*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*92*
*LAST PAGE* 😭😭😭
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Shima Aayaan a rikice ya ƙarasa gurin Nawaz ɗin yana cewa "me ya faru?"
"Naƙuda ce! kama ta mu tafi asibiti" cewar mummy tana riƙe hannun Nawaz cikin nata, Alamun bata kwarin gwuiwa.
"Hankalin Daddy Sosai ya tashi shima ganin cikin ƙankanin lokaci Nawaz ta fita daga hayyacinta, tunawa yayi da maman su Naufal, duk sai yaji zuciyar shi babu daɗi, suma twins wato Naufal da fudail sai sukayi ɗaki suna sharar ƙwalla.
Shikanshi goga Aayaan ɗin sai ya rasa duk wani kwarin gwuiwar shi, gani yake kamar mutuwa zatayi, "Son be strong! Ɗauketa muje mota, kaida ita sai ku zauna a baya Ni sai nayi driving ɗin."
Ciccibarta yayi zuwa motar ita kuma Mummy ta shiga ɗaki Don kwaso siyayyar da tayi ta haihuwar duk da bata san me Nawaz ɗin zata haifa ba.
Driving yakeyi yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, domin ya gama lura da Yadda Aayaan ya sallamawa Nawaz ɗin duka rayuwarshi, yasan idan ta mutu to Aayaan ɗin shima sai dai ya zama kawar gwawa ce ke rayuwa cikin Duniya.
Mummy ma sai addu'a takeyi, bini bini take waigowa tana duba Nawaz ɗin, shikuwa me gayya Aayaan duk yabi ya rungumeta sai sannu yake jera mata.
Nawaz dama tun suna jirgi take fama, daure wa kawai takeyi, saida suka isa gidan ne abin yaci ƙarfinta, addu'oi takeyi a cikin ranta iri iri, idan ta kama wannan saita saki wannan.
Ɗan sauki taji sanda ta fara karanta *"Allahummah la sahla illah ma ja'altahu sahla, wa'anta taj'alal huzna iza shi'ita sahla, Allahu, Allahu, rabbi, la ushrika bihi shai'a"* sosai take ta maimaita ta a cikin zuciyarta ta har Saida ta fito fili, duk ta jiƙe da zufa tsabar azaba, Ayanda take ji daba don Mummy da Daddy suna kusa ba tanaga kila saita zabgawa Aayaan mari, ya wani kanainayeta bayan ita kadai tasan irin azabar da takesha.
Da gudu nurses suka fito da gadon da za'a ɗora Nawaz akai domin takai gejin da bazata iya takawa da kafar taɓa. ɗora ta Aayaan yayi yana binsu cikin hanzari, mummy kuwa tsabar damuwa rungume colonel tayi ta saka kanta a cikin ƙirjinshi ko zata samu sauƙi.
Sanda za'a shiga labour room dinne wata daga cikin nurses ɗin tace wa Aayaan "yallabai iya nan zaka tsaya domin maza basa shiga"
Kofar da take ƙoƙarin rufewa yasa hannu ya riƙe tare da cewa "Matsa ki bani guri Kafin nayi ball dake! Halan kece kika yi mata Cikin!"
Yadda taga idon Aayaan ɗin yayi jajir ga jijiyoyin kanshi duka sunyi ruɗu-ruɗu yasa ta kauce ta bashi guri, fita tayi don taje ta faɗawa Babban doctor.
Shi ko Aayaan be jira komai ba ya gyara mata kwanciya a saman gadon tare da janyo table ɗin da ake ɗora duka abubuwan buƙata, Ruwan naƙuda yasa mata sannan ya ɗura allurar oxytocin a ciki.
Sauran nurses ɗin tsaye sukayi suna mamakin wannan lamari.Damƙe hannuwanshi Nawaz tayi tana cewa "yaya pls idan na mutu ka yafe min"
Ƙara rike hannunta Aayaan yayi tare da cewa "pls kidena cewa haka, lafiya kalau zaki haihu in'sha Allah"
"Yaya azabar tayi yawa, bansan yadda Zan kwatanta maka yadda nakeji ba"
"I'm sorry, pls be strong! I need you, mum need you, dad need you, ummi need you, Abba need you, Aseey need You, and last of all babyn da zaki haifa shima yana buƙatar ki fiye da kowa, pls ki taimaka mana"
Dai dai nan Dr Uthman ya shigo ɗakin don ganin waye wannan me ƙarfin halin, shiru yayi yana kallon Aayaan Sannan yace "buddy ashe kaine, yanzu wata nurse ta kawo min ƙara wai wani ya shiga ɗakin amsar haihuwa kuma wai har yana ce mata zaiyi kwallo da ita"

ВЫ ЧИТАЕТЕ
SARFRAZ
Любовные романыLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...