, tsaye tayi tana kallon yadda su hassu suka koma, gani takeyi ma kamar ba hassun ba, sai Nawaz itama da gaba ɗaya ta chanza ta kara cikowa fiye da da.
Ita Aseey ma ba'a magana Domin ita abun biyu ya haɗe mata da gyaran jikin da salo da salasalar da taketa yi.Godiya sosai mummyn sarfraz tayiwa Mummyn Aayaan Kamar zata ari baki, taji daɗin yadda taga hassu ɗin Takoma, domin dama kullum da tausayinta take kwana, tasan cewa idan SARFRAZ ya hake mata ba karamar wahala zatashaba tunda shi mabuƙaci ne, amma yanzu alamu sun nuna zata iya jurewa sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba kafin ta saba sosai.
Haikan ake shirye shiryen bikin saboda wasu daga cikin ƴan uwan Mummy da dadyn sarfraz har sun fara zuwa, saboda ya kama saura kwana huɗu biki.
Sosai Daddy shima yayi ƙoƙarin aikawa kowa da iv card, wadanda kuma sukayi nisa da yawa ya kirasu a waya ya shaida musu.
Har ranar babu SARFRAZ babu Aayaan babu bandi, kuma abin ya fara ba mummy tsoro kada fa suki zuwa Azo ayi biki babu ango domin ko basu zoba baza'a fasa ɗaurin auren ba.

YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...