69&70

3 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*69*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

   Sosai fa Aayaan ya dage akan shifa saita yi mishi bayani, ita kam Nawaz ko mai zeyi mata bazata iya yi mishi bayanin wannan Abin kunyar ba.
   Miƙewa tayi tace "bari naje bathroom na dawo"
   "Okay to muje na raka ki"
   "No pls kabarshi zani da kaina"
 
    "Okay to kiyi sauri kizo kimin bayanin"
  "To" Nawaz tace tare da yin Hanyar bedroom ɗin, tana tafiya shikuma yajanyo kwalin zuwa gabanshi, bubbuɗewa yakeyi yana cirosu yana ajiyewa a gefe, ko wanne ya ciro saiya karanta jikin kwalinashi ko robarshi, yawanci rubutun da Larabci ne sai English, hakan yasa duka ya fihimci magungunan na Meye!

   Murmushi yayi yace "WOW WOW WOW! Gaskiya ina ƙaunarki Mummy na, yanzu dama duka wannan Abin duk danni akayi shi, gaskiya dagewa zanyi ta riƙa shansu yadda ya kamata...
  
    Hajiya Nawaz kam tana shiga bedroom ɗin ba bayi ta shigaba don dama babu abinda takeji saman gado ta haye abinta taja duvet ta rufe jikinta, aikam bata ɗauki wani lokaci mai tsawo ba barci yayi gaba da ita.

   
    Shi kuwa goga Aayaan yana nan ya dage sai ciro kayan yakeyi yana daɗa bin kowane label yana dubawa, waɗanda basuda rubutu a jikinsu kuma sai dai ya kalla ya jujjuya ya ajiye.
    Saida ya gama fito dasu duka Sannan yaga wata envelope a ƙasan kwalin, aikam beyi wata wata ba ya ɗauketa ya buɗe.

    *_Assalamu alaikum_*
   _Daugter ina fatan kun sauka lafiya, Allah ya albarkaci zamanku ya dauwamar da farin ciki mai ɗorewa a tsakaninku_
    _Inason don Allah Don darajar Annabi daughter kitaimakeni kirika shan magungunan nan domin zasu taimaka miki matuka, and idanma Akwai wani abun daya shige miki duhu pls ki kira Aseey zatayi miki bayani, so nakeyi ki yakice tsoron nan da kika jibgawa zuciyarki_
    _And kuma Ni burina duk sanda zaku dawo ya zamana an tawo mana da tsarabar ƴar England ko ɗan England_
    Haka dai Aayaan yabi duka rubutun yana karantawa sinka sinka har zuwa inda mummy tace

   _A gaida Min da Aayaan ɗin kuma kice nace kullum ya riƙa tunawa da Alƙawarin daya ɗaukar min, na barku Lafiya, Allah ya haɗa kanku_

   Murmushi yayi ya maida takardar ya ninke yadda take Sannan ya Maida ta Cikin envelope ɗin ya sakata a cikin kwalin sannan ya Maida kayayyakin ciki.
    Ganin shiru Nawaz ɗin bata dawo ba yasa shi miƙewa ya nufi bedroom ɗin, murmushi yayi ganinta tana barci lakadan "hmmm sweet heart manya, Allah dai ya barmu tare"
    Cikin bargon shima ya shiga tare da janyota ƙirjinshi yana rungumeta tsam, "ita batada wuyar barci ne? Naga fa bamu daɗe da tashiba amma harta kuma komawa, ko batajin daɗi ne? Jikinta ya taba ko zaiji tracing ɗin zazzaɓi amma bejiba, girgiza kai kawai yayi ya cigaba da kallon fuskarta.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

   Kasancewar ummin Nawaz nada sanyi da karayar zuciya tana ganin umma ta fashe da kuka, kuka takeyi bilhaƙƙi tana tambayarta meyafaru har ƙafarta tayi haka?
   Itama umman kuka ta hau yi tana duba irin zaman cusguna musu data riƙa yi amma ace har yanzu ita bata riƙe ta da wani abu ba, wato har kuka takeyi saboda wani Abu mara kyau ya sameta, nadama da dana sani ne suka ƙara rufeta da tsanar kanta.

    Itakam ummin Nawaz cewa tayi bazata koma Maiduguri ba tunda umma batada lafiya, zata zauna ta kula da ita har zuwa sanda Allah zai yanke jinyar ta samu lafiya, idan da rabo ma sai Abban Nawaz ya dawo.

    Inna talatu kam wani ƙululun baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, "wai yanzu duk cutarwar da umma tayi musu ita da Nawaz tana nufin ta manta kenan? Gaskiya sanyin zuciyar Rahma yayi yawa...., Tana ganin idan itace ma saidai tace Allah ya sauwaƙe ta ɗauki Abinda zata ɗauka tayi gaba, amma babu yadda za'ayi ta zauna jinyar umma.

SARFRAZ Onde histórias criam vida. Descubra agora