67&68

2 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*67*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

     Kuka sosai Nawaz ta fashe mishi dashi akan don Allah ya kyaleta kada ya shafa mata zata shafa da kanta.

    Sosai abin yake ƙayatar da Aayaan domin dama Allah ya halicce shi dason mace mai tsoro da kuma ƙarfin hali a wani fannin, kuma Nawaz duk tana dasu.
    Duƙawa yayi ya ɗauki towel ɗin a inda ya faɗi sannan ya rufa mata a bayanta, ajiyeta yayi a saman gado tare da cewa "bari nayi mana order ɗin abinda zamuyi break fast kafin mu tafi, and kuma ki tabbatar kinyi sauri kin shirya kafin in dawo, don inba haka ba saina shirya ki da kaina.

    Yana fita ta miƙe da sauri ta ɗauki doguwar rigarta ta zira, ko bra ɗin ma saita ƙasa tasata,  mai taɗan mutstsika agaggauce sannan ta maida hijab ɗinta, ai kuwa tana gamawa saiga shi ya shigo riƙe da take away guda uku, wata budurwa na biye dashi da flask da disposable cups a hannun ta.

    A saman table ta ajiye Sannan ta fice, shikuwa gabanta ya ƙarasa yana cewa ''Sweetheart anya wannan shirin na Allah da Annabi ne kuwa? Fitata ace har kin gama shiryawa"
    Murmushi dai kawai tayi mishi don bata da tacewa kuma baso take zancen nasu yayi tsawo ba.

   "Zo ki zaɓi abinda kikeso Anan"
   "Ko wanne ma kabani inaso" cewar Nawaz a hankali

   "Nop Gaskiya saikin zaɓa!  if not kuma na baki da kaina"

   Gabanshi ta dawo tare da buɗe duka take away ɗin, farfesun kaza ne a cikin ta farko, ta biyu kuma farfesun naman rago na ƙarshen data buɗe nema taga snacks ne marasa nauyi.

   Shi ta riƙe tare da cewa "wannan nakeso"

    Murmushi Aayaan yayi domin dama yasan bazai wuce shi zata zaɓa ba "to ai nima shi nakeso"

    Miƙa mishi tayi tare da cewa "gashi Ni bari na ɗauki kazan kawai"
    "Nop sai dai mu raba gaskiya" ita dai Nawaz shiru tayi tana binshi da ido domin ta gane neman magana kawai yakeyi.

   Tana kallo ya ɗauki Flask ɗin Tare Da tsiyaya musu mint tea a cikin cups ɗin sannan ya ajiye mata a gaban ta, take away ɗin ya ajiye a tsakiyarsu tare da cewa "to Bismillah muci"

    Batason ta riƙa yawan yi mishi musu domin ta lura kamar hakan yakeso, domin tana farawa sun soma yin jayayyah kenan.

    Kallonta yakeyi ta gefen ido yadda take yafitar cake ɗin kamar ana yi mata dole, tea ɗin ma idan tayi sipping Dinshi saita jima bata kuma kaishi baki ba.

    Take away ɗin da kazar take ciki ta janyo tare da buɗewa, cinya ɗaya ta ɗauka takai bakinta ta gutsura a hankali, sosai tayi mata daɗi yadda taste ɗin be Wuce ƙa'ida ba saboda sosai kamai yayi normal.
   Tama manta da wani Aayann na gurin saida ta cinye cinya guda biyu ta ɗauki ƙirji Sannan ta tuna, basarwa tayi ta ɗan yagi kaɗan sannan a ajiye ragowar tana miƙewa.
   Bathroom ta shiga ta wanke hannunta tare da kuskure bakinta Sannan ta ɗauki towel ta goge.

   Tana fitowa shima ya shiga, haka dai kowa yayi jugum kamar kurame, wayarshi ya ciro tare da sanar da driver yayi warming ɗin mota gasunan fitowa.

   Komawa yayi kusa da Ita ya zauna sannan yace "my beloved Hope Ban ɓata miki rai ba, naga kamar kina fushi dani".

   Babu shiri tayi murmushi "Wallahi Babu abinda kayi min, kawai dai Bansan me zance maka bane shiyasa kaga nayi shiru.

   "Thank God tunda sarauniyata ba fushi takeyi daniba, amma da harna tsorata "

  Dole yasa ta ƙarayin murmushi duba da yadda yayi maganar kamar gaske.
 
    "Let get going, driver is waiting"

   Miƙewa Nawaz tayi tare da duƙawa tana zira takalmanta sau ciki, shima Nashi ya zira yana kallonta yana taɓe baki.
   Cewa tayi "menene?"

SARFRAZ Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang