*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONESadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx_Tambaya suna yawa! Wasu ina iya amsa su, wasu kuma ina kallon su na wuce su basu da Amsar a lokacin.... Kuyi hakuri labarin nan dauke yake da Zanen kaddara wanda alkalamin ƙaddara ta rubutashi ba labarin soyayya bace da za a ci soyayya akwai a soyayya labari ne wanda zaka samu yana tafiya da asalin rayuwa ban ce labarin ya faru da gaske ba, sai dai labarin iya iya tafiya kamar yadda yake faruwa a wani kaulin, zaku yi hakuri dani nima kuma zanyi hakuri da ku, idan uzurina ya shigo zan jingine nayi sabgar gabana, idan kuma na sami sarari zan baku sama da yadda kuke tsammani! Banyi alƙawarin kyautatawa ba, amma nayi alƙawarin farantawa ban yi alkawarin zai yi dadi ba, amma nayiwa kai na alƙawarin zai badda yadda zai tafi, idan kuka duba taken labarin Journey of Destiny! Wato Tafiyar ƙaddara... Dan haka idan nayi kuskuren ku min Uzuri sabida nima Yar Adam ce! Idan nayi dai-dai ku tuna da kalaman ku da tunatarwa! Kuyi hakuri dan labarin Yanzun muke Littafi ba Ɗaya fatan Alkhairi 👏_
Harshen ka...
BABI NA BIYAR.Goge kwallar tayi tare da kurawa hatsin da aka kawo mata surfe, yau kimanin shekaru goma sha daya zuwa sha biyu, babu wanda ya tab'a ganin ta tayi fada da mutane, Allah ya zuba mata baiwar hakuri da juriya, ta kuma jure halin dan rikon su. Shi yasa yaron ya tashi da mugun kaunar su.
B'ata tab'a daga hannu da sunan dukan shi dan yayi mata laifi ba, sai Addu'a, da fatan shirya shi yasa mutanen gidan da suke, wasu ke jin haushinta, ga Mamoon da mugun sakalci, bai san yayiwa kanshi wani abu ba sai an mishi. shi yasa ya tashi a sakalce, duk abinda akewa yara masu gata shi ake mishi, kai ko takalmi Mamoon baya saka me cinyayyen kasa. Kai rigar shi ce ta yage ba zai kuma sakawa ba sai wata.Gashi dai iyayen rikon shi talakawa ne futtik, amma bai taso da yanayin talauci ba, sai gata kamar jinin gwamna. Haka ta mike tare da shiga cikin gidan ta dauko langa ta dibo ruwa ta wanke mishi tufaffen shi, wanda duk bayan wata biyu sai an dinka mishi riga da wando, kala biyu koda su basu saka ba shi zai saka. Wani irin kauna suke mishi wanda shima Yaron yasan da haka shi yasa ya taso babu ruwan shi da kowa.
Kai zunzurutun bakin hali inji mutanen gidan dan sukan ce bai gaji halin Aminatu da Malam Sanda ba, ya dauko mugun hali a wani gurin can, ko dakin mutane baya shi, yana bakin kofar shi, gashi da farin jini yara cika suke a dakin su. Idan ya kwanta ya mike kafa yace kar ayi magana babu me tari a dakin. Idan kuwa yace a fita dan Uban Yaro ko kaho ne akan Ubanka sai ka fita wannan yasa Yara dayawa suke tsoron shi. Bai da fada amma iya maganar fatan baki ya isheka bakin cikin wani guda....
<<>>
Tunda aka nuna mishi ajin shi baban shi yayi mishi fada kafin ya ciro kudin tara ya bashi.
"Bana kudin nan yayi yawa" ya faɗa yana juya kuɗin.
"Yaron arziki kenan, bai yi yawa ba. Ka rike shi kaji karka yi faɗa kaji na san ka baka da abokin fada kayi karatu kaji yaron baba."
Cogewa yayi yana kifi kifi da ido.
"Almamoon meke damunka?" Duk ya rud'e.
"Baba kazo ka ɗauke ni, a keken ka" murmushi yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah zan zo da kaina, na dauke ka yayi maka?" Ya tambaye shi gyada kai yayi, sannan ya kuma raka shi bakin aji, yayiwa malamin sallama, sannan ya ce.
"Maza shiga dan Baba." Haka ta shiga bai kalli inda malamin yake ba, ya juya yana kallon Baban shi.
"Baba idan kaje gida kaci abinci kaji"
"Insha Allah dan Baba"
Sake baki suka yi suna kallon ikon Allah, wannan irin soyayyar fa, ko makarantar Firamare da ya gama basu yi wannan dirama ba, gyara jakar shi yayi yana kallon ajin kafin ya hango wani kujera babu kowa. Ya zauna.
"Meye sunanka?" Malam min ya tambaye shi.
"Almamoon Isma'il Wodaadabe" ya faɗa a sanyayye,
"Zauna"
Ya zauna yana kallon allon, duk da makarantar kudi ne, haka bai hana shi fahimtar yadda ake koyarwa ba, kasancewar wanda ya gama ma, na kudin ne. Ana tashi tara ya ya dauki jakar shi ya fita.
Dariya yan ajin suka mishi. Murmushi yayi musu tare da kallon su. Haka ya fita yayi break da aka dawo aji aka cigaba da karatu.
Karshe daya Baban shi ya zo da keken shi ya dauke shi a gaba, a hanyar komawar su gida ne suka bi kasuwa, baban ya saya musu kayan abincin da za ayi na dare. Sannan ya dauke shi suka tafi. Har zasu tafi wani abokin aikin Malam na rana shima buzu ne yace mishi.
"Malam Umaru, idan ka dawo ina son magana da kai" dan haka ya kawo Mamoon gida ya koma, zama yayi kusa da Mutumin yace mishi.
"Malam Nasiru gani"
"Kayi hakuri idanuna idan suka ga abu bakina baya shiru, musamman kai da muke tare da kai." Shiru yayi yana kallon ƙasa kafin yace mishi.
"Idan ka tafi ka bashi wannan zoben ya saka a hannun shi duk da kana boye mishi abu akan shi. Kayi hakuri gaskiya rayuwar shi ce akwai daukaka akwai faduwa, bayan nan ban san meye Allah ya ƙaddara ba, amma gaskiya na tausaya mishi domin wata irin ƙaddara da zata sanya shi bayyana kanshi itace ƙaddarar da zata sanya shi kuka.
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
JE LEEST
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mysterie / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....