*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*41*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Babban Doctorn ne yace "wace irin matsala kuma?"
Kusa dashi ya ƙarasa yayi ƙasa da murya sukayi magana yadda su baffa bazasujiba.
Shiru yayi yana tunanin yadda zai faɗawa su baffan wannan gagarumar magana, duba da yadda ya gansu yasan ba masu wadata bane.Natsuwa yayi sosai Sannan ya maida hankalinshi guri ɗaya yadda zai samu abinda zai musu bayani, sannan yayi gyaran murya " Baba ansamu Babbar matsala amma dai za'a iya maganceta.
Baffa yace "likita faɗa min wace irin Matsala aka samu? Tun ɗazu kunata ƙus ƙus amma bakace mana komai ba!"Baba majinyacinmu ba ciwon mantau bane ya kamashi, kwakwalwar shice ta goce daga ma'ajiyar ta. Amma idan akayi aiki ana warkewa sai dai ba'a nan ƙasar akeyin aikinba.
Wata zufa baffa yaji ta sauko mishi, "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Lahaula wala quwwata illah billahil Aliyul azeem! Subhanallah! To likita yanzu ya za'a yi?
Gyara zama likitan yayi yace "ai ba ita kaɗai bace matsalar! Bayan wannan akwai hormones imbalance a tare dashi, kuma bincike ya nuna ciwonma ya daɗe Abokinshi.
A Tare hassu da baffa suka miƙe " likita badai kana nufin mutuwa zaiyi ba ko?
Ɗan murmushi doctor yayi "kada ku damu bazai mutuba, yanzu dai ku koma ku zauna, abu ɗaya ne damuwar shine kudin da za'a fitar dashi ƙasar waje ayi aikin.
"To likita kana ganin zai kai nawa? Baffa yace Yana daɗa daidaita nutsuwarshi.
"Eh to gaskiya baba bazan ɓoye maka komaiba, waccan shekarar mun taɓa samun mai irin wannan matsalar, kuma gaskiya a yanda akayi lissafi sun kashe kuɗi yakai kimanin million goma sha uku.Miƙewa baffa yayi haɗe da cewa "iye! Na'am! Miliyan nawa? Tabɗi aini a halin yanzu ko dubu ɗari ta kaina banida ita balle million.
"Calm down baba! Kada ka tada hankalinka, kasan komai Allah ya tsara ma bawa baya iya kauce mishi, yanzu abinda nakeso dakai shine ayita addu'a, saikaga Allah ya kawo wanda zai biya kudin aikin cikin sauƙi.
"To Allah yasa! ta malam bata wuce Ameen, amma a ƙarnin nan waye zai iya biyan million goma sha biyu don ayiwa wani aiki?
"Numfasawa Doctorn yayi "baba nace ka kwantar da hankalinka kuma kuyita addu'a, kuma inaso inyi maka albishir cewa akwai Wani babban soja da yake biyawa mutane kuɗi idan basuda hali, to shine nakeso idan yazo zanyi mishi bayani kila Allah yasa ya biya mishi.
To shikenan likita mungode, amma yanzu babu wani abu da za'a bashi wanda zai iya taimaka mishi gurin lafiyar shi? Kaga kuma yanada ciwo a jikinshi."A'a duka wannan babu matsala zan haɗa ku d wanda zai wanke mishi ciwon kuma zai baku magani.
Miƙewa baffan yayi "to likita mungode!
Tare suka fita duka zuciyarsu babu daɗi barin hassu da take ganin kamar bazai taba warkewa ba.
Kamar yadda likitan yace haka aka yiwa SARFRAZ dressing ɗin ciwon aka basu magani suka tafi gida.
Sai bayan sun koma gida ne baffa yayi wa bandi bayanin yadda sukayi da likita, shima bandi baiji daɗi ba, Sannan ya ƙara tausayawa sarfraz halin dayake ciki ..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kallon Nawaz ɗin tayi tace "sis don Allah kada ki tafi ki barni!
Take hankalin Nawaz ya koma kan Aseey "sis meyasa kikace haka? Ko wani yace Miki zan tafi gobe ne.
"A'a Kawai dai ina rokon Alfarma ne akan ki zauna tare damu har zuwa sanda zan koma England, saboda duk sanda naganki ji nake kamar ke ɗin jini nace domin nida mummy munyi burin samun yar uwa mace amma dayake Allah ya riga da ya gama tsara komai sai bata kuma haifar maceba sai Aayaan da marigayi..

YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...