*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*73*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Tsoro ne ya kama Nawaz ganin Aayaan durkushe yanata faman zufa bayan kuma sanyi akeyi a garin, da sauri ta ƙaraso kusa dashi, kama mishi damtsen hannunshi na dama tayi wanda tafinta ko rabi be ritsaba "yaya meya sameka? Yanzunnan fa muke Lafiya dakai"
Sosai yakejin jiki, cikin minti uku amma nema yake ya fice daga hayyacinshi "samo min ruwa mara sanyi sannan kije cikin drawer ta Biyar Akwai Wani magani ki kawo Min Yanzu pls"
Da sauri Nawaz ta dauko Ruwan Sannan ta shiga dakin ta duba drawer, babu maganin data gani a ciki Sam
Da sauri ta dawo tare da bashi Ruwan kuma tana cewa "yaya banga maganinba fa kwata kwata, koba a cikin drawer yake ba?
Runtse idonshi Kawai yayi tare da cije laɓɓansa na ƙasa, shi kaɗai yasan Abinda yake ji.
Rungumeshi Nawaz tayi tana cewa "yaya don Allah meke damun ka? Pls ka faɗa min"Idonshi wanda ya chanza kala yayi jajir ya buɗe ƙasa ƙasa yana kallonta, tausayinta ne ya kama shi Domin yasan idan ya chafketa Abin bazai yi Mata kyau ba, jijiyoyin da suka fito a saman goshinshi take taɓa wa tana cewa "ko ciwon kaine ke damun ka?
Cikin wata iriyar murya Wadda saida Nawaz ta ɗago ta kalleshi da kyau donta tabbatar cewa shi yayi Maganar yace "ciro wayata a aljihu kiyi min dialling ɗin wata Number zakiga an rubuta Bestie haidar a jiki"
Dubawa tayi tai dialling sannan ta miƙa mishi wayar, aikam kiran yana fara shiga haidar ya ɗaga yana tuntsira dariyar mugunta "Ai dama zaman jiran kiranka nakeyi domin Nasan dole ka kira"Kallon Nawaz Aayaan yayi yace "pls kije kitchen ki dafa min mint tea"
"To" Nawaz tace sannan ta miƙe da sauri ta nufi kitchen, shifa bawai shan tea ɗin zaiyi ba Kawai ya kore tane saboda ya samu damar yiwa haidar magana."Haidar meka zuba min a cikin tea ɗin daka bani ɗazu?" Tuntsirewa haidar ya karayi da dariya Sannan yace "Irin maganin da kuka zubamin a cikin drinks Ranar da aka ɗaura min aure, Ammafa kai guda huɗu na zuba maka saboda dama Bahaushe yace Ramuwar gayyah tafi ta gayyah zafi"
Cikin Wata irin murya me ƙaraji Aayaan yace "Wallahi haidar na rantse da Allah idan kasa na kashe Yar mutane ko nayi mata wani lahani to wallahi kaima sainazo na harbe ka sai dai duk Abinda zai faru ya faru daga baya, amma ya za'ayi ka zuba min kwaya har guda huɗu bayan Kasan Guda ɗaya akesha itamma ga wanda ke fama da ciwon Rashin sha'awa, kuma ka fa san Irin karfin sha'awa ta koda babu magani"
"Oho Ni sanda kuka zubamin meyasa bakuyi tunanin kada na kashe ƴar mutane ba Nima?"
"Haidar pls keep joke apart wallahi Nawaz is still Virgin banaso naje nayi abin da za'a dawo ana da an sani saboda tun yanzu I'm loosing control of my self"
"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un! Subhanallah, wallahi bansaniba da bazan zuba maka ba, Amma abokina me kake yi har zuwa yanzu baku zama intimate ba?"
"It's my personal issue, yanzu dai koda kasheta nayi nasan iya wayarnan da mukayi ta Isa shaidar cewa kaine sila saboda nayi recording ɗin duka maganganun da mukayi", be jira jin Amsar da haidar zai bashi ba ya yanke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya yana jefata saman kujera.
A daddafe ya ƙokarta ya miƙe yana runtse idonshi saboda Yadda yakejin mararshi tana chure mishi ga wani irin zugi da take Yi mishi, length Dinshi kuwa zuwa wannan lokacin ya koma Kamar katako, da kyar ya samu ya isa bedroom ɗinsu, ai yana shiga yayi flat a saman gado yana sauke numfashi a wahale
"Allah sainaci uban haidar duk randa muka haɗu, Meye Nashi nayimin irin wannan aika aikar?"
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...