86

3 1 0
                                    

*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*86*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

  Fita yayi daga ɗakin ya dudduba waje ko zai ganta a wani guri, duk inda ya duba be ganta ba sai kawai ya koma ɗaki domin yasan bazata wuce ɗakin su Mummy ba.

  Ita kuwa Hajiya Nawaz tana chan bayan gida inda aka hura wuta jiya, wuta ta hura Sannan ta ɗora babbar tukunya inda ta ɗauki bokiti ta riƙa debo ruwa a fampo tana zubawa har saida ta kintaci dai dai wanda tasan zai isa dama kunun Sannan ta barshi haka, murfi tasa ta rufe tukunyar, inda taga mummy ta debo waken da akayi kosai jiya ta shiga ta auno tiya Uku, a hankali a hankali ta riƙa zubawa a turmin tana surfawa har saida ta gama Sannan ta kaishi bakin fampo ta ajiye, cikin store ɗin ta koma ta buɗe babban bawon da gasara ke ciki ta kwashe ruwan saman sannan ta ɗibi bokiti ɗaya da rabi ta rabashi gida Uku ta ajiyesu a bakin tukunyar inda Ruwan keta tafasa, cikin store ɗin ta koma ta dauko wani madaidaicin bokiti wanda zata rika dibar Ruwan zafin tana zubawa a cikin gasarar.

    Cikin mintunan da basufi Goma ba ta gama dama kunun tsaff, murfi tasa ta rufe bokitan Sannan ta kuma ɗebo ruwa ta zuba rabin tukunyar ta rufe.
   Bakin fampo ta koma domin ta wanke wake, a daidai nan mummy ta fito domin ta hura wuta ganin garin ya fara haske.

   Mamaki ne ya kamata ganin manyan bokitai har uku cike da kunu, ga kuma wani ruwan a cikin tukunya shima yana shirin tafasa.

    Ƙarar Ruwan dataji a lungun da fampo yake yasa ta ƙarasa da sauri, Nawaz ta gani a duƙe tana wanke atarugu da tattasai tana zubawa a cikin waken data gama wankewa...

   "Lahaula wala quwwata illah billah! fisbilillah daughter dama kece kiketa faman wannan aikin? Kin manta kedin ba wata cikakkiyar lafiya ce dake ba!  Maza bar aikin nan ki koma ɗaki ki kwanta ki huta Nagode sosai sosai, Allah ya saka da Alkhairi kinyi kokari sosai.."

  "Allah mummy naji sauƙi, kuma Ni kwanciyar ce bana so, don Allah ki barni saiki cigaba Ni kuma ina tayaki "

   Bayanda mummy ta iya ganin Nawaz ɗin ta nace saitayi, sai kawai ta kyaleta bata kuma yunkurin hana taba "daughter bari to naje na kira su Fudail suzo sukai nikan waken"
  
   "To mummy saikin dawo" cewar Nawaz tana ɗaukar bawo a bakin fampo tare da yin haryar store, shinkafa ta auno tiya biyar ta wanke ta zuba kafin Mummy ta dawo.

   Koda Mummy ta dawo faɗa tahauta dashi, "haba daughter! Yaza'ayi ki riƙa daukar abuu mai nauyi haka bayan kinsan cikin condition ɗin da kike!"
    Riri rimi Nawaz tayi da ido tare da cewa "Mummy shinkafar kawai fa zan dafa ke kuma sai kiyi miyar"

  Jinjina kai kawai mummy tayi tana mamakin ƙarfin halin Nawaz.

   Cikin awa daya har tayi perboil ɗin shinkafar ta maida ita ta tirara, lokacin ma har Nawaz tayi nisa da suyar kosai da tayi kane kane ta hana mummy yi, ganin haka sai Mummyn ta hura mata wata wutar saboda idan akace sai an jira shinkafar ta dahu kafin a fara suyar to za'a bata lokaci sosai gashi gari ya fara wayewa.
  Itama mummy gasara tasawa kunun Sannan ta zuba sugar yadda kowa sai dai kawai ya dibi yadda zai mai, itama Nawaz a cikin warmer take zuba kosan data soya.

    Duk mutane sun fara cika gurin saboda sai  fitowa suke suna diba domin su karya,
   Itama Nawaz  ta gama soya kaskon ƙarshe tana tunanin yadda zata sauke man da tayi suyar dash Naufal ya fito yana dariya "Aunty yau ashe better kikace muci! Wannan irin Natural delicacies haka" hakanan Allah ya ɗora musu son Nawaz da ganin girmanta tun lokacin da sukaje Zaria.

  Murmushi mai kamar dariya Nawaz tayi tare da cewa "Nidai bar wannan tsokanar taka ka taimaka ka daukemin man nan ka kaishi store ka adana Saboda da zafi Sosai kada wani ya ƙone"

SARFRAZ Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin