*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONESadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx_Real integrity is doing the right thing, knowing that nobody’s going to know whether you did it or not._
Tafiyar ƙaddara..
BABI NA SHIDA
Rayuwar da aka gina shi domin Allah tafiya yake cike da Yardan Allah, duk wata nasara tana tafe da wanda Allah ya baka, wannan shine adadin farin cikin da Almamoon wanda yayi saukar Alqur'ani wanda yayi daidai da kammala makaranta shi na Sakandiri, kuma Allah cikin ikon shi ya samu tallafin karatun jami'ar Maryam Abatcha dake garin Maradi...Duk wani ƙaddara ta fara ne daga wannan yankin, duk wani tafiya daga nan ta fara, sai gashi cikin Ikon Allah tafiyar ta kuma canzawa izuwa Maradin.
Bayan kwashe watanni suna jiran sakamakon, yana fitowa shi da iyayen shi suka kuma dawowa Maradi domin su abinda zasu iya mishi, Allah cikin ikon shi ya kuma basu tallafin wasu mutane, suka taimaka musu har aka kammala cuku-cukun makarantar, sannan suka dawo dashi gida, aka shiga fadi tashi yadda zasu sami damar nima mishi dakin makaranta domin nauyin karatun shi aka dauka su kuma zasu biya kudin daki da na littafai, abin tausayi wannan karon ma akwatin asusun ta kuma fasawa aka samu kudi me yawa, sannan ta bawa Malam suka dawo Maradi da Almamoon aka kuma biyan kudin makaranta. Sannan suka koma.
Cikin kewar shi suke kallon shi.
"Kasan waye kai? Ka kuma san dalilin ka na zama a gurin nan, akwai al'amarin da zamu gaya maka amma a yanzun shekarunka basu kai nauyin ɗaukar abinda zamu gaya maka ba.Jami'a ba kamar Sakandiri bane, a can gidan Yanci ne. Ba gidan da zaka zauna kayi laifi wani ya fito yayi maka fada bane, guri ne na kowa kanshi ya sani, dan Allah ka dubi girman Allah karka samu kuka, kamar yadda kace zaka sanya mu, farin ciki ka cika mana burin mu, mun san ba iyawar mu bane yasa kake kare kanka Allah ne yake kare ka, zaka shiga inda babu kunya ko tsoron Allah, don Allah karka watsa mana kasa a idanu, ka taimaka kayi abinda muka turaka Allah ya tsare maka imanin ka."
Kallon su yayi yaga yadda suke share kwalla, sai yaji a ranshi akwai abubuwan da ya dace ya tambaye su. Amma kuma,
"Babana me yasa kuke son na rayu a haka? Bayan akwai matsala idan wata rana."Rufe baki Innar shi tayi tana kuka tace.
"Ban da karatun nan bamu muna biya ba, wallahi da ka fasa, tsoron goben ka muke ji, shi yasa muka lullube farin cikin ka, kayi hakuri kayi wannan tafiyar shima kamar tafiyar ƙaddara ce, babu wanda yasan me zaka taras a gaba, don Allah karka yarda wani ya yaudare ka, kaga kai ɗaya muka mallaka, don Allah ka rufa min asiri."Kallonsu yayi yana son tambayar su, amma a yadda yake hango firgici da tsoro ya saka shi had'iye tambayar, ya haɗa kayan shi da wanda yake daya sakamakon dan kudin da iyayen shi suke bashi dukda ba wani samu suke ba, dan Tun lokacin da yace musu yana son fara aiki a kasuwa suka daina barin shi yana niman abubuwan bukata, wani lokacin har kuka yake me yasa ba zai tafi kasuwa ba. Haka suke kokarin faranta mishi amma sabida sun hana shi sake yasa shi hakura.
Yadda ake kaf-kaf dashi wallahi ko mace sai haka, akwai ranar da ya faɗa ai yana da yan mata, a makarantar boko, ranar sai da Innar shi tayi zazzaɓi, idan ta kalle shi sai ya fashe da kuka, tun yana daukar abin wasa har ya shiga tashin hankali, shi yasa ya daina subul da baka, domin yana tsoron abinda zai sami iyayen shi.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....