https://www.wattpad.com/1113398663?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2BxTW4N%2Fi3%2B1dAQX5gbjmfTxgxiRMRb8Nl%2F50OD4pV94UP35Ih%2FrlfzEmYSOqSePFjk4F6wQI4BmDexcUn1v%2B6q7S5wMuA0Uc%2FC5OPGYtcFd9ON0zvTrtgtJg8WkJ5LAn
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN DA HUƊU.
*Ana ta zare idanu 🙄🤡🙋🏾♂️*
Ni a karan kaina nasan ina son Mohan, kuma shima ya san da haka,shi yasa na b'ata lokaci ina hira dashi tare da bashi labari. Kafin na kalli agogon dakin na zare hannuna cikin nashi.
"Zan tafi!" Na fada mishi,
"Bana son kiyi nisa dani, amma babu yadda na iya, Allah ya kiyayye hanya, ki kula min da kanki" murmushi nayi mishi sannan nace.
"Insha Allah! Amma ka godewa Allah da Abbu da Abba da Wallahi sai dai ka nime wacce take." Rufe min baƙi yayi da nashi.
"Don Allah a bar zancen kawai, wallahi ina son mata ta haka." Cizon hannunsa nayi tare da kura mishi ido.
"Ahhh!" Sannan ya sumbaci gurin, yana murmushi.
"Ina sonki"
Girgiza kai nayi, tare da ɗaukar jakata na fito. Na same su har wasu sun zo.
"Don Allah, ki tuna yana da kane irin wannan sakawa a lungu, baki daya. Toh Allah yasa kar muzo cin shinkafar amarya a hana mu ganin ango."
Kasa magana nayi domin Salman yana da raha kamar dan Film.
"Toh zan tafi, na gama abinda ya kawo ni Niamey.""Ke dai kice zaki gudu an kusan amarcewa"
"Sai anjimar ku" na musu sallama na tafi, sannan suka shiga dakin sun same shi kamar mai barci.
"Munafuki idan zaka bude ido ka bude domin yarinyar ka ta nuna mana ka farka." Inji Dan Ba'are Ya fada tare da kallon shi. Gyara kwanciyar shi yayi tare da cewa.
"Dan Ubanka idan ban tashi ba sai ka d'aga ni"Nan suka shiga fadar su ta gado, dan zance ta gado. Kafin suka shiga taimaka mishi yayi wanka da alola, yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi Allah Sarki. Yana yi yana huta. Haka ya sauke sallah da yake kanshi, ana hira da shi Ammyn ta. Shigo ita da Maman Hanan ko inda suke bai kalla ba, sai b'ata rai yaƙe,
A hankali sauki yake samuwa, tare da sanin kulawa daga yan uwan shi, da mahaifin su amma fir yaki amincewa Hajiya Lateefah, sosai yaki sake jiki da ita, idan ya fara waya da Maimunari kuwa kowa sai ya tashi inda yake, domin kasa kasa yake maganar kamar ba zai yi ba, baka tab'a jin abinda yake faɗa.
Satin shi daya aka sallame shi saura sati biyu bikin su. Ba karamin shiri ake ba,duk ta inda kake tsammanin abin ya wuce haka, bikin saura kwana tara aka kai kayan lefe, akwati ashirin da hudu (😏😒☹️ saura kuce zuki tamalle🤣😂) tare da kyautar motar sabuwa jaguar, kukan da Innah keyi Allah kadai ya sani, domin babu wani da zata ce danginta ne sai Al'ummar Annabi, sune suka mata kara, dama tun kafin a kawo kayan Radiyah ta turo min, da ranar da za a kawo, tuni na dawo gida na shiga Niman inda za ayi mana abincin alfarma. Tare da kayan ciye ciye dake ban san yadda ake abin ba, sai da ta gaya min.
Na kawo kayan drinks aka ajiye, sai da na gama kome tare da bawa Innah kudi me yawa ta basu tukwaici. Aikuwa haka ce ta faru. Amma Innah taki amsar motar da gwala-gwalan cikin kayan.
Atamfoffin kuwa kamar shagon sayar da kaya za a bude, haka akayi ta kirga su har suka gaji suka bari, tunda na ga kayan gabana ya tsinke, ban kuma samun kwanciyar hankali ba, ga mugayen mafarkai da suka sani a gaba, a tsakanin kwanakin har saukar Alqur'ani sai da nayi, ana saura sati za a saka ni a lalle na koma gida bani da kawa bani kowa sai su Salihu Muhmuda, sune abokaina dan haka da su muka yi ta zirga-zirga.
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
ESTÁS LEYENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Misterio / Suspensolove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....