*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*35*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Kuma hakan yanada nasaba daga zoben dana gani a hannunta, to bayan nayi mata bayanin zoben shine tace min itama ba nata bane wai Sarfraz ne ya bata,
To yanzu mudai munzone a dubemu da idon rahma akan zoben nan don girman Allah idan kunsan wani abu akan shi ku faɗa min.
Daddy wanda tunda ta fara magana yake tuna yadda mumtaz take nuna mishi muhimmancin zoben sanda tana raye, har randa zata mutu Saida ta bashi zoben a matsayin amana idan SARFRAZ ya girma ya bashi.
Ashe shi SARFRAZ ɗin ma yaje yayi kyauta dashi, mummy kuwa harda kwalla domin tasan labarin zoben kuma tasan idan mehtab taji mumtaz ta mutu akwai damuwa duba da yadda ra kwallafa ranta akan ita Yar uwar Tata.
Gyaran murya daddy yayi haɗe da gyara zamanshi sannan yace "tabbas babu ko tababa duk Wanda ya ganki yaga ƴar uwarki mumtaz, kamar takuma har ta ɓaci domin Ni dana gankima sam na manta cewa tace ku Yan biyune, nayi zaton ko fatalwace...
Sai daga baya na tuna, yanzu abinda nakeso dake shine kinsan komai na duniya Allah ne ya halicce shi, kuma sanda zai halicce shi beyi shawara da kowa ba, kuma babu wanda ya tayashi yin halitta.
Kinga kuwa duk abinda yayi dai-dai ne, sannan kuma babu wanda ya isa yace yafi Allah son halittar shi.
Rayuwa da mutuwa kuma duk suna gurin Allah, babu wanda yasan Sanda zai mutu, zai kai gobe balle jibi.
Kuma Allah yanason masu hakuri, kuma yanason waɗanda idan kaddara ta samesu ko wace iri ce su amsheta hannu biyu .
Mummyn Aayaan ce ta katse shi dacewa "komenene kafaɗa min kada kaji komai, Ni dama tuni zuciya ta ta hakura da koma me zanji, amma ina so nasani tabar wani abu dazan riga ganinta dashi?
Kowa na ɗakin idonshi cike yake da hawaye, shikuwa daddy mamakin irin ƙarfin imanin mehtab yakeyi.
Ayanda ta nuna ƙaunar ƴar uwarta be tava tunanin zata amshi ƙaddara haka da wuri ba.
Daddy ne ya fara magana a nutse " nine mijin mumtaz, mun haɗu a University of pesherwar Dake Pakistan , daga baya mukayi aure.......
Nan dai Daddy ya gama bata labarin har zuwa inda bayan ta haihu Allah ya amshi ranta,
Mummyn Aayaan tayi kuka sosai sai dai na zuci, domin idan ka kalleta hawayene Kawai ke zuba a fuskarta baya ko tsayawa....
Babu wanda beyi kukanba, sannan kuma kima da darajar mummy ta Karu a idon kowa dake falon saboda sunji yadda ta rike sarfraz babu kyara babu tsana bare tsangwama...
Haka dai akayita jajanta wa juna, haɗe da alhinin abubuwa da yawa da suka faru...
Nawaz na gefe babu abinda ke fita daga idonta sai ruwan hawaye, tayi iya kokarinta akan ta tsaida shi Amma ta kasa ..
Mamakin halin Mummy takeyi, irin yanda take nunawa SARFRAZ ƙauna babu wanda bazai dafa Kur'ani yace itace mamar shiba...
Lallai ashe har Yanzu Akwai masu yin soyayya don Allah...
Duk motsinta idon Aayaan na kanta dukda shima yana cikin damuwa amma ganinta da yayi a hakan saiya kasa sukuni, bini bini idonshi na kanta....
Rarrafowa Nawaz tayi zuwa tsakiyar falourn sannan ta tsuguna ta haɗa hannayenta guri guda tana rusa ihu, muryarta har rawa take yi tsabar damuwar da take ciki ga idonta ya kumbura yayi jajir.
"Don Allah ku yafemin, wallahi ba'a son raina muka rabu da sarfraz ba, babu yanda na iya ne shiyasa...
Amma nayi muku alkawarin hardai yana raye saina nemo muku shi, dukda Nasan bazaku Dena kallona a matsayin wadda na jawo muku bakin ciki da cikas a rayuwaba amma ina rikon alfarma akan kuyafemin idan zaku iya ..
JE LEEST
SARFRAZ
RomantiekLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...
