*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*78*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Yayi yayi ta faɗa mishi menene amma sai tace babu komai, daya matsa mata sai ta fashe mishi da kuka tana cewa "yaya don Allah kada ka rabu Dani, Wallahi na dena yi maka musu, kuma duk abinda kakeso zanyi maka"
Lallashinta ya fara yana cewa "dear Nothing will happen In'sha Allah, we will live together, ko a cikin aljannah ke nake fata ki zamo min mata, babu abinda zaisa na rabu dake in'sha Allah "
"Promise bazaka barni ba"
"I promise to be together in'sha Allah, tare zamu raini cikinmu, kuma tare zamu haihu don bazan bari wani ya gan mini Naƙudar mata ta ba"
Shiru Nawaz tayi domin maganar da Aayaan yayi ta karshe ta bigeta, kenan ciki gareta shiyasa komai nata ya canza?Farin ciki taji a maimakon taji fargaba, "yaya da gaske ciki gareni?"
Mamaki ne ya kama Aayaan ganin Nawaz tanata farinciki, be taɓa tunanin haka Abin zai zo mishi da sauƙi ba, ai da tuni zai faɗa mata, ya zaci zata shiga damuwa ne idan taji,
"Kinaso ne?"Aayaan ya tambayeta
"Eh ina so, amma me kama dakai kuma sunanka nakeso asawa jinjirin"
Rungumeta yayi yanajin wata irin ƙaunarta har cikin ruhin shi, sosai take bashi tausayi saboda cikin data samu cikin gaggawa, sam bata huta ba, danma Allah yasa laulayin na kwadayi ne bana ciwo ba.
"Kinsan wani abu kuwa?
"A'a" Cewar Nawaz tana daɗa shigewa cikin jikinshi
"Nifa kunya nakeji a ganki da ciki, nasan kowa cewa zaiyi ɗan ƙaniya, yayi aika aika"
"Hmmm balle ni kuma, don Allah kada ka faɗawa su mummy da Aunty Aseey"
"Kai! Ni dana ke jin kunya ta ina zan iya faɗa? Sai dai ko ke"
"Rufamin asiri Nima Wallahi bazan iyaba.
Ahaka suka wuni suna hira, sai dai har zuwa lokacin zuciyar Nawaz cike take da fargaba, tsoro takeyi kada abin data gani a mafarki ya zama gaske, idan haka ta faru ta shiga ukunta, bata san inda rayuwa zata kuma jefata ba.
"Dear yanzu ace na mutu zaki iya Auren Sarfraz?" Tambayar da Aayaan ya jefowa Nawaz kenan
Idonta ne ya cika da ƙwalla "kaga ka dena min maganar mutuwa a gurin nan, meye na zancen wani Sarfraz? To bari kaji wanima bazan iya aureba balle Sarfraz, banda ra'ayin kowa face kai."
Sanyi Aayaan yaji har cikin ranshi jin cewa matarshi na sonshi "to misali na mutu kafin ki haihu, idan kika haihu zaki iya ba mummy ɗan da kika haifa ko zaki riƙe ne?
Fashewa da kuka Nawaz tayi tana tuna mafarkinta, cikinta ta shafa tare da kama hannun Aayann tana ɗorawa a saman cikin "kayi alkawarin cewa tare zamu raini ya'yan mu, mu basu tarbiyya me kyau "
"Nayi miki alkawarin hakan, hatta rainon cikin bi'iznillah tare zamuyi shi"
"To yaya don Allah ka dena maganar mutuwa duk da nasan tana kan kowa, amma kada ka manta yanzu fa kaine bango na kuma majingina ta, idan ka mutu ya kakeso nayi, to aini kaina yanzu Yar gidan mummy ce balle Abinda na haifa."
"Nevermind we will die desame day in'sha Allah, hope U Are happy now"
Murmushi Nawaz ɗin tayi tare da cewa "yea i am Happy "
Rufe bakinta keda wuya wayar Aayaann ta fara ƙara, koda ya duba sunan "colonel ya gani "
Da sauri ya ɗaga yana mamaki saboda ɗazu suka gama waya dashi "hello Sir"

KAMU SEDANG MEMBACA
SARFRAZ
RomansaLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...