76

3 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*76*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

    "Fatima dama nace Miki an kashe boss, kalli kiga" Cewar maman sudeis tana nunawa fatima stain ɗin dake jikin zanin gadon

   "Ni dai ajiye mu fita kada ta tashi ta gammu kisa muji kunya" Cewar Fatima tana yin hanyar fita daga faloun.

    Shara da kakkaɓe-kakkaɓen ƙura sukayi mata da ƴan gyare-gyare amma iya falour da kitchen sai ɗaya bedroom ɗinsu wanda suke kwana da.

   Maman sudeis ce tace "Anya kuwa fatima bazamu dafa musu wani Abu ba! Nasan ba wani abu suka ci ba kuma Dole bakinta babu daɗi"

   "Eh ya kamata amma kamar me"

  "Mu fara duba freezer muga abubuwan dake ciki, Kinga sai musan me ya dace a girka"

   "To" Fatima tace tare da miƙewa Sannan suka nufi kitchen Dukansu.....

   Bubu abinda babu a cikin freezer ɗin, nadaga kaji, kifi dasu vegetables.

   Kaji biyu Maman sudeis ta ciro da kayan lambu sai catfish guda uku manya, kifin taba fatima tace ta gyara ita kuma ta daɗa ɗauraye kazar ta ɗora a wuta tare dayi mata haɗin tafashe.

    Sosai aikinsu yayi nisa inda har sun gama pepper chicken da roast fish, fried rice ɗinne basu gama ba, babu Nawaz babu alamunta, hakan ke nuna har yanzu bata tashi ba, shima kuma Aayaan har yanzu be dawo ba.

   A ɗaki kuma tashin Nawaz kenan daga barci taga babu Aayaan, sosai taji daɗi Saboda zatayi komai a sake tunda shi ya kase gane tana jin kunyar shi, miƙewa tayi a hankali ta fara tafiya, ita kanta mamakin ya akayi batajin irin mugun zafin nan takeyi, tasan dai tanajin zugi amma ba Irin wanda take tunani ba "kenan Sarfraz mugunta yayiwa hassu, tunda har fa ɗinki akayi mata" bathroom ɗin ta shiga a hankali tare da kunna tap ɗin water heater.
     Bath ta cika da Ruwan zafi Sannan ta sirka zuwa yadda zata iya shiga, cire rigar jikinta tayi sannan ta shiga cikin Ruwan a hankali, daɗi sosai Ruwan yayi Mata, tayi kwance luf a ciki dumin na ratsa ta tako ina.

    Saida ta canza ruwan har sau uku Sannan ta haƙura tayi wanka ta fito, zanin gadon dake gefe ta ɗauka ta koma bayin ta tura shi cikin washing machine ta zuba ruwa da liquid soap.

   Bedroom ɗin ta dawo  ta samu mai a cikin drawer ta mutstsika a jikinta sannan ta feshe duka jikinta da turare, rasa kayan da zata sa tayi saboda babu kaya a cikin wardrobe ɗin.

    Tana tunanin fita zuwa ɗauko kayan saboda kada su haɗu da Aayaan kila yana falour ko kitchen, gashi kuma towel ne Kawai a jikinta, shiru tayi naɗan wani lokaci inda daga bisani ta koma bathroom ɗin ta ɗauko doguwar rigarta ta mayar jikinta tunda dama Sallah kawai tayi da ita bawai tayi datti bane.
    Tufke gashin kanta tayi daya dameta a fuska Sannan tayi hanyar fita falour saboda cikinta ya fara kiran ciroma, mamaki abin yaba Nawaz ganin maman sudeis da Fatima hakimce a kujera sunata shan hira "lah! Ikon Allah! Don Allah yaushe kuka zo gidan nan? Ina yayan yake?"

    "Hmmm Madina kenan, nifa har yanzu na kasa yarda ba ciki gareki ba, wannan uban barci kamar barcin mutuwa" Cewar maman sudeis tana kannewa fatima ido
   Ita kuma Fatima tace  "Tun ƙarfe goma muna nan gidan fa, yayan naki kuma ya fita tun sanda mukazo"

     "Kai dan Allah! Shine ko ku tasheni!"

   "Hmmm Madina manya, mu munsan  meya saki Barci ne da zamu tashe ki?, muje mu tasheki mu samu zunubi"

    "Kai Don Allah wane zunubi kuma" Nawaz tace tana yin hanyar kitchen, sosai ta gyara rafiyarta saboda kada su fuskanci wani abu (Nikam nace hajiya Madina kin makaro, ai duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, balle kuma sun gani da idonsu)

SARFRAZ Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt