23&24

3 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*23*

*_Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji_*✍️

  Zaune Nawaz take ta saƙa wannan ta warware, bata taɓa tunanin rayuwa zata juya mata baya hakaba acikin ɗan kankanin lokaci.

   Kuma nadamarta bata wuce da tasan haka zata faru da duk yanda za'ayi bazata yarda  Sarfraz ya biyo ta ba...

   Pure water aka basu  kowa guda ɗaya "ga ruwa nan kuyi duk abinda zakuyi dashi don shine abincin ku na yau.

   Shiru Nawaz tayi tana tunani "Gara nayi alwala da ruwan nan idan yaso sai insha wanda ya ragu.

     Gefe ta samu tayi alwala, suma sauran mutanen ganin tana alwala yasa suma suka farayi.

    Ɗaya daga cikin Mutanen da suka sato su ta kalla "don Allah inane Gabas?

  Nuna mata yayi da hannu , juyawa tayi ta kalli inda ya nuna mata ta tada kabbara.

   Tayi raka'a biyu wani shima sanye da rawani ya ƙaraso gurin, ganin yawancin mutanen suna sallah, taɓe baki yayi ya kalli wanda ke gefensu a tsaye yace"kai iluu kana tsaye ka bari suke sallah saboda suyi addu'a Allah ya tona mana asiri koh?

    "A'a oga naga ai sallah sukayi ba wani abuba, kuma idan na hanasu yin Sallah Ai aikinmu zai iya ɓaci.

   Sigari ogan ya fito da ita yasa lighter ya kunna sannan ya fara zuƙa, bai cewa iluu komaiba ya wuce gaba.

   Dai dai nan Nawaz ta idar da sallar,. Jingina tayi da bishiya tanata addu'a a cikin zuciyarta.

   Shi dai iluu sai kallonta yakeyi, tun sanda aka kawosu dajin yaji ta burgeshi gashi tana mai yanayi da kanwarshi..

   Ji yayi anya zai iya bari ayi mata wani abu kuwa?

    Dan kusa da ita ya matso ya fara magana a hankali "sannu baiwar Allah, kinajin yunwa ne?

  Mamaki ne ya kama Nawaz ganin har wani ya damu da halin datake ciki, taso ne tayi banza dashi to amma ko babu komai ya nuna ya damu da ita kuma ko bahaushe ma yace ka gaida mai gaida ka.

   A hankali tace "yauwa sannu, banajin yunwa sai dai gida da nakeso naje,

   Shiru yayi bai kuma yin maganaba ya matsa daga kusa da ita,

   Ita dai Nawaz sai addu'a takeyi a cikin zuciyarta musamman ma _ALHAHUMMA AJURNI FI MUSIBATI WA AKLIFLI KAIRAN MINHA_

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

  Wasu yan Fulani ne tafe da shanun su, da alamu sun dawo daga kiwo ne,

   Mace da namiji ne dukkanin su bazasu haura shekara goma sha uku zuwa sha huduba.

   Har sun gifta macen ta dawo baya saboda taga kamar mutum kwance, ile kuwa  ganin sarfraz tayi kwance shame shame ko numfashi bayayi.

   Cikin razana tace "bandi ware"
    Wanda ta kira da bandi ɗin ne ya karasa kusa da ita cikin hanzari.

   Shima zare ido yayi ganin mutum kwance baya motsi...

   Tsugunawa yayi yana tattaɓa sarfraz ɗin don ya gane yana raye  ko ya mutu.

   Pulse ɗin shi ya taɓa cikin Sa'a kuwa yaji tana bugawa a hankali.

   Kallon macen yayi yace "hassu bata mutuba mu kaita gidanmu che mu mata magani kinga batada jini kuma harbinta akayi, idan muka barta anan mutuwa zatayi.

  Cikin Hausar ta dake nuna ita ɗin tsantsar fulanice tace "bandi taya zamu iya daukan ta?

   "Ki kama min ita mu ɗora ta akan gwalbo,

SARFRAZ Where stories live. Discover now