https://www.wattpad.com/1111755716?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ARAB'IN DA BIYAR.
Kai Mishi duka Mohan yayi, Dan Ba'are ya rike shi. Ya kuwa fashe da dariya tare da kare kan shi kamar me tsoron duka, cikin fusata ya ce Mishi.
"Dake ni! Idan ka cika dan halal idan kai namiji ne ka tsaya muyi damben niman aurenta! Ka tsaya da kafarka bawai ka koma gefe kana ihu zaka dake ba, lusarin banza dan daudu kawai, mara lafiyar gaba.""Ban ce Karku kuma min fada ba?" Na fito waje sakamakon hayaniyar su da nake ji, ganin yadda dukkan su, suka samu rauni. Kallon su nayi kafin nace musu.
"Ina cewa kashe ni kuke son yi? Ina ce rayuwata tace kuke bukata?"
"A'a Munnah babu haka, zan tafi zan tafi yanzun nan." Inji Ansar, ya shiga motar shi,.tare da d'aga min hannu. Kallon Mohan nayi yana kallona, juyawa nayi zan koma cikin gida yace min.
"Baki gaya min meye nayi miki ba, wallahi bani da nutsuwa ki gaya min meye na miki idan yaso idan rabuwar ce zan rabu dake wallahil billahi Azim,"Takowa nayi gaban shi, ina kallon shi.
"Sabida kai, na rasa kome nawa. Sabida kaina ƙaddara ta fada, sabida kai yau nake kuka. Kasan me? Saboda nasan da kanka zaka juya min baya, zaka kore ni a rayuwarka, me yasa zan damu da kaina a kanka? Me yasa ba zan rabu da kai ba? Don Allah ka tafi ka barni ina son sauran farin cikin da ya rage min na hada na rufawa kaina asiri."Sannan na juya zan tafi, riko hannuna yayi, ya saka a kirjin shi.
"Ji yadda yake bugawa! Ko kallon ki nake bugawar shi na daban ne, balle kuma idan ina jin saukar kalaman ki, ba zaki kashe ni ba. Ba zaki lalata min rayuwa ba, Moonah idan laifi naki ki gaya min wallahi zan baki hakuri kamar haka."Ya zuba gwiwar shi dukka biyu a kasa.
"Haba Maimunari! Idan yayi laifi ki gaya mishi ke ba abin kunya bane mutum kamar Mohan yana zuba gwiwar shi a gaban ki, meye yayi miki da zafi haka? Idan baki kaunar shi.""Khalil Ibrahim, kyale ta rokonta nake." Ya fada bayan ya mike, kukan da nake yaci karfina. Kwace hannuna nayi cikin tsiwa da masifar yadda zan rabu dashi na kama fada.
"Toh dole ne! An tab'a soyayya Dol..." Bakin shi na ji akan goshina. Bayan ya rungume ni.
"Ba'a tab'a soyayya Dole ba, kuma akanki ba za ayi ba, Nagode sosai idan na mutu karki min kuka don Allah, kiyi min addu'a."Daga haka ya bude motar su ya shiga, tare da rufewa bai kuma kallon inda nake ba, bai kuma d'aga kai ya kalle ni ba, asalima kamar bana gurin haka sukayi tafiyar su. Durkusawa nayi a gurin ina kuka tare da shasheka, d'aga ni Innah tayi tana faɗin.
"Indai laifin shi bai girmama har haka ba baki yi hakuri mana ya a sonki yana kaunarki""So da kaunar ba zai min rana ba, zai iya gudu na." Kallona tayi tare da rike hannuna.
"Me aka miki Maimunari na?" Ta tambaye ni tana min wani irin kallon tsoro, bakina yana rawa na rufe tare da rike hannun ta daya.
"Innah!!" Jan hannuna tayi har cikin d'akinta, ta kuma zaunar dani, tare da durkusawa a gabana,ita kuka ni kuka. An rasa me magana a cikin mu. Sai gyada kai yake tana kara kallona hawaye na zuba a idanun ta.
"Meye ya faru dake?"
"Fy..de.." na fada a tsora ce. Domin nasanta da zafin rai, wani irin riko tayi min tana kuka ina kuka.
"Waye ne haka yayi miki wannan wulakancin? Waye ne ya tozartaki? Waye ne ya cutar dake haka? Me kika musu da zafi? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,Ya Allah ka tsayar mana haka. Ya Allah ka rufa mana asiri haka."Da sauri ta ja kasan gadon ta, ta shiga niman wasu tarkace, fita tayi domin Baba yana ban daki bata zauna ba, can bayan minti arba'in sai gata, daura tunkuya tayi bayan ta wanke saiwowin da tazo dasu, ta saka a tukunyar ta haɗa mishi wuta. Ya cigaba da nuna. Ni kuma ta shigo d'akin. Tace min.
"Bude naga gurin domin nasan ai baki da lafiya."
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
ESTÁS LEYENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Misterio / Suspensolove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....