🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN DA SHIDA.
"Kai tsafe kari ke da wanin Allah, Ni kuma Alqur'an na rike da Allah ka yarda wani abu ya same ta, sai duniya sun ji mu. Gabanka da Mamman Nasir Aghali ya tsaya a can muku yarinya ta kuwa kashe ku zanyi daga kai har d'an ka "
Yana gama fadar haka ya juya tare da barin gidan, ina Hisham ya kwaso wannan masifar ai yasan waye Sama'ila Wodaadabe, wannan ai Bala'i ne da kanta, waye ya aike shi niman bala'i. Tabbas duk da yana son zama shugaban ƙasa, ya hakura dan yasan Sama'ila sanin hakika, yasan Waye shi. Ya kuma san dalilin da ya saka shi barin gidan amma bai zata Almamoon Yar shi ce ba, ina zai kai bala'i haka, idan ya kuma zuwa billahi azim sunan shi gawa, ko abinda dan shi yayi mishi bai kai kashedin da Uban Almamoon yayi mishi ba.
***
Niamey.Yadda Hajiya Latifah ta hana kowa sukuni da firgice, yasa aka fara mata addu'o'in.
"Mohan ka dawo da ita wayyo Allah na, zasu kashe ni. Don Allah ya dawo da ita, wayyo Allah na."
"Meye ya faru?"
"Alhaji nasa ya saki matar shi ce saboda Shegiya ce an samar da ita ta aure."B'ata ta daina ganin abinda yake gani tare da kallon su.
"Meye ya faru?"
Gaura mata mari Primer minister yayi sai tayi tambul, kafin ta zauna da kyau..
"Alhaji marina kayi"
Cikin tsuma ya mike tare da watsata waje.
"Kije na yanke igiyar aurena baki daya akanki, Allah ya bi mishi hakkin shi na cutar da d'anki da kika yi"Ya fada tare da juyawa tana ihu tana kome, kifa hannu Mohan ya a fuskar shi, kamar ba sadauki ba yana kuka me ban tausayi.
"Kayi hakuri, baka yi sa'ar uwa ta gari bane." Ya fada tare da shiga dakin shi ya kwanta, kowani dan adam yana da nashi ciwon mai illa ko mara illa, tashi ciwon ya zama tarihi na tsawon shekaru saba'in da wani abu, abinda mutane suka kasa fahimta akan wannan al'amarin shine rashin karban ƙaddara da uzuri. Shi yasa tafiyar Ƙaddara take rugu rugu da zukatar su.
**
Kwana biyu ina kwance, ranar da na farka kallon Innah nayi, sannan na dauke kaina. Shigowar Dr Zainab ya sani ce mata.
"Mommy don Allah ki taimaka min ina son na tsarkake jikina""Toh" haka ta taimaka min ta had'a min ruwan zafi, nayi wanka tare da gasa jikina, sannna na fito ina tafiya a hankali, sake mai dani tayi tana faɗin.
"Zaki lalace muje na guda ki da kyau."Haka ta dawo dani ban dakin ta dubani sannan ta zuba min ruwa me zafi da wasu magunguna ta sani na zauna a cikin shi. Hawaye ke zuba min, har na gama na fito, sannan ta had'a min shayi me kauri ina sha ina kuka, ina idarwa na wanke bakina, na zauna na gabatar da sallar da ake bina sannan na daura da addu'o'in, wanda badan Ta rufe min bakina ba, Allah kadai yasan Irin Bala'in da zan janyo musu.
"Wallahi addu'o'in da nayi ne, Ni na mishi Allah ya juyar da shi kanki, don Allah karki yi addu'a. Ƙaddara ce ta faɗa min amma wallahi na sha zuwa niman ki aka ce sun tafi dake?"
"Wacece ke?"
"Sai kin tambaya ne? Ai balagazar da ta kasa yarda da ƙaddara ce ta tafi bata kalli abinda ta haifa ba, ta bishi da mugayen fata gashi Allah ba azzalimin sarki bar ga kayan ki nan tunda ta bude ido ta san meye soyayya masifa da bala'i da rashin jin dadin rayuwa suka sakota a gaba, an ce miki Allah abokin wasan kine!""Ya isa haka Aminatu!" Abie ya daka mata tsawa.
"Uwata kiyi hakuri, gamu nan iyayen ki dukkan mu biyu, don Allah kiyi hakuri."
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....