🎀🎀 *SARFRAZ*🎀🎀
*19*
*✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*
Inaso kaje gidan hajiya Bilki ka amso mata atampopi da lace dinkakku koda material ko shadda,
Saika wuce kasuwa ka siyowa su inna Suma atampopi dadai sauran abun Bukata, yanzu dai zauna in gama rubutamaka.
Zama yayi a Gefen mum Don babu yanda ya iya, saboda shi yasone yaje d'akin mummy yaga Nawaz saboda bega giftawartaba ....
A Saman table ta dauki jotter, na Nawaz ta fara rubutawa sannan ta rubuta Wanda za'a kaiwa y'an uwa.....
Cewa SARFRAZ tayi biyoni d'akin daddyn ka...
Kumbura baki Yayi sannan yabi bayanta, suna shiga mum tacewa daddy "kaga abubuwan dana rubuta sunyi?
Amsa dad yayi ya Duba "Eh sunyi amma sainaga baki wani rubutawa ummanki abubuwa da yawa ba, gaskiya Ki kara.....
Murmushi tayi "to Alhaji nagode Allah ya saka da Alkhairi!
D'aga mata hannu Alhaji Yayi "dakata! Wai so nawa zance miki ki denamin godia ne?
Gaskiya banso ki dena.
Murmushi mummy tayi "to Allah ya huci zuciyarka, kuma naga ai duk Wanda bai iya godewa mutumba bazai iya godewa Allah ba.
SARFRAZ ne yace mummy bari nazo....
Da sauri mum tace "A'a babu inda zaka, amshi takardar nan kawai ka tafi yanzu, inyaso saika fara zuwa gidan hajiya Bilki tukuna....
Amsar takardar yayi ya fita, dad ne ya kwala mishi Kira "fabulous zo mana.....
Dawowa SARFRAZ Yayi Amma ranshi a had'e, "gani dad"
Murmushi dad yayi "kafita banbaka master card 💳 ba, to dame zakayi siyayyar?
Dad akwai kudi a account d'ina ai.....
Hmm wannan ai nakane, yanzu amshi wannan saikayi siyayyar, idan kagama komai saika ajiyemin a drawer....
Amsa yayi "to dad nagode "
Girgiza Kai dad yayi "kaima mummyn taka ta koya maka Dabi'ar ta ta godia koh?
shi dai SARFRAZ fita yayi, parking space ya wuce ya shiga mota ya fita daga gidan, daka kalleshi zaka gane yana cikin damuwa......
Bai wuce ko inaba sai gidansu ABDUL (abokinshi na islamiyya)
yana shiga kuwa yaci Sa'a, dashi ya Fara haduwa.......
D'akin ABDUL suka koma, ganin ABDUL Yayi duk shashin bulala a jikinshi Dayake singlet ce a jikinshi......
Mamakine ya kama SARFRAZ 🤔😳, Kai kuwa ABDUL waye yayi maka wannan danyen aikin?
murmushi ABDUL Yayi "SARFRAZ Allah yasoka kabi malama Nawaz ka tafi gida ranar nan, wallahi dabansan yanda jikinka zaiyiba barin gaka fari!
Ai in takaice maka zance, katuna sanda zaku fita ai malam bilal ya shigo ajinmu koh?
SARFRAZ ya daga kai alamun "eh
Abdul yaci gaba da cewa" to wallahi daya fara dukanmu Kai kazata Allah ne ya aikoshi..
domin maganar danake maka yanzu haka Zainab da uthman suna asibiti harda Karin ruwa akayi musu......
tausayine ya kama SAFyRAZ ganin irin yanda y'an ajinsu suka shiga halin ha'ula'i kuma duk sabo dashi.....
cewa Yayi "ABDUL amma ya fad'a muku abinda kukayi mishi.....
BINABASA MO ANG
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...
