*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*53*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji ✍️*
Sam SARFRAZ beji zuwan ƴan sandan ba sai ganinsu yayi a gabanshi, ai kuwa duka suka sauka a motar tare da zagayeshi.
Daya daga cikin su ne ya kama hannun sarfraz ɗin tare dasa mishi handcuffs, tasa ƙeyarshi akayi har cikin mota sannan aka tasa su bandi da Hassu, sosai SARFRAZ yake roƙonsu akan su bari ya kira yayanshi, amma fir Yan sandan suka ki yarda.
Haka SARFRAZ yanaji yana gani aka tafi dasu, wasu daga cikin turawan kuwa sunata dariya, dama akwai waɗan da Sarfraz ɗin ya addaba a cikinsu.
Haidar ne shima tafe akan titin domin komawa gida saboda yau beda shifting ɗin rana, har ya gifta motar Yan sandan sai kuma yayi reverse ya juyo saboda wasu ya gani aciki kamar su Hassu...
Da gudu yabi motar, ai kuwa su ya hango a ciki, tsaki yayi "wallahi idan Aayaan bezo ya maida yaron nan gidaba wallahi nasan tsaff zaisa nima a koreni a ƙasar nan, ko yanzu me yaje ya aikata Oho..
Ƙarawa motar gudu yayi tare da shan gaban Yan sandan, parking driver ƴan sandan yayi tare da dirowa daga cikin motar yana jaraba.....
Ganin haidar da yayi sai ya dena fadan ya fara tambayar shi meyasa ya tsare musu hanya? Saboda yasan haidar ɗin, kasancewarshi babban likitane a fannin abinda ya shafi ƙwaƙwalwa.
Hakuri ya fara bashi tare da cewa laifinshine daya manta be rufe SARFRAZ a cikin gida ba."Kamar ya laifinka? Bayan mu mun kama shine da laifin karya mana dokar hanya!
"Eh yallabai, abinda yasa nace maka haka shi ɗin majinyaci nane, kuma yanada matsalar kwakwalwa ba'a saiti yakeba sha tara sha tara ne.
Girgiza kai ɗan sandan yayi Sannan yace tabbas da alama, don Nasan me hankali bazaiyi wannan abin da yayi ba, amma don Allah ka riƙa kula dashi sosai kada wata rana yaje yayi abinda zai Cutar da kanshi..
Sosai haidar yayi mishi godia tare da cewa in'sha Allah zai kula dashi dakyau.
Sakinsu akayi aka cirewa SARFRAZ handcuffs ɗin sannan aka fito Musu da kenen su, su kuma Police ɗin suka tuƙa motar su sukayi gaba.
Suna tafiya haidar ya fara yiwa SARFRAZ faɗa "kai bakajin Magana Koh? Nayi maka nasiha nayi nayi amma kaƙi ɗauka, wai ya kakeso nayine?
So kake a koreni daga garin ko? Yanzu in banda abinka ya za'ayi mutum uku suhau keke guda ɗaya, ko tsoron lafiyarku bakwa yi ko?Shidai SARFRAZ tunda haidar ya Fara fada ya duƙar da Kai yayi shiru kamar faɗan yana ratsashi.
Hassu haidar ya kalla Sannan yace "kema kina matsayin mace amma kina biye musu Koh? Kici gaba idan wata Rana suka karyaki ke kika sani..
Keken ya gungura ya sakata a Mota sannan yace musu " ku Wuce ku shiga mota mu koma gida.
Sif sif suka shige seat ɗin baya suka zauna suna raba idanuwa.
Koda suka isa gida a waje sukaga Madam haidar itama ta fito zata shiga Mota.
Da sauri ta ƙarasa gunsu tare da cewa "sweetheart Ashe ka amso su? Wallahi yanzu Florence yazo yake cemin wai Yan sanda sun kama baƙi na sun tafi dasu. Bakaji zuciya taba, Yanzu haka na shirya ne zan tafi station ɗin.
Cewa yayi "Wallahi basa ji sam, ace kullum daga wannan sai wancan Nidai na gaji Gaskiya, Aayaan Zan kira wallahi yasan yanda zaiyi su koma gida Kafin susa a koremu gaba ɗaya, yanzu haka da kika ganni dasu karya na shararawa cp ɗin shiyasa har ya bani su cikin Salama, amma da Wallahi sai munsha wuya zai bamu su.

ESTÁS LEYENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...