*🎀 🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*91*
*SECOND TO THE LAST PAGE 😭😭*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Ko motsa yatsanta ta kasa yi sai zallar gudun da zuciyarta takeyi, wata Irin fargaba ce ta kama ta wadda ko a aurenta na fari bata ji irin taba.
"Ashe haka Nawaz taji! Lallai Nawaz nada haƙuri domin ita kanta da ta taɓa aure abin ya bigeta balle wadda bata taɓa aureba kuma bata samma wanda aka aura mata ba"
Da kyar ta dawo cikin hayyacinta, ba tare data cewa Aseey komai ba Kawai ta miƙi hanyar sasan da su baffa suka sauka, so take taje taji waye ya shirya mata wannan manaƙisar.Tsabar saurin da takeyi yasa lafayarta ya fara warware wa da kanshi, bata jira komaiba ta ƙarasa cireshi da kanta, Nannaɗe shi tayi ta ɗora a saman kafaɗarta tana ci gaba da tunkarar sashen.
Warwarewar da lafayar tayi sai ya ƙara bayyanar da duka surar mummyn a fili, barin ga kuma saurin da takeyi hakan yasa duka jikinta ke juyawa tako ina musamman mazaunta, kuma dama su take ɓoyewa kullum cikin lafayar, sai lafiyayyen gyararran gashinta daya sauka har gadon bayanta.Colonel ne tafe da Aayaan suna maganar yadda za'a bullowa Mummy, basaso taji zancen a bakin wani, sunfi so su faɗa mata da kansu Saboda Abin zaifi zuwan musu da sauƙi. Aayaan ne ya taɓa Colonel yana nuna mishi Mummy Wadda ta nufosu cikin wani irin sauri, "Daddy da Alamu wani yaje ya faɗa wa mummy"
Cirko cirko sukayi suna jiran mummy ta karaso gurin su saboda suga yadda za'a kare, abinda basu sani ba shine sam Mummy bata ma gansu ba, gaba ɗaya hankalinta da tunaninta duka yana hanyar kofar ɗakin su baffa.
Ganin ta wucesu batace musu komai ne yasa suka gane bata gansu ba, zata ɗaga labulen ɗakin su baffa kenan taji baffa yana cewa "Aini mehtab ta gama yimin komai a Rayuwa, tunda nake da ita ban taɓa yin abu tace baiyi ba, tun Muhammad yana raye ko kara na ajiye bata tsallake wa, kuma har bayan ya mutu bata rage komai daga abubuwan da take yimin ba, Allah dai yayi mata Albarka ya albarkaci Aurensu, yasa shine hanyar da zata shiga Aljannah.....
Jin wannan Maganar da baffa yayi akanta sai mummy taji gaba ɗaya gwuiwarta ta sage, bata da wani sauran kwarin gwuiwar zuwa ta samu baffa tace mishi batason auren, juyawa tayi da nufin ta koma daki domin zuwa yanzu ta amince cewa Auren ta da colonel A Rubuce yake.
Ganin colonel tayi tsaye shida Aayaan, da alamun ma ba Yanzu suka ganta ba, ji tayi bazata iya cigaba da tsayuwa a gaban suba, wai wannan Abin Kunyar har ina! Fisbilillah ace kamarta ce wai akaiwa auren dole, ta gefen su Colonel ta wuce ba tare data ce musu komai ba.Hakan saiya darsa wa colonel tsoro a cikin zuciyarshi, yaso ace tayi masifa,tayi jaraba Saboda ta fitar da duka damuwar ta, wannan shirun yana nufin Akwai sauran rina a kaba kenan.
Da ɗan sassarfa ya ƙarasa kusa da ita tare da ɗan shan gaban ta "Pls ki tsaya ki saurareni, wallahi shirun nan ƙona ni yakeyi, koma me zakice pls kice.
Kaucewa tayi zata cigaba da tafiyar ta, besan sanda yasa hannunshi ya riƙe damtsen taba "pls ki saurareni, beat me, slap me or do anything you like, wallahi mehtab da gaske ina sonki, kuma bawai nayi miki karfa karfa bane saboda na nuna baki isaba, ƙaunar kice tamin yawa a cikin zuciya ta.
Wani iri mummy taji a damtsen ta, wani yamm gurin yakeyi mata, ƙoƙarin kwace hannun ta tayi ya kuma riƙe wa da karfi, "pls ka barni mana"
"Promise me bazaki tafi ba koda na sake ki"
"Eh bazan tafi ba, sakeni"
Sakin ta yayi yana daɗe babbake hanya wai duk don karta wuce "pls mehtab uzurin ya isa haka, hakurina ya ƙare akanki, kullum kice saboda Madam ɗina ne bazaki Aureni ba, to yanzu ma babu ita amma kin ƙi yarda dani a matsayin miji, anya kuwa zaki taɓa kauna ta??
![](https://img.wattpad.com/cover/320786670-288-k864880.jpg)
ESTÁS LEYENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...