49&50

1 1 0
                                    

*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

* 49*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

     Sai wani mazurai takeyi, ita ala dole babu mai rabata da sarfraz.
    "Sarfraz zo nan!" cewar hassu tana daɗa cin magani, Ai kuwa da sauri sarfraz ya miƙe ya karasa kusa da hassu, shima sai kallon Aayaan ɗin yakeyi.

    Farouk ne yace "hassu ki barshi yazo gurin yayan shi mana, bakiga sunyi kama da juna ba? *_(Shi ɗin ma bawai yasan shi bane illah dai yagane SARFRAZ ɗin da Aayaan ya gama bashi labarine, duba da Yadda kamanninsu ya nuna a fili)_*

      Chuno baki Hassu tayi sannan tace "bazai zoba" Tare Da rungume sarfraz ɗin.  Shima SARFRAZ saiya ƙara rungume hassu sannan shima yace "bazai zoba".

     Aayaann kam sai abin ya bashi dariya yadda SARFRAZ da Hassu suka rungume juna kamar zasu haɗe, ga mazuran da hassu takeyi, bandi ya kalla Sannan yace "wai yaushe suka saba ne haka? Bayan naga ko cikakkiyar wata biyu ba'a yiba".

       "Hmmm ai waɗan nan ka kalle su Kawai, don nima Babu Yadda banyiba amma ganin abun yafi ƙarfina shiyasa na zubawa sarautar Allah ido, itafa keyi mishi wanka, ita keyi mishi komaima, to ƙarshe ma bari kaji gado ɗaya suke kwana rungume da juna...

    😳zaro ido Aayaan yayi "Lallai, ikon Allah, kace abin Babba ne! Shikam Farouk dariya yakeyi Tare Da nuna Hassu yana cewa "Ashe ɗa kika tsinta, to aini danasan da labarin nan da tun tuni Maman SARFRAZ nake ce Miki..

    Ɗan murguɗa baki Hassu tayi " ina ruwanka? Ai kai wallahi bakada amana, daga cewa ka taimaka shine zaka wani nemo yan uwan shi, to basai muga wanda zai raba muba.

      Shima dai sarfraz saiya murguɗa baki sannan yace "ina ruwanka? Ai kai wallahi bakada amana, daga cewa ka taimaka shine zaka wani nemo yan uwan shi, to basai muga wanda zai raba muba.

      Me Aayaann zaiyi inba dariya ba "aaah Lallai Ashe Hassu tazama role model ɗinshi, wato duk abinda tayi shima sai yayi.....

    Shi dama Farouk tun tuni dariyar yakeyi, abin kamar a Film..

  Guri Aayaan ya samu ya zauna sosai sannan yace "hassun SARFRAZ yanzu ya kikeso ayi to?
   
     Ɗan kallonshi hassu tayi Sannan ta wani basar irin ita isasshiyar nan, saida ta ɗauki Kusan minti Uku Sannan tace "kawai mu Yanzu Bama buƙatar taimakon ku, kawai ku tafi ku barmu, inyaso Ni sai in siyar da su gwalbo mukai kuɗin chan Asibitin da za'a yi mishi maganin.

    Tuntsirewa da dariya Farouk ya kuma yi "wai ke in banda abunki meye Abinda ya shafe ki dashi? Naga ga dan uwanshi ko, to kibari su tafi mana! Ke meye naki?

   Daɗa ƙanƙame sarfraz hassu tayi "wallahi baku isa ku rabamuba,  ina ruwanku damu, kunsan kuna sonshi kuka bari ya ɓace?
      Shifa Aayaan Abin harya fara sashi tunani, Wato haɗuwar jini ma wata abace kenan, yadda yaga hassu ta dage yasan idan aka rabasu zata iya shiga Wani hali, duba da Yadda shima yaketa fama da damuwar rashin Nawaz

   Kwantar da murya Aayaan yayi "haba ƴar ƙanwata! Ai ki kwantar da hankalinki domin ƙafarki ƙafar sarfraz, babu Wanda Zai rabaku ko don wahalar da kikasha dashi.  Yanzu abinda nakeso shine ki haɗo kayan ki kizo mu tafi tare.

    Cewa tayi harda bandi amma Koh?

   "In banda abinki dama ya za'a yi a tafi ba tare da yaya bandi ba?

  Mota suka shiga Dukansu suka tafi gidan baffa malam, anan Aayaan ya shaida mishi cewa zasu tafi da sarfraz tare da su hassu amma insha Allah ba za'a daɗe ba zasu dawo, domin idan Allah yasa anyi aikin a Sa'a ba za'a wuce wata Uku ba Komai zai daidaita...

SARFRAZ Donde viven las historias. Descúbrelo ahora