*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*57*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
"Ƙaniyarka Sarfraz! Nace ƙaniyarka!!, Kanada hankali Kuwa? Kallon Aayaan dady yayi sannan yace "Wai Aayaan nikam kodai yaron nan ya samu wata matsalar ne a kwakwalwa dadilin ciwon da yayi?
Kasancewar Aayaan ɗin nada shekaru kuma ya karanci rayuwa sai ya zamana koda ka kalleshi bazaka taɓa gane yana cikin tashin hankali ba, amma a baɗini kuwa shikadai yasan Yadda zuciyarshi ke tafarfasa.
"Daddy Allah duk gwaje gwajen da za'ayi anyi kuma an tabbatar kwakwalwar shi ta koma normal babu wata matsala."Eh Lallai! kenan iskancine yasa yake ƙunduma min ashariya a cikin gida, to Wallahi Sarfraz ka kiyayeni! saboda kai ɗan Gwal ne shiyasa mijinta zai saketa kai ka aureta, kuma naga ai Allah dakanshi yace saki halal ne amma bayasonshi.
Wato saboda wani shirmen banzan ka sai ayi abinda Allah bayaso Koh?
Aseey kam haushin sarfraz ne ya kamata, "wato a saketa! to sannu ɗan lu'ulu'u, idan ba lu'ulu'u ba taya Muna murnar munsamu gwarzuwa kazo zaka ja mana jarfa" abinda Aseey ke tunani a zuciyarta kenan, daga karshe ma tace "ka mutu mana! Ka daɗe baka mutunba, ya gama wahala dakai shine zakazo kuma kana ƙunduma mishi ashariya, don kaga yarinya gwanin kyau, ga komai da komai shine kake ganin da kai ta dace".
Mummyn sarfraz ce tace "haba fabulous meye kuma na zagi bayan kana kallon manya a gabanka, ai Nasha kai me hana wani ne idan kaji yanayi".
Ita kuwa hassu ji tajeyi kamar ta zunduma ihu, yanzu Sarfraz wata zai aura ya manta da ita kenan, shidai bandi zaune yake yana kallon ikon Allah.
Mummyn Aayaan kam tayi nisa cikin tunanin yadda zatasa Aayaan ya saki Nawaz ɗin salin alin, domin ita kallon sarfraz takeyi a matsayin mumtaz ɗinta, kuma duk duniya babu Abinda take ganin bazata iya yiwa mumtaz ba.
Ɗan ɗaga murya Aayaan yayi "sweet bro dawo, zo gurina, ka manta alƙawarin da mukayi nida kai? To yau zan fara amfani dashi.
Takowa Sarfraz yayi ya dawo gaban Aayaan ya tsaya.
"Ka tabbatar kana ƙaunar Nawaz? kuma zaka iya zama da ita har ƙarshen rayuwarka? Aayaann ke tambayar Sarfraz yana kallon Cikin idonshi."Eh yaya, wallahi ina matuƙar ƙaunarta! Sarfraz yace shima yana kallon Aayaan ɗin.
Miƙewa Aayaan yayi Tare Da cewa "Aunty Aseey zo muje, kaima Sarfraz tawo."
Mummyn Sarfraz ce tayi sauri ta miƙe Tare da cewa "kul Aayaan! Kul nace! Kada ka sake kayi abinda bashi bane, kadaiji na gaya maka.
Shima daddy cewa yayi "laillai Aayaan! Ina kallonka a matsayin me hankali, taya zakayi abinda Allah ma zaiyi fushi damu?
Kwantar da kai Aayaann yayi Tare Da cewa "Dad and mum pls trust me! I will never do something that all of us will regret, but I'm just trying to do something that will be a way to both of us.
Shiru kawai duka sukayi basuce komai ba, amma zuciyarsu na ɗan bugawa kada fa Aayaann ya saki Nawaz, ita kuma Mummy addu'a takeyi akan Allah ma yasa Aayaan ɗin ya haƙura da Nawaz ɗin ne.
Fita harabar gidan Aayaan yayi, Aseey da sarfraz suna biye dashi a baya har zuwa wani gefe inda aka Wadata da hasken lantarki duba da Lokacin dare yayi sosai "SARFRAZ inaso ka saurareni dakyau, yanzu zansa Aseey taje ta tawo da Nawaz nan gurin, Ni zan matsa inda bazata ganni ba.
Inaso ka tambayeta shin zata iya aurenka ta zauna dakai a matsayin miji? Ni kuma wallahi nayi maka alƙawarin har dai tace eh to Wallahi saika aureta duk wuya duk rintsi.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
SARFRAZ
Любовные романыLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...