*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*45*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Haka Nawaz ta yini a ɗaki ko abinci bata ciba, tana tsoron fita falourn saboda kada ta haɗu dasu mumy.
Sai da Aseey taga abin dagaske ne sannan ta samu ta dafa mata Noodles ta kawo mata, da kyar Nawaz ta tashi ta amsa, Saboda kwanciya tayi ta rufe da duvet.
Aayaan kam yana chan yana fama da muhsien, wai dole sai sunje yawo gashi kuma shi sam bayason fita yau, yanaso yaɗan huta kafin al'asar...Hakanan dai daƙyar ya samu yayi mishi wayau akan zai kaishi gobe, sannan ya zuge back pack dinshi ya kwaso chocolate ya haɗa shi dasu.
A Ranar kam kowa Saida jikinshi ya gaya mishi da yunwa, kasancewar dama Nawaz ce keyin girkin sai kowa ya sakankance.
Sai wajen ƙarfe biyu da hantsi ya dubi ludayi shine Aseey ta leƙa kitchen ɗin ta dafa Noodles da kwai, haka kowa yaci don sun san mai dafawar bazata fitoba balle su sa ran samun abincinta.Ko bayan da Aseey ta dame ta akan ta tashi taci abincin hakanan ta ɗaure fuska "Aunty a Gaskiya Abinda kikayi baki kyautaba, kinsan dai babu kyau namijin daba muharraminka ba ya riƙa taɓa maka jiki amma kina kallo ya Aayaan yana daukaka kuma a matsayinki na Babba baki tsawatar mishi ba...
"I am sorry dear! Bazaki gane komaiba har sai an sanar dake, amma bani keda wannan damar ba sai dai idan zaki tambayi Mummy ita zata feɗe Miki biri har wutsiya.
Shiru Nawaz tayi kirjinta kuma na bugun tara-tara, hakanan taji Maganar batayi mata ba ga Wani tsoro daya dirar Mata a zuciya lokaci guda ta zaro ido "Aunty Don girman Allah ki sanar dani koma menene"
Murmushi Aseey tayi "ooh! Sisto meye na tada hankalin ki haka? Sekace nace miki gobe zaki mutu! To gaskiya Ni banason wannan tsoron inasone ki zama jaruma.Nawaz Kamar zata zunduma ihu tace "Aunty ba wannan ba don Allah Ni kiyimin bayani ne yadda zan gane me kike nufi" itakam Aseey abinma dariya ya koma bata domin duk Nawaz ta fita daga hankalinta harda ƴar zufarta...
Murmushi tayi tace "my sister nothing bad, bafa Wani abu bane kawai dai naji kamar Mummyna tana cewa zataje ta roƙi baffa akan a barmata ke kici gaba da zama tare damu, wai tanajin daɗin zama dake....
Saida Nawaz ta sauke Wata sassanyar ajiyar zuciya Sannan tace "indan wannan ne babu Matsala Insha'Allah lokaci zuwa lokaci zan rika zuwa ina yi mata kwana biyu.
Rashin wayon Nawaz Aseey ta gani Saboda Yadda ta yarda da maganar Lokaci guda batare data tuna abinda Aseey ta fara ce mata ba .
Bata fuska Nawaz tayi 😞 a gaskiya banji daɗin Abinda yaya Aayaann yayi mini ba, ace a gaban su Mummy ya fito rungume dani Amma shi ko a jikinshi, kuma hmmm bari Kawai nayi shiru tunda babu wani amfanin faɗa domin aikin gama ya riga da ya gama.
°
Yau kusan kwana huɗu da dawowar Aayaan Amma Nawaz ta kasa samun damar guduwa, saboda duk sanda ta tashi da asbah sai dai taga Aseey zaune, abin har mamaki yake bata saboda da ita take tashinta amma yanzu sai taga ta rigata tashi, har Saida Nawaz ta Fara tantamar anya ko dai Aseey taji sanda tace zata gudu ne!Ta ɓangaren Aayaann kuma yaune za'a yi passing out a N.M.S barrack ɗin dake sabon Gari a Zaria, inda achan zai haɗu da Mutane kala kala harda waɗan da a ƙalla ya Kai 5years rabon da su haɗu....
Shiryawa yayi sosai a cikin complete New uniform waɗanfa suka bi ingarman jikinshi suka zauna kamar Anan Allah ya halicce su, sosai yayi kyau Sannan ya ɗauko Beret ɗin soldiers ya kafa a kanshi ya ɗan karkata ta gefe abin dai gwanin ban sha'awa sai wanda ya gani...Bai ɗauki komaiba ba illah side pack wadda ya ɗan Zuba abubuwan da zai iya buƙata Tare Da ƙaramar bindiga koda wani abin zai iya faruwa.
Duk Cikin kwanaki huɗun sam bai kuma ganin Nawaz ba, abin har Saida ya ɗan taɓa shi Amma ya shanye tunda komene ne ma ai shi yaja.

KAMU SEDANG MEMBACA
SARFRAZ
RomansaLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...