21&22

5 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*21*

*✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*

No wonder sai barci nakeyi babu fullstop ba coma..

  Amma kuwa Fatima bata kyauta min ba wallahi.

   Nawaz ce ta shigo "Assalamu alaykum mummy tace na Duba Wai koka gama shiryawa,

   Cewa Yayi "malama kimini jaje don Allah....

  Nawaz tayi murmushi "jaje name pah?

Fuskar tausayi SARFRAZ Yayi "Dana fita daga nan gidansu ABDUL na fara zuwa, anan ya kawomin tea da doya....

  Ashe acikin ruwan tea d'in kanwarshi ta zuba kwayoyin sa barci guda biyar wai saboda yasha yayi barci saboda baya iyayin barci....

   Mu Kuma bamu saniba nasha, gamu da tafiya a gabanmu....

  Yanzu yaza ayi kenan.
Nawaz tace kada ka damu kai dai  yi sauri ka shirya....

   Mummy ce ta fara kwala mata Kira *Nawaz Nawaz,
   Amsawa Nawaz tayi "Na'am mummy ganinan Yana wankane be fitoba...

  Da sauri ta fita zuwa wajen mum,
  Mum ta kalla tadanyi murmushi "mumy ba dazu driver yace zai tafi jigawaba, shine nace don Allah idan be tafiba mu tafi tare, kinga Sai ya rage mana hanya...  

   Banaso tukin yayiwa SARFRAZ yawa,. 

  Dad'i mummy taji ganin Nawaz ta nuna damuwarta akan SARFRAZ d'in.....
   "to daughter kada ki damu bari nayi mishi magana,

   Mum na fita naw6az tayi d'akin SARFRAZ Da gudu, cikin rashin Sa'a ta samu ya shiga wanka,,,  fitowa tayi tana jin dad'i zataje taga ummin ta.

   umma ce ta fado mata "oh koya jikin umma Oho, gaskiya ta maru domin SARFRAZ bai sassauta mataba....

    dai dai nan mummy ta shigo tare da driver,
   Akwati biyu ya dauka ya fita, Nawaz ta dauki d'aya zata bishi,  nan mummy ta hanata

   "haba naywaz kin manta Bakida Lapia ne,  ki bari yanzu zai gama, idan sarfraz ya fitoma zai tayashi kinji.....

   "to Nawaz tace sannan ta samu guri ta zauna.....

*GIDANSU NAWAZ*

umma nagani ta tasa fauziyya a gaba "wallahi fauziyya idan baki samomin bokan dazai sa nawaz tabi duniyaba wallahi zamu raba jaha.....

   tun tuni sai kashe kudi nake a banza, aiki  bayayi, yanzuma ji rashin mutuncin da aka mini kuma ta sanadinta... Amma ko abin ya dameki ki tashi tsaye.

  fauziyya tace "umma kiyi hakuri don Allah, kuma kibani kwana biyar saina nemo mana hatsabibin boka aduk inda yake......

   umma tace na baki amma ki tabbatar aikinshi Kamar yankan wuka yake....

   to umma zan ƙoƙarta cewar fauziyya tana Mikewa "bari naje gida mamarshi zatazo yau, kada tazo bananan kinsanta da gulma donma a tsaye nake..  ..

  to ki tafi Amma idan ta tafi ki dawo......

   *SARFRAZ*

  ya shirya Tsaf ya fito amma daka ganshi zaka gane akwai damuwa a tare dashi,  fitowa gurin mummy yayi.
  "mummy na shirya, gashi kuma kaina ciwo yake dakyar in zan iya yin tu'kinma,...

  dariya mummy tayi "SARFRAZ kenan, ai Bakada matsalar tuki, domin y'ar uwar ka ta nemar maka sau'ki, tace driver ya kaiku jigawa inyaso sai Kai ka karasa daku Maidugurin,
  
  Murmushi yayi "Allah sarki malama Inaga ta gane banajin dadine,
  Murmushin mummy takuma yi "uhm kundaifi kusa.....

SARFRAZ Where stories live. Discover now