BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.

1.2K 275 43
                                    

https://www.wattpad.com/1105787433?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Ja9wL7QqFEErjgU2q%2BSBeLU5C48TPF6alEcOeA68MXjwsxZkfzIB%2B1qokdEbQ55KLRjZ93ztdNSly6DP588o1P6bkl7taWFOl0ee6BP9d%2B%2F0Yz5SwmP2bjWvOwHDMKnB

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.

Shan gaban shi nayi ina kallon fuskar shi.
"Kace zai dauki tsawon watanin yana ciyar da wasu iyalin?" Tura ni cikin elevetor yayi yana me faɗin.
"Na gaji da tambayoyin, ba sai ka nuna min Dalibin lauya ne." Ya fada min tare da tsayuwa yana kallon gaban kofar,  shiru nayi kafin nace mishi.
"Kasan me? Kawai garin nan ya hadu, amma ya abin yake komawa ƙasa?" Na fada ina kallon shi, gajiya yayi da tambayar toshe min baƙi yayi tare da kallon yadda nake zare ido ina ƙoƙarin sai nayi magana.

      Haka muka shiga dakin tare da kallon ko ina, dakyar na shiga ban dakin nayi wanka da alola bayan na fito na samu baya d'akin amma ga kayana akan gadon dauka nayi na shafa mai, tare da saka kayan sannan na fito ina saka takalmi, kallon shi nayi domin yayi kyau cikin riga da wando sai gyara gashin da yayi, kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Kayi kyau, amma kuma kayan nan ya mai da kai wani babba dayawa, ka saka kananun kaya zaka fi ka kyau"
Na fada ina kallon shi, bai kula ni  ba sai aikin gaban shi yaƙe.
"Hammah, zo nan" na kira shi ina   a kujeran sa yake falon. Daure fuska na nayi, sannan na kuma kallon shi, na mishi alama yazo da hannu na.

   Shi kan shi mamaki ya gama kama shi abinda yaron nan ke mishi wallahi yana wuce gona da iri, bai musu ba. Domin ya lura Yaron na jin farin ciki ne dan haka ya nufi gurin shi cikin sauki da salama, ya tsaya yana kallon shi.
"Kawo kunnen ka!" Wallahi a tunanin shi abin arziki zai gaya mishi dan haka ya sunkuya tare da kallon bakin shi.
"Kunne nace" ya gaya mishi haka, mika mishi kunne yayi. Sai da ya gama ja mishi kunne kafin yace mishi.
"Wani ya taba gaya maka kai kyakyawa ne? Toh wallahi kai kyakyawa ne gaka kamar dan dambe gingimemme da kai kamar tsohuwar bishiyar kuka." Wato haka nayi ta yabon shi ina kuma rage mishi wani abun. Kallon fuskana yayi tare da cewa.

"Da alamu yunwa ce ta saka zuba kamar tsohuwar rediyo?" Had'iye yawu nayi tare da shafa cikina, ina kallon shi.
"Idan ka taimaki dan cikina Allah zai gina maka katon gida a aljanna domin yunwa nake ji, kuma Ni kamar mareniya ce" na fada ina had'iye yawun yunwa.

  Jan hannuna yayi muka fita, muna fita ya hango wani mutum da alama shima dan Afrika ne, wani irin juyar dani yayi tare da had'a ni da bango, kafin kaina ya kai bango ya kai hannun shi, tare da daidaita tsayin shi, ya kai fuskar shi kan nawa, kamar zai sumbaci bakina, zato idanu nayi ina kallon shi. Jikinsa ya matse nawa numfashin sa yana dukar nawa, kwayar idanun shi yana cikin nawa, baki daya na kasa cire idanuna cikin nashi mamaki yake bani yadda ya iya juyar dani cikin zafin nama, *Ka manta shi din soja ne* kuma haka ne fa? . Haka mutumin yazo ya wuce da wata baturiya a gefen shi. Sai da ya tabbatar ya wuce sannan ya d'ago ni.
A tsora ce nake kallon shi jikina yana kara sanyi. Kuma na kasa magana, baki daya kamar  wacce baya cinye min bakina.
"Rediyo me jini ya kai yi shiru?" Tura baki nayi ina me Cigaba da tafiya.
"Abokina babu magana ne?" Kara dauke kai nayi ina kallon cikin Elevetor da muka shiga. Daukar wayar shi yayi tare da dannawa ya manna a kunne, kafin ya fara magana,

    Buzanci ya juya baki daya kamar babu Hausa a bakin shi ko French, haka yayi ta hiran har muna fito, ganin kofar ta bude naka hannun shi mu tafi wayar ta fadi kafin na dauka ya taka, kamar zai bugani da kasa ya dauki wayar yana kallon yadda screen din shi yayi daga daga, gashi suna magana me muhimmanci ne da Hammah Khalil. Ranshi yayi mugun b'aci,
"Kasan abinda ka aikata min? Kasan Meye kayi? Me yasa baka da hankali ne? Kalli wayar yadda kayi min da ita? Wallahi baka jin magana mara hankali kawai, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin wayata na baka sauran canjinka"

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora