*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*80*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
*Ina ƙara ba masoyan Aayaan haƙuri, kunsan shi littafi yadda yazo haka yake tafiya, ban taɓa zaton Aayaan yanada masoya ba sai jiya daya mutu, to haka ma a rayuwar duniya Akwai wanda zakaji baka son shi amma wata rana sai yazo yafi wanda kakeso ma, Saboda a sanda na kawo Aayaan cikin littafin nan kowa baya sonshi, kowa haushinshi yakeji, amma jiya naga zahiri*, *To saboda haka wannan ya zama Aya a garemu, idan zamuyi so muyi ɗan dai dai, haka idan zamuyi ƙiyayya itama muyi ƙadan*
Kuma inaso Don Allah ku jure kuci gaba da karanta littattafin nan saboda akwai sauran darussa a gaba. Nima banso Aayaan ya mutu ba, Nagode 🙏🙏🙏🙏🙏.
*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA AMINA HARUNA (MEENASH COOL) INA FATAN ZAKI YAFE MIN, SABODA KE BABBAR FAN ƊIN CAPTAIN AAYAAN CE, KUMA IN'SHA ALLAH NAWAZ ZATA HAIFA MIKI WANI SABON AAYAAN ƊIN*
Haka akayi kama-kama aka shigar dashi Babban falourn gidan daƙyar, saboda Saboda yawan mutanen da suka cika gidan.
Gaba ɗaya gidan sai ya daɗa rikicewa saboda yanzu kowa ya tabbatar da cewa Aayaan ɗin ya mutu, Mummy zaune kawai take kamar itace gawar Saboda komai na mutuwar mahaifin Aayaan Sabo ya dawo mata, itakam yanzu meye ya rage mata a rayuwa da bata ganiba, ta rasa iyaye a sanda take cikin tsumman goyo, ta rasa ƙanwarta MUMTAZ, tazo ta rasa mijinta, yanzu kuma ta rasa Aayaan, shiyasa kukanma nemanshi tayi ta rasa....
Aseey kuwa har suma ta riƙa yi, ummin Nawaz ce da mummyn Sarfraz suketa kula da ita saboda suma sun rigada sunzo, Sarfraz kam zuwa yayi ya ƙanƙame gawar Aayaan ɗin yana kuka.Allah sarki Nawaz, tanachan tana barcin maganin barci da Ayanzu ya zame mata kamar ruwansha, duk wannan abu da akeyi bata saniba, baffan Aayaan baffan Nawaz, da duk wasu dangi suna zaune kowa idonshi a kumbure Alamun sunsha kuka sun gaji,
Baffa ma cewa yayi, "mutuwa dama Ni kika ɗauka kika bar Aseey da ɗan uwanta, tunda Ni yanzu me ya rage min cikin duniyar"
Kowa saida maganar ta ƙara tayar mishi da hankali.Ɗaukar gawar Aayaan akayi aka shiga da ita cikin falourn mummy saboda Anan za'ayi mishi wanka, duk wani abunda ake buƙata wanda za'ayi Amfani da shi an riga an tanada, kamarsu sabulu, turare, kafur, ganyen magarya, auduga dadai sauransu.
Cikin ƙasa da awa ɗaya an gama yi mishi wankan har ansa mishi likkafani, amma ambar iya Fuskarshi a waje saboda Yan uwa suzo suyi mishi addu'a kafin a kaishi makwanci shi.
Koda aka tawo da mummy tafe take kawai kamar gunki, Aseey kuwa gaba ɗaya ta zabge lokaci ɗaya, duk gaban Aayaan suka tsuguna kowa da Irin addu'ar da yake yi mishi, Aseey kam faɗawa jikinshi tayi, shima SARFRAZ daka ganshi zakaga ya koma kamar wani mahaukaci.
Dai dai lokacin Nawaz ta buɗe idonta, bata jira kowa ba ta fige allurorin dake jikin hannunta tayo waje da sauri, don itafa baza tayi ta zama a cikin gidan nanba ba tare data san matsayin da Aayaan yake ciki ba.
Fitowar da zatayi taga mutane da yawa a cikin falourn ga mutum kwance samɓal da likkafani, zuba wa gawar ido tayi, Aayaan ta gani cikin likkafanin idan ba gizo idonta keyi mata ba, jitayi kamar ta zunduma da gudu ta faɗa kanshi amma kafin tayi yunkurin yin hakan saboda yadda jikinta yake babu kwari taji baffa yana cewa "to yanzu a taso matarshi itama tazo tayi mishi addu'a kafin a kaishi gidan shi na gaskiya"
Mummy ce tace "baba Don Allah kada a tasheta, wallahi idan aka tasheta komai zai iya faruwa, Saboda tun bata san ya mutuba muke fama da ita balle yanzu taga gawarshi shimfiɗe"
Ahankali taja jikinta ta koma cikin ɗakin Aayaan ɗin da a yanzu ya zama nata, saboda tunda ya tafi a ciki take zaune, dayake duk sun bata baya basu ganta ba kwata-kwata.

BINABASA MO ANG
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...