BABI NA TALATIN DA UKU.

1.1K 219 26
                                    

https://www.wattpad.com/1108262550?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=cavWiGGyBrCAo%2BWqCLglY3Gs%2BgN1rFoDPpKB0zWz6PoxIH7kodf8pwkn%2Bapj%2BNu2jcr3lLRQ1jZyx3x0Y0w3eVNqEUJhy%2FQFfQ%2FqU6I47IboRfk%2Fq6JpeUV04y6Fe%2BIf

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA TALATIN DA UKU.

Ban tashi sanin inda kaina yake ba sai a gadon asibiti, a hankali na bude idanuna. Da nake ganin dishi dishi, d'aga hannu nayi kamar zan yi wani abu. Naji ana magana kamar daga can nisa, maganar ma amo take min kamar yadda nake tsammanin amsakuwa na saka.

        A hankali naji an kuma tsikara min allura, nace.
"Wash" daga haka ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai washi gari da safe. Na bude idanuna na hango Baba yana zaune.

         Kokarin tashi nake, Baba Mari ta mai dani.
"Koma ki kwanta yar nan Sannun ai kin auna arziki, tunda gashi kin farka da kanki." Kallonta nake tare da kuma kallon dakin.

"Sannun Maimunari, Allah ya baki lafiya yasa Zakkar jiki ne, inji Innarki wai a gaishe ki" inji Baba, na san ya fada ne kawai amma bawai dan Innah ta saka shi bane, dan haka na mike dakyar na nufi ban daki. Da taimkawar Baba Mari nayi wanka da alola. Sannan ta mika min doguwar riga na saka, kafin ta kuma taimaka min na fito waje.

    Sallah nayi da wanda yake kaina, ina cikin yi Hammah Mohan suka shigo tare da dan Ba'are. Gaida Baba yayi fuskar shi a daure tam, sai harara ta yake. Yaki min magana.

   Tea ya hada min sannan ya mikawa Baba Mari, ta fara kokarin ganin na sha, ture tea din nayi. Tare da kallon shi, takaici ne ya kuma kama shi. Ya mike tare da zuba hannun shi dukka biyu aljuhun rigar shi.

   "Me yasa ba zaka min magana ba?" Kura min ido yayi sannan yace min.
"Duk abinda zan yi a rayuwa ina niman albarkan iyaye ne me yasa da tace bata son alaƙar mu kika dage?" Ya tambaye ni, tare da zuba min ido, wanda suke cike da b'acin rai.

      "A'a Hammah Mohan, kai ne nake ganin zan samu nutsuwa da kai kace zaka d'aga min hankali? Sai na wuce diffa, kuma wallahi gurin Malam Ansar  zan tafi" na gaya mishi ina kuka.
"Sai me? Ki wuce diffa ki tafi duk inda yayi miki. Ina can ina faffutikar rayuwar da zamu yi saboda ke zaki b'allo min wata tashin hankali,

   Toh ki sani da kinyi kuskuren tafiya diffa da har abada kin rasani kenan, dan haka zaki tashi kibi Baba Damagaram, kuma kika sake ki kayi wani shirme."

   Mikewa nayi akan Abin sallah, na tako gaban shi ina kallon shi.
"Idan ka sani na koma can toh na rantse maka da Allah zaku nime ni ku rasa." Na gaya mishi,
Kasa magana yayi sabida yadda na kafe shi da ido, ina ƙoƙarin ganin ya yarda da abinda zan aikata. Kasa magana yayi sannan ya juya tare da cewa.
"Nag."
"Mohammed ka kyaleta ta zauna a nan Maradi tunda ga Iya Mari, ina ga idan ta zauna a nan hankalinta zai kwanta, itama Innarta hankalin ta zai kwanta. Babu amfanin a maida ita gida dole, tunda ga shi akwai inda zata zauna babu wani abu."

"Baba nawa Moonah take da zata bawa mutane zab'i? Ita wacece da zata bawa mutane zab'i?" Ya fada a sanyayye, abinda na lura nice yake Zafaffa min murya amma duk wanda ya fishi yana ƙoƙarin gaya mishi kowacce kalma cikin sanyi da nutsuwa.

"Bance dole ka zauna dani ba,
duniya tana da fad'i zaka iya tafiya akwai Dubun ka da suke buƙatar rayuwa dani, ka gane" na fada ina ninke kayan da nayi sallah dashi, a yanzun da nake jin haushin kowa, wallahil billahi azim duk wanda ya kuskura ya tab'a Ni zai ji magana me tsada.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon