*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*87*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Kuma ina ƙara yiwa Allah godiya daya lalata Abin ba tare da nima na cutar da wani ba, kin cuceni! kin cuci Rahma, kuma duka akan Abinda Allah be haramtaba, daga baya kuma kika maida kiyayyar taki kan me sunan mamana.
Tunda Madina ta buɗe ido a cikin duniya take cikin kuncin rayuwa, Abin be tsaya nan ba har saida kikasa ƴan uwanta na jini suma suka tsaneta, yanzu to wa gari ya waya..? Waye ya koma Abin tausayi kuma abin ƙi ga kowa? Ke kanki kinsan idan ƴan Uwanki sukasan da wannan maganar to kin zama Abin gudu, babu wanda zai yarda ki raɓe shi.Waigowa yayi ya kalli ummin Nawaz sannan yace "wai ko Rahma kinsan cewa ita tasa akamin asirin da zai tafi da hankali na yasa na manta komai da kowa? Sannan bata tsaya iya nanba saida tasa aka min shashatau akan ku ta yadda zan watsar da lamarin ku baki daya! Kuma fa wai duk hakan akan kishi tayi shi?"
"Kayi hakuri ranka ya daɗe! (Dama tun tuni haka take ce mishi), nidai na yafe mata kuma zansa Nawaz ta yafe mata, sannan kaima ina rokonka Alfarma akan ka yaf........"
"Dakata Rahma! Wai ke kuwa wace irin zuciya gareki wadda bata fushi? Ni dai bazan iya yafewa ba, idan ma na yafe to taje na saketa domin bazan iya ci gaba da zama da ita ba""Innalillahi wa'inna alaihi raji'un, haba Abban Nawaz meyasa zaka yanke hukunci cikin fushi, ya kamata ace ka samu lokaci kayi tunani tukun kafin kace komai game da wannan maganar"
"Wane tunani kuma zanyi banda wanda nayi a baya? Ai iya tunanin da nayi da ƙuncin dana shiga sun isheni, Kuma Ni Sam ba'a cikin fushi nakeba, domin da a cikin fushi nake Wallahi zan iya rufeta da duka har saita dena motsi, Rahma wai ko kinsan me na gani?, Kinsan halin dana shiga? Kisan irin ciwon da zuciyata ta ƙunsa? Haka fa rayuwata ta koma banida maraba da mahaukaci, in banda Allah ya haɗani da malamin kirki mutumin ƙwarai, wanda yasan meye malinta kuma yake amfani da ilimin da Allah ya bashi wurin temakon al'umma da yiwa addini hidima, shine fa ya tsaya tsayin daka sai daya karya duka sihirin data yi min, amma ai da tuni na dade ta fara hauka tuburan"
"Abban Nawaz don Allah adena tone tone, muma masu laifi ne a gurin Ubangiji, ya kamata ka yafe mata dalilin hakan sai Allah ya ƙara shiryata kuma kaima ya yafe maka."
Umma wadda tunda suka shigo bata furta komai ba illa hawaye da yaketa kwarara daga cikin idonta, bata taɓa jin kunya da nauyi irin na yau ba, lokaci ɗaya tsana da ƙyamar kanta da ayyukan ta suka saukar mata, nadamar da tafi wadda tayi a baya ita ta cika cikin ƙwaƙwalwarta.
Sosai ta ƙara fashewa da kuka jin irin kalaman da mijinta keyi akanta, lallai ta tafka babbar asara a rayuwarta, yanzu bazata iya nuna wani abu me kyau da zatace itace ta aikata shiba domin kiyamarta, gaba ɗaya ta shagala da duniya wadda kuma ba matabbata bace.
Cikin gunjin kuka tace "Muhammad Nagode maka sosai, Allah ya saka maka da Alkhairinsa, kuma hukuncin daka yimin wallahi na chanchanci fiye da haka, amma Nasan adalcinka ne yasa haka domin Ni shaida ce akan kyawawan dabi'un ka .... Nagode sosai sosai, amma ina ƙara baku haƙuri dukanku musamman Rahma da Nawaz, na cutar dasu iya karfina, sannan mama (tana nufin mahaifiyar Abban Nawaz) sai kai, Don Allah ku taimakeni ku yafe min dukda cewa banida tabbacin cewa Allah zai yafe mini"
Da sauri ummin Nawaz ta katseta da cewa "A'a umma kidena cewa haka! Domin wallahu gafurur Raheem,"
Abban Nawaz ne yayi saurin katse ummin Nawaz da cewa "kuma shadidul iqab ba"
Ƙara rushewa da kuka umma tayi tana girgiza kanta cike da nadama da dana sani!
Sallamar inna talatu (kawar ummin Nawaz wadda Nawaz ta gudu gurinta) ce ta cika tsakar gidan..
ESTÁS LEYENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...