*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*90*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Duk ya rude sai sannu yakeyi mata, saida ya samu ta gama duka aman sannan ya kwantar da kanta a ɗaya gefen kafadar shi inda be ɓaci ba, bayanta ya riƙa shafawa a hankali soboda tayi saurin samun relief.
"I'm sorry sweetheart, wallahi na kasa riƙe aman ne Kum......
"Shiii🤫 keep quiet, meye zaki bani haƙuri bayan Nine nayi cikin! Kuma after that aini zaki haifawa yaro and kuma ma aike kika sha wahala baniba, so Kinga ai Ni ya kamata na baki hakuri!! I'm sorry dear duk Nasan nine naja miki duka wahalar nan, da ace banyi cikin ba da yanzu kina sabgarki cike da lafiya"
Mamaki ne yasa Nawaz tayi shiru tana sauraron shi batare data ce komai ba har ya gama maganar shi, "wai wane irin miji Allah ya haɗa Ni dashi ne? Wasu mazan fa sun san su sukayi cikin amma kyamar ka suke komawa suna yi, wasu har ma su riƙa kyarar ka suna daka maka tsawa idan kayi wani abun, Lallai Allah ya zaɓe ta a cikin dubu" zancen da Nawaz ta gama ayyana wa kenan a cikin zuciyarta.
"Sweetheart bakice komai ba! Hope ba fushi kike dani ba!"
Duk maganar da Aayaan zaiyi sai taga kamar ƙara kwance mata notikan mamaki yake ƙara yi,
"No dear, ni baka yimin komai ba, kuma ai dama burin kowace mace ta zama uwa. So kaga babu wani laifi daka yimin"Ɗaukar ta yayi ya shiga bathroom inda ya gyara mata jiki sannan yayi mata wanna shima yayi suka fito.
Zaman ɗakin duk sai ya ishi Nawaz duk motsi saiya ce menene? Me yake damunta? Ko akwai abinda take bukata?Tafiya ma ya hanata yi sai dai komai ya ɗauke ta, hatta bayi idan zata shiga saiya rakata.
"Sweetheart pls kabarni mana! Meyasa zaka riƙa wahalar da kanka haka ne?"Dariya Aayaan yayi "lallai har yanzu akwai sauran shakkun dakikeyi akaina game da soyayyar ki kenan Koh?"
"A'a sweetheart"
"Hmmm to meyasa kike cewa na rabu dake"
"To shikenan kaci gaba! Nagode" cewar Nawaz tana kwantawa a saman jikinshi
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kafin wani lokaci Inna talatu da ummi sun gyara ko ina tass kamar ba inda aka haihu ba, ko ƙarni babu illah kamshi da ko ina keyi, gefe ɗaya kuma Fauziyya ce kwance ana ƙara mata ruwa.
Likitan ce tace "a buɗe jikin Jamila ta gani saboda tasan me zata dauko wanda zatayi amfani dashi wajen yin ɗinkin, koda ta duba sai ta girgiza kai kawai ta fita.Inna talatu ce ta kalli ummi tace "Rahma ko na kira Khalifa na basu yaron nan suje su birne shi? Kinga har yanzu Abban Nawaz be fito ba kuma ga yamma ta fara yi"
"Ki tambayi umma kiji" abinda ummin Nawaz tace kenan saboda bataso ace ta cika zaƙewa a abun.
Kafin ma Inna talatu ta tambayeta Umma tayi saurin cewa "duk abinda ya dace kuyi, aini babu abinda zance muku domin kun nuna min ku ƴan halal ne, kuma ai Jamila ƴar kuce"
Waya ta ɗaga ta kirashi tare da cewa yazo bakin junction ya sameta.
Ba'a fi minti goma ba ya kira yace ya karaso saboda dama yana kusa da gurin.Nannaɗe jinjirin tayi cikin fallen zani ta tallabeshi a cikin hijab dinta ta fita, a tsaye ta sameshi bakin wata kwata, "yauwa Khalifa don Allah so nake ka samu abokan ka ku ɗan binne Yaron nan, wata yarinyar kawata ce tayi ɓari, kuma ba'a nan garin suke ba sunzo ne"
"Haba inna ai babu komai kin wuce nan, amsar shi yayi ya wuce ya tafi tare da ciro wayarshi a cikin aljihu don kiran sauran abokanshi saboda asamu wanda zai siyo likkafani da sauri.
![](https://img.wattpad.com/cover/320786670-288-k864880.jpg)
ŞİMDİ OKUDUĞUN
SARFRAZ
RomantizmLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...