15&16

5 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*15*

✍🏻by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji 

Sakin hannun yayi, yai igniting d'in motar yahau titi.......

    Tafe suke tana rokonshi "nidai Don Allah safraz ka kyaleni wallahi ni ba irin wad'anda kake tunani bace.....

   Murmushi yayi "kingane koh!  Zama irin hakan ba wahala bane domin Suma Wanine ya maidasu haka,  kinga kenan Kema zaki iya zama koh?

   "Amma SARFRAZ ban ta'ba tunanin zakamin hakaba wallahi, domin ni na daukeka tamkar yayan nawa dakace....
   Kuma ni duk atunanina kai kamiline......

    Kashe mata ido yayi had'e da d'aga mata gira.... "kada ki damu ai hakan nake, kinji?
   
    Amma kinasona?

"taɓ ai wallahi gara na mutu dana so  fasikin mutum....

   "haba sister maiyasa har zakiyi judging d'ina tun banyi miki komaiba... 🤨

   Ai nasan zakayine shiyasa.....  But nasan Allah zai kareni kuma wallahi babu abinda zaka iya yimin.....

    Jitayi yayi parking,  kallon glass tayi tagansu a gidansu SARFRAZ.

    Fita yayi yazagaya,  bud'e mata mota yayi "madam Mun iso!

    Harara ta balla mishi "wallahi baka isaba,  domin ni gidanmu zaka maidani, saboda bazan kuma kwana a gidanku ba, fitsararka ta isheni wallahi ......

    gabanta ya tsuguna "please malama kiyi hakuri, wallahi karya nakeyi 
   Kuma wallahi  wasa nake miki, domin abinda kikayimin a asibitine da kuma gurin mai awara shine nace saina rama ....

   Kallonshi tayi "hmm wai yanzu so kake na yarda dakai?

   "wallahi malama kawai yimiki nakeyi saboda naga kin tsorata sosai ne....."

    cikin idonshi ta kalla a ɗarare,  ganin nadama tayi tsantsa.....

    zancen zuci take "to shi inba dama bashida  kunyaba ya za'a yi ya ri'ka yimin wadannan maganganun kuma hankali kwance......"

muryar SARFRAZ taji Yana cewa "malama kin yarda da abinda nace? '

   Rufe idonta tayi "wallahi ni kawai ka maida ni gidanmu,  babu abinda zan kumayi a gidanku tunda Kai Bakada kunya......"

    kafin ta rufe baki taji ya dauketa chak yayi hanyar falour da ita.....

   wuntsil wuntsil ta farayi "wallahi kasakeni, kasan dai haramne ta'ba macen da ba Matar kaba,, Amma kullum burinka ka daukeni,  Ka maidani Kamar wana yar tsana........ "

    banza yayi da ita..  dai dai nan ya Isa parlour,
  Mummy dake tsaye ta tawo da sauri "SARFRAZ wane asibiti kaje ban gankaba?
     Maza kwantar da ita a sofa dinnan.....
    Meyasameta? Me likita yace? Ya fad'a maka matsalar?

    sarfraz da dariya ta kusa kamashi cewa Yayi "mum to yanzu wace tambayar zan Amsa?

    Kwantar da ita Yayi Gefen mum,  harda Gyara mata kwanciya Kamar dama chan barci takeyi.....

   mummy da take a rud'e cewa tayi "halan allurar barci akayi mata?
   yanzu nidai SARFRAZ don Allah ka fad'a min Meyasameta?

    "ehmmn mummy munje aeydan hospital ne,  sannan kuma likita yace wai ciwon marane, sannan wai period takeyi kuma yace wai tanada strong......

   Dasauri nawaz ta Mike "wallahi mummy karyane ba Haka likita yaceba! Domin a zatonta zaice tanada strong sexual desire ne....  Batasan zaice strong contraction bane......

SARFRAZ Where stories live. Discover now