*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azi_zat*Gaisuwar ce wannan shafin Aunty Safiya Jos, Ummi Ilham Gombe, Mom Sayeed Kano, Mrs Faruq matar kakana Nagode sosai*
Sai da rai....
BABI NA SHA BIYU.
Da'go kai yayi tare da kallon su, cikin nutsuwa da yanayin shi na cin Uban kowa ya kwana lafiya, yace musu.
"Matukar wanda zai kula da ya iya kome dukkan ku barin gidan nan zaku yi domin ban yarda da fuskar ku ba. Ku b'ace min da gani marasa mutunci"Rabil da Hurayyah suka wuce kitchen, Bilal da Moussa suka wuce gurin wanki, Sarah da Nouhu suka wuce bayan dakin da ake ajuye kayan aikin cikin gidan.
Hurayyah da Rabil girki suke, Bilal da Moussa, wankin da guga suke. Sarah da Nouhu sharan gidan suke da goge goge. Kusan idan ya cire Hurayyah itace Mohan ya kawo ta da kanshi sauran kuwa. Daga can fadar gwamnati aka kawo su. Kuma yana kyautatta zaton Hajiya Safiya ce. Ya tsani matar nan kamar me.
***
Niamey.Shige take da fice, tana hango yadda Hajiya Latifah ta harde ana mika mata wasu takardu, zata saka hannu. Murmushi tayi sannan tace.
"Da Sannun zan ruguza ki, tunda nai babban nasara kawar da wanda ya tsaya muku"Fitowa tayi cikin shigar Alfarmar ta nufi gurin da Hajiya Latifah take.
"Barka da hutawa ranki shi dade"
Sai da ta b'ata lokaci kamar ba zata amsa ba kafin tace mata.
"Hmm"
Ta cigaba da aikin ta, kamar bata san da tsayuwarta a gurin ba.
"Hmm, dama ranki shi dade akan batun matsalar Mohan"Ta faɗa tana kallon yanayin da Hajiya Latifah ta shiga, ganin yadda Jikinta yake rawa yasata sake murmushin mugunta, sannan ta cigaba da cewa.
"Dama naga"
"Kije bana son jin sunan shi tashi ki bar min nan"
Ta daka mata wani irin tsawa, wanda yasata mikewar dole, domin babu karya ta razana. Bayan tabar gurin kan Hajiya Latifah ya shiga sara mata kamar zai rabe biyu.Tsaki tayi tare da mik'ewa, ta nufi cikin gidan, koda ta shiga har ta manta kome akan shi. Itama Hajiya Safiyar dadi ya sata bata kuma bin wani abu akan Mohan din, sai dai tana da kudirin jibi Insha Allah zata dira a Maradi ta cirewa dan Ba'are rashin mutuncin da yake kan shi.
Kuma wallahi ta isa sai ta ganawa Mohan azaba, dan duk cikin Yaran Hajiya Latifah ta tsani Mohan sama da kowannen su,, shi yasa bata yi kasa a gwiwar gurin tsayawa sai da kome ya faru dashi kafin hankalinta ya kwanta. Shima dan Ba'are sabida ba haka kawai yake ba da ta jijjiga shi da karfin ta. Ta kuma nuna mishi Allah daya ne.
***
Washi gari
Kamar ba zan shirya ba, amma sabida irin yadda Malam Ansar yake bina da idanun yasa ni hada kayana, na raba biyu. Na saka rabi a cikin wata jaka, rabi kuma na barshi a dakin Baba Mari, sanan na tsaya tare da cewa.
"Baba idan aikin da sauki zan na zuwa duba ki, Insha Allah."
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....