BABI NA ARAB'IN DA D'AYA.

997 262 39
                                    

https://www.wattpad.com/1110334727?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=X%2FgaE6gSz58j9QDiZ%2Bv%2F87PO5wzh9ybyc4ylC%2BD2x4kNIYjRRXgnpq5FbUohenIlvbXnn8LMctzK9uaapnzp5Pumy73OiDN5uRmPbdvvha53DDMXTyRQBKT77Pt4B4E6

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARAB'IN DA D'AYA.

Karfe ɗaya da rabi ya dawo dani gida lokacin har  Rukayyah ta gama shiryawa, ina zuwa sallah muka yi, domin ya koma abincin da na tawo dashi na zauna muka ci kafin yazo shi da Dan Ba'are da Malik, ya kasa ce min kome haka nima na kasa magana, kwalla nake kawai.

Haka na shiga motar bayan shi da Dan Ba'are sun shiga nasu, zasu kai Rukayyah tasha, Ni kuma da Malik muka nufi hanyar Damagaram. Bayan sun kai Rukayyah tasha, ya biya kudin motar sannan ya shiga nasu.
"Alhamdulillahi, yarinyar ta tsira saura mu kuma, kai ma zaka iya barin garin nan kafin karfe sha biyu na dare."

  "Abota na da kai gaskiya ce, dan haka babu ina da zani sai abinda Allah yayi mu mutu tare mu tsira tare" "a'a Khalil"
"WALLAHI kuwa Mohan na shirya tsaf"
"Nagode"
"Nima mahaifina ne"
Wayar shi ce tayi kara ya ga bakuwar lamba. Dauka yayi tare da cewa.
"Mohan Mamman Nasir Aghali akan layin"
"Kana magana da."
"Ai kai ne?"
Nan yayi shiru,tare da cewa.
"Gamu nan zuwa"
---
Koda suka isa gidan gonar babu kowa, sai shi. Zama suka yi suna kallon shi ganin yadda ya zuba kiwo kala kala.
"Sannun ku na kiraku, kuma ina wani abu na daban."

       Abinci ya tura musu, kallon shi Mohan yayi sannan yace mishi.
"Bana bukata"
"Da dai kaci dan zai maka amfani Insha Allah." Kallon dan Ba'are yayi sannan yace mishi.
"Kai ma ba zaka ci ba?"
"Daukar filet din yayi tare da kallon shi.
"Idan da zan cutar da kai bazan tab'a kiran ku ba! Kaci namar kazar daji ce, idan kaci kamar yadda take da wuyar kamuwa haka zaka zame musu."

    Aikuwa dan Ba'are ya fara ci yana ci, sosai gashi girkin yayi masifar dad'i.
"Akwai sharadi?" Kallon shi ɗan Ba'are yayi yana niman karin bayani.
"Karka sake kaci duk wani abinda za a sarrafa shi da ganyen karka yarda kayi mu'amala da macen da take cikin jinin haila, bayan nan kuma toh ku ji dadin ku!"
"Ni ban yarda da abinda za a bani domin na yarda da Allah sama da wanin shi" ya mike tare da barin gurin.
"Yau aka shirya gagarumin lamari akan ka, gobe Mahaifinka zai saka hannu akan duk wanda ya ganka ya kashe ka, ka ajiye wannan maganar a ranka, sun yi nisa kana da damar dakatar da jirgin da zai taso da ministocin mahaifinka mu gani, kafin kayi taurin kai dubunka sun yi, kuma sun fadi."

       Juyawa yayi tare da kallon shi.
"Zauna kaci sai na kara maka da basirar mu ta manyan mutane" ya faɗa mishi.
Zama yayi yaci abincin da kazar sosai, yana kallon Alkali. Yana gama ci ya mike.
"Zauna! Kanwarka Khausar, kayi farin dabara da ka nime su tafi hutu ita da Yaranta da dayan Kanwar ka, sauran kuwa suna cikin kariyar Ubangiji.

   Kasan Meye matsalar ka? Baka yarda da kanka ba, sannan ita kanta Yarinyar da kake so baka yarda da ita ba, kayi kuskuren tab'a wannan Yaron, sabida abu biyu yaƙe dawainiya dashi, yana da Sa'a. Kuma yana niman mace mai Sa'a kamar Yarinyar ka, Ansar Yusuf. Ba shine sunan shi ba.
"Hisham Waadi Ansar shine cikakken sunan shi, bai tab'a niman abu ya rasa ba, sai Yarinyar da kake tare da ita, Hisham Ansar Yusuf, dan kasar nan ne, mahaifin shi dan kasar nan ne, amma mutum ne da yake da goyan bayan wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar nan, sun fito takara da Mahaifinka, shi ba a zab'e shi ba aka zabi mahaifin ka. Kasancewar Yasaka buri akan mulkin yasa shi samun shanyewa barin jiki suna garin Diffa da zama.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now