*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*88*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
With high excitement tace "bro da gaske cikin yananan?" Gyaɗa mata kai Aayaan yayi haɗe da ɗaga mata gira, Kamar zata faɗi don sauri haka ta ƙarasa gaban Nawaz tana yi mata magana ƙasa ƙasa daga bisani kuma ta fita daga faloun."Allahamdulillah ala Ni'imatuka ya Rahman" Abinda Colonel yace kenan fuskarshi cike da matsanancin farinciki.
Itama mummy saida ta kasa boye farincikin ta duk da bata furta komai ba a matsayin ta na suruka, amma daga kalle ta zaka gane tana cikin farin ciki, suma sauran mutanen gurin Sosai suka nuna farincikin su duk da basusan usulin Abinda ya faru a baya ba.
Ita dai Nawaz Duk kunya ta cikata, yanzu kowa yasan ciki gareta bayan kuma kowa yasan Abinda ke faruwa kafin ayi cikin, daɗa rintse ido tayi tana tasbihi Acikin zuciyarta, tunda akace cikin nanan bataji wani Abu game dashi ba sai yanzu, ji tayi dama zata iya ganin waye a cikin nata, amma tasan in'sha Allah mai Albarka ne tunda Allah ya kareshi daga lalacewa.
Aayaan ne ya karaso ya ɗauketa yana fita daga faloun zuwa dakinsu, Babu wanda ya dube shi balle ya tanka mishi tunda sun riga da sun gama gane halinshi (baya iya boye soyayya ga wanda yake so)
Saida ya tabbatar ya kwantar da ita sannan ya fita don ya koma mota ya dauko abubuwan daya siyan mata a hanya.
Naufal ne tare da fudail suka shigo Harabar gidan, alamun kamar daga kasuwa suka dawo hannunsu ɗauke da manya manyan bamboona, tsabar farin cikin da yake ciki yasa be tuna cewa basusan komai game da cikin ba ya tare su yana cewa "My twins kunsan da mukaje asibiti Ashe cikin be zube ba!"
"Cikin wa?" Cewar Naufal yana shafa kai alumun tunani
"Au ashefa baku saniba ba " cewar Aayaan sannan ya ƙara da cewa "dama kwanaki ne mu dear tayi ɓari, to ashe cikin nanan be zube ba sai dazu da mukaje asibiti akayi mata scanning da wasu tests akace yana nan.Cikin nuna farin ciki afili Naufal yace "masha Allah, Alhamdulillah, Gaskiya naji daɗi, nima zanyi ƙani, idan kuwa mace ce nayi mata wallahi"
Ajiye bamboon Fudail yayi tare da cewa "to sannu ɗan iya, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi! To idan namiji ne kayi aboki idan kuma mace ce nayi Mata"
Dariya Abin yaba Aayaan, "to to to ya isa haka, bari naje nabar auntyn taku ita kadai""Okay Uncle sai mun hadu anjima" cewar Naufal yana ballawa Fudail hararara, nanfa musu yaci gaba, shidai Aayaan yayi saurin barin wajen bayan yasa hannu a cikin ɗaya daga cikin shopping bag din ya ciro babban plastic take away guda ɗaya ya mikawa Naufal tare da cewa "for both of you, kuma saura kuyi faɗa! Nasan halinku"
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Anan wajen fauziyyah ta zube a ƙasa tana rusa ihu, Abinda taketa gudu kenan shi yasa koda yaushe takan cewa umma ta riƙa haƙuri akan wasu abubuwan amma taƙi, har gurin bokayen ƙarya ta riƙa kaita don dai taga babu Abinda ke samun su ummin Nawaz kila ta haƙura amma ta ƙi denawa, kullum ƙiyayyar gaba takeyi, itama saida tayi iya kokarinta wajen dasa mata ƙin Nawaz ɗin.
Yanzu fisbilillah kamar ita ace babanta ya saki mamanta? Ai wannan ma babban abin gori ne Wallahi, ga mazan yanzu da Neman ba'asi, Abinda be kai ya Kawo Bama sai suyi maka gori akai, balle Abu irin wannan, barin yanzu ita kanta auren nata girgiɗi yakeyi.Inna talatu ce ta kama ta ta miƙar da ita tsaye tana bata baki "Addu'a zakiyi fauziyyah ba kuka ba, domin kowa da Irin tashi kaddarar, fatan mu kawai shine Allah yasa muyi kyakykyawan ƙarshe, kuma wannan kukan da kikeyi ƙara tayar mata da hankali zaiyi.
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...