29&30

4 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*29*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

       A tare sukace "Baba wane Muhammad ɗin?

    "A.V.M Muhammad mai goro,  nida babanshi malam Aliyu me goro aminaine irin amincin da ake zama kamar ƴan uwa... Ba irin na yanzu ba

     Yanzu hakama bamufi awa ɗaya da gama waya dashiba.
    Amma dai Allah yayiwa Muhammadun da na sani rasuwa, yaron Arziki...
    Allah dai yayi mishi Rahma, sau biyu yana kaini Saudiyyah.

    Wani daɗi ne ya ziyarci mummy jin yanda ake yabon mijinta marigayi...

    Cewa tayi "Ni matar shice wannan kuma ɗan shine sunan shi Aayaan,

      Da sauri baffa ya miƙo hannu "zo zo zo nan jikana Ayatullah, Allah sarki ashe dai inada wasu ahalin ban saniba.
     Miƙewa Aayaan yayi yaje gaban baffa yana sussunne kai
    Akan cinya baffa ya ɗora shi, ai da sauri Aayaan ya miƙe yana murmushi..

   "Baffa ai sai in karya maka kafa" Aayaan yace yana murmushi...

" Aikuwadai, baba Wannan gabjejen zaka ɗora a cinya? Cewar mummy tanajin farinciki a zuciyarta

     fadawa dai sai murmushi sukeyi saboda sun daɗe basu ga hakimi yana farin ciki hakaba....

      

    NAWAZ
   Koda ta shiga cikin gidan da gudu ta faɗa jikin umminta tana farin ciki, Allah na gode maka da kasa na ƙara ganin ummina..

    Sakin baki kowa yayi ganin Nawaz tsaf cikin kwanciyar hankali.
   Nura ne yace "Nawwarah daga ina?
      Hmmm kawu ai abin akwai tsawo, bari na gama ganin ummina zan baku labari, ina Amma?

    Ta shiga bayi cewar Nura, wanda a kallo ɗaya zaka fahimci irin farin cikin da yake ciki.

   Ummi kuwa tama kasa magana domin ganin abin takeyi kamar a mafarki, sai hamdala taketa yi a zuciyarta tana godewa Allah subhanahu wata'ala daya dawo mata da ƴarta sanda ta cire rai da kuma ganinta.

    Itama Amma da gudunta ta fito daga bayi, Nan ta zauna gefen Nawaz tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta, domin bata taɓa zaton zata kuma ganin Nawaz ba.

    Bayan an kimtsa ne Nawaz ta fara basu labarin abinda ya faru da ita....

    Su kuwa acan fada hirace ta ɓarke tsakanin baffa da Aayaan, saboda baffa nata bashi labarin yarintar mahaifinshi...

     Sai daga baya baffa yace, au farinciki ma yasa na manta komai..
   Ga dukkan alamu kune kuka tawo da Nawwarah koh?
     "Baba Nawaz kake nufi? Cewar mummy

   "Eh ita nake nufi ƴata,

   Aayann Mummy ta kalla "son kabashi labarin abinda ya faru.

     Nan ya sanar da baffa duk abinda ya faru, tundaga farko babu abinda ya ɓoye mishi...

   Baffa ne keta yi mushi godiya, yana sawa Aayaan albarka, sannan ya ƙara da cewa wannan wahalar da kasha bazata tashi a banza ba, zanyi maka kyauta mai girman gaske, saboda ka dawo mana da farin cikinmu har gida, don haka kyautar guda ɗaya ce tamkar da dubu kuma zata ƙara mana danƙon zumunci..

     Mummy ta fahimci abinda baffan yake nufi amma Aayaan ko a takalmin shi, domin shi bema gane me baffa yake nufi ba,  shidai abinma dariya ya bashi, wai shi za'a yi wa kyauta.

    
    °
A cikin gida kuma Nawaz ta gama basu labarin abinda ya faru da yanda Allah ya kuɓutar da ita...

    Sunyi farinciki sosai da fatan Allah ya daɗa kiyaye gaba, sannan suka taso don zuwa fada su yiwa su Aayaann godia...

SARFRAZ Where stories live. Discover now