*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀🎀*
*27*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Yanda ya fita ya bar su haka ya dawo ya samesu a inda suke, baffa ya kalla "baffa babu inda ba'a kaini ba, tun daga kan dakin majinyatan har dakin waɗanda aka kwaso har mutuary babu Nawaz sam..
Fashewa da kuka baffa yayi "shikenan abinda nake fargaban ji Saida naji shi, yanzu shikenan ba'a ga nawwaraba?
Nura ne yace "baffa kayi hakuri insha Allah za'a ganta tunda ai bata cikin gawarwakin.
Amma ce tace "Nura kayi shiru kawai, kaifa yanzu da bakinka kake faɗa mana har asibitin kunje amma bata, to a ina za'a ganta kenan?
Ummin Nawaz tace "baffa da amma kuyi hakuri kawai mu dauki kaddara haka Allah ya tsara, amma mu zauna muna daɗa ɓata wa kanmu rai bashida wani alfanu...
Ni nayi imani da Allah kuma nasan komai ya faru haka Allah ya tsara tun farko...
"Yanzu ke da zamuba hakuri mu kike ba? Allah yayi Miki albarka kuma insha Allah sai hakan ya zame mana Alkhairi dukan mu..
Nura dake gefe yace "Amin" yana goge hawaye..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mota mummy zata shiga dadyn sarfraz Yace a'a bazaki iya driving ba, Nima da nake na miji bazan iyaba, yanzu abinda za'a yi shine Ni zan tuka motar muje tasha
Achan saimu samu driver ya kaimu ya dawo damu inyaso sai ya fadi nawa zamu bashi,
Haka kuwa akayi suka samu driver akan shi zai kaisu ya dawo dasu amma a motar su, sannan suka dauki hanya...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A hankali ta saki Nawaz daga rungumar da tayi mata "ƴata ya sunanki? Amma ta faɗa cikin Hausar ta mara fita..
"Sunana Nawaz" cewar Nawaz a hankali...
"Wow sunanki is special, kada na dameki zo muje in rakaki ɗakin ki ki samu kiyi wanka kici abinci kiyi barci ki huta idan kika tashi sai muje gidanku mu kaiki ko?
"To" Nawaz tace tana mamakin wai takaini ɗaki na, to a ina ya zama nawa?
Bakin wata ƙofa ta tsaya tayi danne danne sannan ta kama hannu Nawaz tasa a cikin sensor ɗin dake jikin kofar take kofar ta buɗe,
Sakin baki Nawaz tayi, murmushi Amma tayi mata "it is your room, kije ki shirya, hannunta taja ta saka a cikin ɗakin sannan ta rufe mata kofar ta koma gurin Aayaan...
Ganinshi tayi ya cika yayi famm, dama tasan za'a rina Domin Aayaan akwai baƙin kishi..
Ƙarasawa kusa dashi tayi "sweet heart Yana ganka haka?
Ko kanajin zazzaɓi ne? Pls kaje kasha magani kayi wanka kaci abinci saika kwanta kafin a kira sallah ko?
Shagwaɓe fuska yayi "mummy wallahi kinsan abinda ke damuna shine kika chanza magana!
Oh oh oh! Aayaaaann Wai har yanzu baza'a Dena kishin nan ba? Yanzu fa ka girma.
Mikewa yayi "shikenan ai dama na lura kina ganinta kika manta dani, Saida kika gama shirya ta sannan kika dawo gurina.
Kawai don Allah yayi ni namiji ke kuma mace kikeso shine za'a riƙa nunamin wariya..
Da sauri ta rufe mishi baki "I'm sorry, ba haka bane, she is our guest, ya kamata muyi comforting ɗin ta, amma daka shigo saika kyaleta a tsaye bakace ta zauna ba baka bata ruwa ba, and kasan wannan ba halin musulmi na kwarai bane...
Kuma Ni na kula tane saboda na wanke laifin da kayi
Murmushi yay "to mum Amma kada ki kuma kyaleni kinji?
"To" kawai tace tana mamakin halin Aayaan da bazai chanzaba...
Dtaga hannu Aayaan yayi sai sannan amma taga bandejin dake hannunshi
Hankalin tane ya tashi ta rike hannun "Aayaan me ya sameka a hannu?
KAMU SEDANG MEMBACA
SARFRAZ
RomansaLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...
