7&8

10 1 1
                                    

🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀 
7

Written by MATAR RAHEED

Idon safraz yayi ja,  Yana Kallonta amma yakasa magana...

    Sakamakon wani takaici daya rufeshi "wai ace Kamar shi mummy bata yarda dashiba.....

    Cewa tayi "wato ka maidani mahaukaciya koh?
  Inata magana amma kayi banza Dani koh?

    Wani siririn Hawayene ya zubomai a ido d'aya,  "tunani yake azuciyarshi,  Dana bar yarinyarnan a wajensu da Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita....  Wai kuma na taimaketa abin kuma ya juya kaina...

    But I know Allah wouldn't allow this to happen cuz i did it with a good intention.....

    Mummy ce ta dawo dashi daga tunanin dayakeyi "wato safraz munkai gejin dazan rika yi maka magana kanajina kuma kayi banza Dani koh?

    Tunda yaji tace safraz yasan ranta Yayi mugun baci, domin bazai iya tuna last data Kira tsuran sunan shiba......

   Ahankali ya iya had'a Kalmar "yi hakuri mummy"
   Murmushin takaici mummy tayi "Hmmm hakuri ya rage naka ai,

   Yanzu fad'a min a Ina ka daukota? Kuma wacece ita?

dakyar safraz yace "bansan taba kuma bansan ko wacece ita ba......

   Hanyar d'akin shi mummy tayi "bari ni naje na tambayeta dakaina kaga saitamin bayani.....  Sannan ta shige d'akin .....

    Nitsewa safraz yayi a cikin sofa, gaba d'aya zuciyarshi na mishi tukuki,  saboda baiyi abinda ake tuhumarshi akaiba....  Kuma mai  tuhumarma mummy....

    Tarar da ita tayi tana yinkurin tashi,  da alamu tanajin jiki....
   Taimaka mata mum tayi ta Mike....

   A Gefen gadon ta zauna ta Dafata "Sannu kinji "
     Ya jikin naki?
A yanayin tsoro nawaz tace "Dan Allah a Ina nake?

   Cewa tayi kada ki damu babu abinda zai faru dake kinji?
  D'aga Kai nawaz tayi alamun "to"
  
   mummy ce tace zaki iya magana 'yata?
  
    Ahankali NAWAZ tace "eh zan iya"
     
     please inaso duk abinda zan tambayeki ki fad'a min gaskiya kinji?

   nawaz ta d'aga Kai had'e da cewa "to "

    Mummy ta gyara zama tace "my dear inasone ki fad'a min abinda ya faru Wanda kika Sani a matsayin abinda zaki iya tunawa na karshe..

   Nawaz tace to "Amma Dan Allah sammin ruwa nasha!
   Dasauri Ta Mike ta fita falour tayi dispensing din ruwa a dispenser. sannan ta koma ciki da  sauri

   Mika mata tayi "gashi "
   Amsa tayi Tasha rabi sannan ta ajiye ragowan a Gefen bed side drawer...

   Abinda zan iya tunawa shine Daren jiya
   Na fito daga bayi na shiga d'aki kawai sainaga Maza biyu suna mana dubedube.
   nace su waye ?
Sainaga sun nufoni zasu kamani  danaga da gaske ni sukeso su kama shine Nayi Waje da gudu..
   Haka Suma suka yi ta  bina a baya tundaga layinmu har saida mukakai captain street,  sannan ne suka kamani....
    Dayan ya rike hannuna da karfi yanda bazan iya kwacewaba, shi kuma Dayan ya Fara yagamin Riga...
    ganin Dagaske zasu wulakantani yasa na ciji Dayan a hannu, dayaji azaba shine ya sakeni...
    na juya da gudu naji nayi Karo da wani abu mai karfi to Daganan bazan iya tuna komaiba .....

    mum ce tace "ko zaki iya siffantamin kamannin wadanda suka biyoki..
   NAWAZ tace "Eh nasan d'aya ma  domin yana zuwa gurin uwar gidan abbana kuma sunanshi Tasiu, Amma bansan Dayan ba,  kuma dukansu daka kallesu zaka gane y'an shaye shaye ne......

SARFRAZ Where stories live. Discover now