75

3 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*75*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

   Sweetheart pls ki barni zan duba jikinki ne, babu Abinda zanyi miki.
   Ɗan sakin jikinta tayi amma still Idonta a rufe gam, tanajinshi ya buɗe cinyoyin ya duba "Alhamdulillah!!! Allah na gode maka, gaskiya Allah yanasona da yawa"
    Ɗagota yayi yana cewa "sweetheart bakiji ciwo ba, dama inata tunanin ta yadda zan yi miki stitching saboda tausayinki nakeji, ace duk wannan wahalar da kikasha bazata tsaya iya nan ba,  gashi kuma bazan iya barin kowa ya ganin mini guri mai matuƙar muhimmanci a rayuwata ba.

    Duk Abinda yake faɗa jinshi takeyi kamar yana yi mata tatsuniya ne, ya za ayi ma Yace mata bataji ciwo ba? Duk wannan Uwar azaba da zugin da takeji a cikin jikinta ta ina suke zuwa?

    Zuwa wannan lokacin zazzaɓin ya riga yaci ƙarfin shi amma jarumta ta hana ya nuna, don wani irin sanyi ne yake ratsashi tako ina ga jiri Jiri da yake gani, ajiyeta yayi Sannan ya shiga bayin ya haɗa ruwan zafin ɗan dai-dai Yadda bazai chutar da itaba, farincikin shi ɗaya ma da bataji ciwo ba.

    Komawa yayi ya ɗauko ta ya nufi Cikin bayin da ita, cikin dabara ya sakata cikin ruwan zafin, ai kuwa take ta saki wata Uwar ƙara, babu shiri Aayaann ya cireta daga cikin ruwan yana cewa i am sorry dear, taɓa ruwan yayi don tabbatar da yanayin zafin shi, NORMAL yaji shi  amma yasan ita dole taji zafinshi saboda ciwon dake jikinta.
    Ƙara sirka ruwan yayi sannan ya ɗauke ta chak a kirjin shi, shiga cikin ruwan yayi rungume da ita, har zata fara wani ihun taganshi acikin ruwan shida ba ciwo gareshi ba, hakanan ta daure duk da Irin azabar dake ratsata, gaba ɗaya gashin kanta da goshinta sun jiƙe da gumi, sosai tausayinta ya kamashi domin yasan dole taji zafi kuma shine silar komai.

    Saida ya chanza mata Ruwan so uku sannan yayi mata wankan tsarki tare dana sabulu, goyata yayi a bayanshi sannan ya fita zuwa bedroom ɗin, yaye zanin gadon yayi ya ajiye a gefe sannan ya ƙarasa ya buɗe wardrobe ya ciro wani bedsheet ɗin yayi spreading dinshi.
    Kwantar da Nawaz yayi ya gyara mata kwanciya Sannan ya janyo duvet ya rufeta dashi, bayin ya koma inda shima yayi nashi wankan, koda ya fito Lokacin Nawaz ta riga tayi barci, kissing ɗinta yayi a goshi tare da cewa "I Love You sweetheart! You mean everything to me" sannan ya ɗauki jallabiyarshi yasa tare da matsawa saman carpet ya tada kabbara.
        Sallah yayi tayi raka'a bibbiyu har saida yaji jiri na neman kada shi ƙasa sannan ya haƙura ya zauna ya fara zuba addu'oi, sosai yayiwa Allah kirari tare da gode mishi bisa baiwar da yayi mishi na bashi Nawaz a Matsayin mata, kuma dukda Kasancewar ta daɗe batayi Aure ba ya sameta a cikakkiyar budurwa Abinda yayi ƙaranci a zamanin yanzu kenan, addu'oi yayi musu sosai akan Allah ya basu zaman Lafiya ya albarkacesu da ƴaƴa na gari.
       zuwa lokacin zazzaɓin yaci ƙarfin shi, kasa tashi yayi Daga inda yake, Sai kawai ya  koma  ya kwanta a Saman carpet ɗin Tare da curewa waje ɗaya saboda sanyin da yakeji yana Ratsa duka sassan jikinshi zuwa ɓargonshi.

     Kafin wani lokaci jikinshi yayi wani irin zafi rau, haƙoranshi har haɗewa da juna sukeyi, sanyi sosai yakeji amma ya kasa tashi ya ɗauki bargo ya rufa.

    Itakam Nawaz tanata barcinta wanda bata samu tayi da dare ba, sai bayan kamar awa biyu wani irin fitsari ya tasheta  daga barcin da takeyi, koda ta tashi zaune bataga Aayaan kusa da ita ba, Hannu tasa ta janyo towel ɗin daya zame daga jikinta sanda tana barci ta ɗaura Sannan a hankali ta miƙe tsaye, takawa ta farayi a hankali Amma tana ɗan jin zugi a HQ ɗin ta, a haka ta daddafa ta shiga bathroom ɗin tayi fitsarin ta fito, ga mamakin ta ganin Aayaan tayi a ƙudundune saman carpet yana rawar sanyi, sannan tanajin gunjin numfashinshi irin wanda zazzaɓi yayiwa mugun kamu.

    Neman zafin da takeji tayi ta rasa, ita kanta Batasan sanda ta isa gareshi ba Tare da ɗago kanshi tana cewa "yaya meya sameka?
     Rau haka taji jikinshi kamar garwashin wuta, rasa yadda zatayi tayi sai kawai ta fashe da kuka tare da cewa "nashiga uku! Don Allah meya sameka?

SARFRAZ Место, где живут истории. Откройте их для себя