*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*43*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Sosai Hassu take fama da SARFRAZ, domin abin nashi ma kamar ƙara gaba yakeyi, don a halin yanzuma mummy yake cewa Hassu.
Kuma kullum sai dai ya kwanta a cinyarta, tun bandi na hanawa har ya gaji ya Dena.
Zaune Hassu take ta Miƙe kafa sarfraz yana kwance a cinyarta, ita kuma tana Amfani da metilated Spirit tana wanke mishi ciwo, shikuwa sai raki yakeyi akan idan bata denaba babu ruwan shi da ita, kuma bazai sammata biscuits din Shiba idan bandi ya siyo mishi.
Da sauri bandi yace "a'a sarfraz rabani da shirginku babu ruwana domin Nima ba kyaleni kayiba"
Sosai Hassu tayi dariya "babban yaya ayi hakuri muna neman sulhu ne...
Haka dai suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa Kamar yadda suka saba kullum.
Tsintar SARFRAZ sukayi amma Yanzu ya zame musu wani sashi na rayuwa, sun san cewa idan SARFRAZ yaji sauƙi Dole ne ya koma Cikin ahalinshi, to amma yaza suyi tunda ba gida ɗaya suke ba, hassu duk tafi shiga cikin damuwa idan ta tuna cewa wata rana ko tanaso ko bata so dolene su rabu da sarfraz, har hawaye takeyi idan ta tuna hakan....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sosai Aayaann yayi ƙawalliya sannan ya feshe duka jikinshi da turare, cike da kuzari ya shiga babban falourn Colonel Yana kwalawa su Naufal da fudail kira.
Mamakine ya kama Colonel wanda shigowar shi kenan "son what causes the sudden change? Wow gaskiya naji daɗi my real Aayaan is back.
Dariya Aayaan yayi "sir ka bari in dawo zan faɗa maka abinda ya faru yanzu zamuje shopping ne dasu fudail.
"A lallai! Masha Allah haka nakeso na riƙa ganinka kullum cikin karsashi da kuzari.....
Su Naufal ne suka karasa suna murmushi "Auncle mun shirya mutafi.
Sallama suka yiwa colonel Sannan suka fita daga faloun zuwa harabar gidan.....
Ɗaya daga cikin securities ɗinshi yayiwa magana akan ya tuka su, sannan Dukansu suka shiga baya suka zauna
Wayarshi ya ciro yana murmushi sannan ya daɗa buɗe inbox yana daɗa karanta message ɗin da Nawaz ta turo mishi, daɗi sosai yakeji, kuma sosai zuciyarsa take ƙara mishi kwarin gwuiwa akanta yanzu.
Samun kanshi yayi dayi mata reply da.
*_Wa'alaikis salaam matar Aayaan_*
*_ina lafiya lau Alhamdulillah kuma kema ina fatan kin yini lafiya, ya Bayan rabuwa?_* *_wato bakima san abinda kika minba ko?_*
_*Shikenan babu komai nakusa dawowa, ki tanadar mini tarba me kyau*_
_*Mai sonki ba abokin faɗan kiba AAYAANN*_
Bayan ya tura mata sai murmushi yakeyi, bai ankara ba yaji su fudail suna cewa Uncle "munzo sharaton mall ɗin"
Namfa ake yinta! Duk Abinda hannun shi yakai sai dai ya saka a basket, yayi siyayyah ta wuce tsammani, suma su Naufal sai jida sukeyi saboda dama yace musu su zaɓi duk abinda suke so....
Haka aka cika Boot dam da kaya sannan seat din baya shima haka, dole suka koma daya motar securities ɗin da suke binsu a baya domin gurin bazai isaba.
Bayan sun koma gida ne Aayaan yasa securities suka kwashi siyayyar su Naufal suka kai musu ɗaki, inda shi kuma yabar nashi a Cikin motar...
Sosai colonel yake farinciki domin ya lura Aayaan ya warware sosai, sai dai besan silar warwarewar tashi ba.
Kallon Aayaan yayi Sannan yace "Son zo ka zauna a kusa dani! Zamuyi magana.
VOUS LISEZ
SARFRAZ
Roman d'amourLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...
