37&38

2 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*

*37*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

    Da sauri hassu tayi hanyar shingen da suke hura wuta, tukunya ta samu ta ɗora ruwan bayan ta hura wutar.
    Shi dai sarfraz yana biye da ita duk motsin da tayi.

      Shi kuma bandi yana gefe sai dariya yakeyi yanaso yaga yanda abun Zai ƙare, koda ruwan yayi zafi sai ta ɗauki babbar robar da sukeyin wanka da ita ta juya ruwan zafin sannan takai bayi.

    Gurin bandi ta ƙarasa ta tsaya ɗan nesa dashi tace "banda na dafa ruwan"
        Gumtse dariyar dake bakinshi yayi "to ina ruwana, kije kiyi mata mana! Tunda dama abokinkice

     Juyawa tayi batare da tace komai ba, Sabulu da soso ta ɗauka a inda suke ajiye ta kama hannun sarfraz bata kuma ko kallon inda bandi yakeba, har cikin bayin inda suka ajiye dutsen da suke zama ta kai sarfraz tasa ya zauna a dutsen, sannan daga bisani ta cire mishi riga da dogon wandonshi sai tabar gajeren ajikin shi.

      Ganin ta nufi bayin batace komaiba yasa bandi miƙewa hade da fargabar Allah yasa ba wankan zatayi mishi ba, cikin sanɗa ya karasa gurin bayin ya leƙa .
     Har wata ajiyar zuciya ya sauke  me nauyin gaske ganin irin dabarar da hassu tayi, shi dama wasa yakeyi mata yasone tayita bashi hakuri shi kuma yayi ta ja mata rai...

      Lafiyar Allah aka gama wankan suka koma ɗaki, akwatin ƙarfen da bandi yake zuba kayanshi ta buɗe ta zaɓi me kyau sannan ta bashi tace "zan fita kafin na dawo kicire wannan jikakken wandon kisa waɗan nan kayan.

     Waje ta fita ko kallon inda bandi yake batayiba Saboda Abinda yayi mata ya ɓata mata rai, shikuma ta gurin bandi ji yayi wata fargaba ta kamashi saboda fushin hassu baida kyau don sai su wuni su kwana bazata kulashi ba.

    A hankali ya karaso kusa da ita "hassu sannu da kokari ashe kinzata da gaske nakeyi? Nifa wasa nake Miki so nake inga yanda zakiyi!

     "Ai kaga yadda nayin Koh" haka tace batare data kalli inda yake a tsaye ba, sannan ta daɗa murtuke fuskarta...

     Fitowa SARFRAZ yayi jikinshi sanye da kayan bandi, abin gwanin ban dariya saboda Sam basuyi mishi ba duk a ɗingile duba da irin girman jikin SARFRAZ ɗin...

      Itama shiryawa tayi ta kama hannun sarfraz din suka nufi gidan baffa Malam, ganin yadda hassu ta ɗauki zafi yasa bandi be kulataba illa shima sai yayi sauri ya shirya sannan yabi bayansu....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

     Tunda tai sallar asbah bata tashi a saman dadduma ba, azkhar taitayi tare da addu'oi tana fatan Allah ya bayyana sarfraz sannan Allah ya kawo mata hanyar da zata koma gida taci gaba da yin rayuwarta kamar da.

  Wata irin ƙullewa cikinta yayi kasancewar yunwar da takeji, gashi jiya da dare babu yanda ba'a yi da itaba akan taci wani abuba amma taki.
      Kallon su mummy tayi taga sunata barci itada Aseey dayake muhsien a gurin Aayaan ya kwana.

     Ledar da Aayaan ya ajiye mata jiya da dare ta janyo sannan ta buɗe ta a hankali....

     Kwalalo ido waje tayi ganin tulin chocolate da ice cream duk sun huce ma sun zama ruwa kasancewar ba'a sasu a fridge ba.

     Murmushi ne ya kufce mata batare data shirya zuwanshiba. Robar ice cream ɗaya ta dauka ta kafata a bakinta Saida ta shanye sannan ta cire robar..
      Chocolate ɗin ta ɗiba da yawa ta zuba a cikin aljihun rigar ta sannan ta maida ledar ta ajiye....

    Miƙewa tayi a hankali kasancewar kafarta Tayi tsami saboda daɗewa da tayi a zaune.
     A hankali ta buɗe ƙofar ta fita saboda bataso ta tashesu daga barci, shiru faloun babu kowa hakan yasa taji sha'awar ta fita harabar gidan taɗan miƙe kafarta.

SARFRAZ Where stories live. Discover now