🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN DA TAKWAS.
Kura mata ido yayi yana mamakin yadda Allah ya daura mata son kanta, sunkuyar da kai yayi yana kallon shaddar jikin shi.
"Zan nima maka maganin ko kurwanka ta kama ta sake maka shi, Insha Allah wannan masifar da me yayi kama."Bai ce mata kome ba, haka dai ta gama masifar ta, yayi mata sallama ya bar gurin. A cikin kwanakin bai da lokacin kanshi domin tun da ya rabu da Maimunari ya ajiye aikin soja, sai ya koma kasuwanci, kuma dama yana kasuwancin bai mai da hankali bane. Amma yanzun da ya mai da hankali yana ganin Cigaba sosai.
Yau da la'asar ya shirya zuwa duba Maimunari, yana isa da kayan marmari da ya kawo mata,ya samu basu asibitin. Ya tambaya aka ce ba. A san inda suka tafi ba,bai kuma tabbatar da ya rasa Maimunari ba sai da yake gidan Abie ya samu a rufe nan ya gane cewa sun tafi da ita wani gurin ne, haka ya kira Khalil ya gaya Mishi. Amma babu wani labari, da ya sami Abbu da zancen cewa yayi.
"Ban san inda suka tafi ba, amma koma yayya ne ai Mahaifiyarka ta bukaci haka, dan haka idan na isa kuma na haife ka ka kyale musu yar su ta huta, ita ba matar ka bace Yanzun sannan kuma ba zai yiwu uwarka tana tozarta su ba, dan haka na gargade ka da ka fita hanyar ta, ko kuma na sab'a maka."
"Amma Abbu!" D'aga Mishi hannu yayi tare da cewa.
"Itama iyayenta suna SONTA, kuma babu wanda zai yarda ayi ta wulakanta Mishi d'a. Dan haka ka tafi ka zauna da uwarka ita ka barta da nata iyayen, saboda kai ta saka su a kotu, saboda kai ta wulakanta su, duk sabida soyayyar ka. Indai har zata aikata haka saboda tana son ta dawo rayuwarka amma uwarka taki meye yasa ba zaka kyale ta ba? Me yasa ba zaka hakura da ita ba? Tayi kokari tayi kokari. Don Allah ka kyale ta ta huta Ubangiji ya bata wanda ya Fika kai ma Ubangiji ya baka wacce ta fita."Jikinsa ne yayi mugun sanyi, sannan ya mike a hankali tare da nufar hanyar waje.
"Insha Allah na hakura da ita, Nagode sosai Abie"Tun daga ranar yayi wani irin sanyi, magana ma bata dame shi ba, baya harka da kowa sai Khalil shima sai yana gari,.ana cikin wannan yanayin me niman auren Radiyah, suka turo har an gama magana, amma mahaifiyar yaron ta tawo da kanta, har gurin Hajiya Latifah.
Bayan sun gaisa tace mata.
"Hajiya Lateefah nice Mahaifiyar Safwan kawai jiya Mahaifin shi yace min sun zo nima Mishi auren yarinyar da yake nima bai gaya min ba sai da suka gama magana. Toh gani nan nazo na gaya miki gaskiya. Bana son had'a zuri'a dake! Ba dan kome ba sai dan mijinki shege ne bai da asali""Keke!"
"Ke yi kasa da muryanki! Indai har uwa irinki zata kashe auren danta ranar da ya kwanta da matar shi, meye laifina dan nazo akan a fasa auren dana da Yarki a? Dan haka ita da kika saka ta wulakanta iyayenta. Kin ga ina son kaina da arziki ba zan so dan da na haifa ya maka ni a kotu saboda yar ki ba.A takaice dai ba zan tab'a barin shi ya auri yar ki ba, da ya auri Yarki wallahi gwara ya mutu bai yi aure ba, balle kuma ga mata kaca kaca."
Ta mike tana kad'a keyn motar ta, tare da ɗaukar jakarta, har zata fita tace mata.
"Wallahi kamar yadda kika saka iyayen Maimunari kuka haka zaki yi kuka ga yara mata gasu nan a gabanki"Sannan ta fita, yadda kuka san gumki haka ta koma, tana cikin wannan yanayin, Khausar ta shigo dauke da jakar kayanta, niki niki. Idanunta cike da kwalla,
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mistério / Suspenselove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....