89

4 1 0
                                    

*🎀 🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

  *89*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

   Sakin labulen ɗakin Abban Nawaz yayi ba tare da ya damu da halin da yaga su Jamila ba, Domin yanzu duk wani abu da ya shafi Umma baƙinshi yake gani.

    Cikin ikon Allah ummin Nawaz ta samu fauziyyah ta farfaɗo dakyar, Ruwa ta bata tasha sannan ta koma gurin jamila inda inna talatu ke tunanin sai anje asibiti Domin dukkan alamu sun nuna naƙuda takeyi kuma gashi cikin be isa haihuwa ba.

   "Inaga fa sai anje an taro adaidaita mu kaita asibiti kada wani abun ya faru, saboda jinin da yawa yake zuba gashi ta fara fita daga hayyacinta"

   "To bari na samo" cewar ummin Nawaz tare da hanzarin fita daga ɗakin

  "Kada ki sake ki fita daga cikin gidan nan" Suka jiyo muryar Abban Nawaz a kausashe.

   A zuwa wannan lokacin zuciyar umma ta gama bushewa gaba ɗaya, jira kawai take taji ance mata Jamila ta mutu, tana inda take a zaune domin babu ƙafa kuma koda da kafar bata tunanin zata iya tashi saboda tashin hankalin da take ciki, hannuwanta kawai tasa ta rufe fuskarta tana jero istigfari a cikin zuciyarta.

  Tsaye ummin Nawaz tayi tana ta'ajibin wai ya akayi Muhammad ɗinta ya zama haka ne?  shirin bashi haƙuri takeyi saboda kada wani abu ya sameta. "Abban Nawaz don Allah kayi haƙ....."  

"Sanda tayi cikin tayi shawara dake ne da yanzu kike nemar mata mafita?"
  Maganar data ƙara dukan Jamila kenan jikin nata ya ƙara rikicewa..

     Itama Inna talatu  sai ta fito da nufin su haɗu su ƙara bashi haƙuri kila ya sauya ra'ayinsa, kafin ta ƙarasa gurin da suke tsaye ma ya shige ɗaki ya turo ƙofa.

  Cirko cirko sukayi a bakin kofar suna tunanin mafita, "Rahma kinada garin kanumfari da garin Cinnamon" Inna talatu ta tambayi ummin Nawaz

  "Eh inada su" ummin Nawaz tace tare da nufar falonta don daukowa
   "Ki haɗo da sabuwar reza nasan bakya rabo da ajiyewa" inna talatu tace da ƙarfi yadda ummin zata jiyota

   Da sauri ta fito riƙe dasu har tana neman yin tuntuɓe tsabar tashin hankali.

   A inda suka barta Anan suka sameta, gaba ɗaya jikinta yayi laushi, "Umma inaga fa sai dai muyi mata dabaru irin namu na gargajiya don inba haka ba zamu iya rasa ta" inna talatu tace tana ayiye hijabinta a gefe

    "Kuyi mana, Allah ya taimaka" Abinda umma ta iya cewa kenan ta maida hannunta ta rufe fuskarta.

    Kofi ummi ta dauko ta ɗebo ruwan dumi ta kawowa Inna talatu, amsa tayi ta juye Garin kanumfarin da na Cinnamon ɗin ta jujjuya saboda ya jiƙu da wuri.
   Fita ummi tayi ta ɗauko muciya a kitchen saboda itama zasu bukace ta, dago kan jamila tayi ta kafa mata kofin a baki tare da cewa sha.

   Tsabar azabar da jamilan take ciki yasa bata ji daci da yajin kanumfarin ba ta riƙa kwankwanɗa har Saida ta shanye shi tass, jira sukayi na Tsawon minti goma amma shiru babu wani yunkurin tawowar ɗa daga cikin.

   Ummi ce ta mikawa Inna talatu muchiyar tace "inaga fa sai anyi amfani da muciya kada karfinta ya gama ƙarewa, buɗe bakin jamilan ummin Nawaz tayi ita kuma Inna talatu ta tura mata muciyar chan cikin makogoronta, cikin ikon Allah kakarin da tayi sai ta fara yunkuri, bata cire muciyar ba saima ta ƙara turawa ciki yadda za'a samu tayi yunkurin mai karfi.

   Allah ya taimaka har jinjirin ya fara tawowa, gyara kafafuwanta ummi tayi don ta duba taga ko jikin nata ya buɗe, amma cikin rashin Sa'a ɗan ya sako kai har ana ganin gashin kanshi amma jikin a tsuke yaƙi buɗewa.

   Da sauri ummi ta fita zuwa dakinta ta ɗauko man zaitun da man kwakwa, sosai take zubawa tare dasa hannunta tana bude cikin jikin jamilan ko Allah yasa yaji santsin man ya buɗe, amma ko gezau yaƙi buɗewa, babu yadda basuyiba amma abu yaci tura.
   "Ina rezar nan take" inna talatu ta tambayi ummin Nawaz

  Miƙa mata rezar ummin Nawaz tayi tana jin zuciyarta na karyewa saboda tasan yanka ta talatu zatayi tunda ta kasa haihuwar da kanta,
  Aikuwa dai abu babu daɗi saida ta ƙara ta har guri biyu sannan aka samu kan ɗan ya fito, cikin dabara suka taimaka jinjirin ya gama fitowa..

    Saida ya gama fitowa suka lura baya numfashi, gashi dama ɗan karami ne sosai, jijjigashi suka riƙa yi ko suma yayi amma daga baya sai suka gane ya mutu ne, wato wahalar da yasha a ciki yasa ya mutu kafin a haifeshi.

   Inna talatu ce taciro mahaifa tare da kwashe mata jinin cikin marar ta sannan tasa wani zani ta tare jikin jamilan dashi, ko motsi kwakkwara ta kasa illa idonta da yake abude ne kawai zai shaida maka tana raye bata mutu ba.

   Shirun fauziyyah ne suka ga yayi yawa, koda ummi ta ƙarasa kusa da Ita ta duba sai taga ashe ta kuma sumewa ne, cikin tashin hankali ta fita ta ɗebo ruwa ta fara yayyaafa mata....

*(Jama'a kun dai ga Yadda jamila tasha wuya, yau da ace Aure tayi ta samu cikin, ana farin ciki za'a kaita asibiti kuma ayita nan nan da ita, kowa yana cikin tashin hankali har saita haihu, ballantana ma mijinta, idan yanada hali ma har kyauta zaiyi mata bayan ƙaunarta da zai kara, ga abinci me kyau da gina jiki da za'a tanadar mata tun sanda ta samu cikin ta yadda idan tazo haihuwar Allah zai taimaka naƙudar tazo mata da sauƙi)*

   *ALLAH KASA MUFI ƘARFIN ZUCIYAR MU, KUMA ALLAH KA ƘARA NESANTAMU DAGA KAIDIN SHAIDAN DA SHARRINSA (AMEEN)*

  °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

   Bin bayanta colonel yayi, koda ya shiga ɗakin be ganta ba sai kawai ya kwantar da muhsin ɗin yaja musu Kofar ya fito ya koma falon.

   Anan ya samu Aseey zaune a dining tana jiranshi, ta fara serving dinshi kenan saiga su Naufal sun fito kowa da rabin ƙatuwar kaza a hannunsa yana yaga "ina kuka samo kaza ƴan-biyu" goggo ta tambayesu miyaun ta yana tsinkewa

  "Yaya Captain ne ya bamu" Naufal yace yana ƙarasawa dining din shima.

   Kafin yace wani abuu tuni muryar Fudail ta karaɗe ɗakin "Aunty pls Nima a zuba kin better ɗin da aka haɗawa Daddy"

  "Kaji ɗan baƙin ciki" abinda Naufal yace kenan yana balla mishi harara "wato saboda kaga na riga ka shine zaka yimin katsalandan Koh"

    Daddy ne yace "kuci gaba kunsan sauran ai, tunda ku ako ina kuma a gaban kowa ma saikun raba hali"

   Shiru duka sukayi ba tare dasun shirya ba

   Goggo ce tace "wai Ni kam gidan nan sai naga yana komawa kamar ba gidan zaman makoki ba"

   "Eh goggo ai kinsan idan mutum ya daɗe yana jinya mutuwarshi bata cika damun Mutane ba kamar wanda ana tare da an rabu ace wane ya mutu" cewar kanwar marigayiyar

   "Ai kuwa dai ai Aunty tasha jinya wallahi, Allah dai ya jikanta yasa kankarar zunubai ne" cewar yayar Colonel tana miƙewa

°°°°°

    Sosai Nawaz tayi barci domin sai bayan la'asar ta tashi, samun kanta tayi rungume cikin jikin Aayaan shima yana barcin shi peacefully.
   Motsin data yine ya tashi Aayaan, da sauri ya tashi ya zauna tare da cewa "sweetheart kin tashi? Ya jikin naki? Fatan babu inda yake miki ciwo Koh?"

  Ɗaga mishi kai tayi kawai domin bata sanma tambayar da zata amsa mishi ba,
   Ɗaukar ta yayi ya kaita bathroom ya wanke mata baki shima ya wanke nashi sannan ya dawo da ita ya zaunar da ita a saman bed.
  Duka abubuwan daya siyo mata ya buɗe mata tare da cewa "Ranki ya daɗe Bismillah!.

    Sosai take cin kazar kamar ɗan gudun hijrar daga fi sati be ga abinci ba, tana gama ci zata sha madara sai amai ya kwace mata, tashi tayi da gudu da nufin ta shiga bayi amma Aayaan yayi saurin riƙe ta tare da rungumeta "dear kiyi anan kawai..
   Tun kafin ya ƙarasa tuni aman ya tunkuɗo waje, duk jikin Aayaan ɗin ya ɓaci har wajejen wuyanshi, sam shi ba wannan bane ma ya dameshi illa yunƙurin da yaga tana ƙara yi, sai faman jera mata sannu yakeyi kamar wadda za'a shiga da ita ɗakin haihuwa..

   *MASU KARATU KO A IYA NAN AI MUNGA ILLAR SON ZUCIYA, JUST KU KWATANTA JAMILA DA WAHALAR DA TASHA, NAN KUMA GA NAWAZ DA YADDA AAYAAN KE  KULA DA ITA*

MATAR RASHEED ✍️

SARFRAZ Where stories live. Discover now