*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*51*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Yadda yaga Nawaz ta ruɗe Kamar taga dodo ne yasa ya tsaya a Inda yake "sweetheart wai meyasa kike mugun jin tsoro nane, ji abinda kikeyi fa, sai kace kinga dodo"
Itama Nawaz sai taji kunya ta kamata, ɗan natsuwa tayi kaɗan amma kanta na kallon ƙasa.
Hakan da tayine ya ƙara ba Aayaan damar daɗa ƙare mata kallo, Lallan kafarta dana hannunta yakebi da kallo, Aayaan yanason lalle sosai, saboda yasha taya Mummy idan zatayi, kuma Bayan tayi yaita kallonta yana Cewa tayi kyau...
Maida kallonshi yayi kan hips ɗinta, "a'a to wai da wauta ce tasa banma San yadda takeba ko kuwa? Sosai hips ɗin ya baje a cikin doguwar rigar, har wani ɗan tudu yayi daga gefe, koda yakai idonshi kankirjinta nanma dai zare ido yayi...
Gashin kanta kuwa har wani ƙyalli ƙyalli yakeyi, wani irin Abu yaji ya tsirga mishi, gyaran murya yayi Domin jin Muryar tashi yayi Kamar ta dishe "sweet heart meyasa kika gudu kika barni da ciwo a zuciya ta? Kinsan da gaske Ina sonki kuma ina ƙaunarki.....
Ɗan ɗago da Ido Nawaz tayi da nufin ta saci kallonshi, ai kuwa charaf suka hada Ido, Anan ne yaga usulin Khan da Nawaz tayi....
Da ɗan sassarfa ya ƙarasa kusa da ita, ɗaga ta sama yayi sai yaji ta ƙara Nauyi fiye da da, "Sweet love me Inna take bakine kika Zama Yar lukuta? A hankali ya sauketa sannan ya haɗa ta da kirjinshi ya rungumeta, a yanda yakeji a zuciyarshi da ace zai iya fasa ƙirjin shi ya sata a ciki da Hakan zaifi yi mishi daɗi, hannun shi ya zagayo yayi wrapping a ƙugunta, gaba dayansu bugun zuciyarsu saiya tsanan ta kuma a tare jikinsu ya bada wani Ni'imtaccen dumi da kamshi....Shiru Nawaz tayi tana sauraron bugun zuciyar Aayaann, amma zuciyarta Fall tsoro kasancewar ta ita kaɗai kada Aayaan yayi mata wani abu..
Ƙasa yayo da Fuskarshi dai dai saitin kunnenta yace "please dear ki bani dama just one kiss.
Namma dai Nawaz shiru tayi tana sauraron shi, bataso tace zatayi mishi Musu, domin Babu maceci sai Allah, ajiyar zuciya tayi haɗe da furzar da numfashi mai ɗumi daga bakinta "yaya Aayaann pls ka sumbaci goshina kawai.
"Nop mouth To mouth Nidai nakeso, a taimaka min pls. Sannan ya daɗe haɗe ta da jikinshi sosai.....
Wani irin Abu Nawaz keji yana bin duk illahirin jikinta (tsumin inna ya Fara aiki 😉) ga wata uwar kasala data saukar mata nan take, gaba ɗaya ta ƙasa yin wani kataɓus,.
Aayaann kam ji yayi tsayuwar tayi yawa, ga duka gwuiwowinshi sunyi weak, Kujerar Inna ya ƙarasa ya zauna tare da tattare Nawaz zuwa saman cinyarshi, Sannan yayi cuddling ɗinta, yau kam Nawaz ta bashi mamaki domin sam babu wannan tsiwar Tata, tayi shiru kamar Ruwa ya cinyeta....
Ita kuma Nawaz addu'a takeyi a zuciyarta akan Allah yasa hadiya ta shigo, kila Aayaan ya rabu da ita.
Sun daɗe a haka Kafin daga bisani Aayaan yace "an bani dama?"
"Pls kayi hakuri don Allah, baka faɗamin ina Mummy da aunty Aseey suke ba, da muhsien ma da kuma Mummyn SARFRAZ!
"Dukansu fushi sukeyi dake kuma sunce babu ruwansu dake tunda baki daukesu a komai ba.
Wani iri Nawaz taji har zuciyarta, tabbas bata kyautaba Amma ai Aayaan ɗinne ya hanata saƙat, kuma ya riƙa bata kunya."Ki shirya abinda zaki faɗa Musu idan mun koma, Domin ƙafarki kafata tare zamu koma in'sha Allah. Fargaba ce ta kama Nawaz Lokaci guda, ita batasan me zatace Musu yasa ta gudu ba, kuma bazama ta iya kallon suba "ummina tasan bananan?
Ɗan murmushi Aayaan yayi "hmm ai ummi ma cewa tayi ta cire hannu Babu ruwanta dake, wai kin nuna basu isa dakeba...
"Wallahi yaya Aayaann duk kai kaja min wannan abun, nace maka kadena taɓa min jiki amma kaƙi, kuma saboda Rashin ta ido ma a gaban Mummy fa ka fito dani daga dakinka, baka tunanin suyi wani tunanin.
أنت تقرأ
SARFRAZ
عاطفيةLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...