BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.

1K 278 45
                                    

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.

Juyawa yayi tare da yafito ni,da dan sassarfa na isa bayan su, suna tafiya ina take musu baya har cikin gidan, ba dan na je Dubai nayi kallon duniya ba, ba mamaki sai an daure ni, har falon Primer Ministan na shiga inda ya zauna tare da jan dan shi a jikin shi kamar zai mai dashi cikin shi.

     A hankali na zauna a kasa, kallona Primer ministan yayi tare da cewa.
"Ga key din inda zaka zauna sabida na saka an ware maka maka shashin."

  "Abbu dalibi ne kuma ina son dawo dashi nan da karatu sabida zan fi sanin meke yi."  Da sauri na kalli bakin Hammah Mohan da yayi magana kamar bashi ba, domin yana gaban Abban shi kamar wanda yake daukar karatu wani irin nutsuwa yayi kamar ba shi ba.

"Ka tuntubi iyayen shi? Ko ka tuntubi yaron? Kar karfin ikon da Allah ya bamu yasa kayi tunanin kome mana," a hankali ya juya mishi buzanci.

    Kallon Almamoon yayi da ya nutsu kamar baya gurin yace mishi.
"Tashi kaje gurin Harisu zai nuna maka inda apartment dina yake ka gyara kome kafin na iso."

    "Toh" na ce tare da mikewa, na bar falon.
"Yaron nada cikar kamala, yana da nutsu. Amma bai da kwaɗayi?" Primer minister ya tambayi Mohan, gyara zama yayi sannan ya gaya mishi kome akan Yaron, amma bai gaya mishi akan jinsin shi ba, murmushi yayi irin na manyan mutane.
"Amma kai me ka gani akan Yaron ni dai a tunanina ka mai dashi makarantar shi, sannan ya koma hannun dangin shi, tunda jinya yazo maka."

        Duk da sanyin Ac bai hana shi jin wani mugun zafi ba, kurawa Abbu idanu yayi sannan yayi kasa da kanshi.
"A'a dama zan cigaba da aiki na a maradin kawai, domin yadda kake ganin yaron ba wani wayo ne dashi ba, kuma akwai wani da yake takura mishi, hmm hmm kuma kuma kawai hannun kawai nake bukata."

         Kallon mamaki yake mishi domin idan ya fahimta Mohan ba zai iya rabuwa da yaron ba. Sake kishingide yayi yana kallon shi kafin nan yace mishi.
"Toh ba laifi amma ba zaka zauna da namiji a gida babu mace ba, tunda ka sami lafiya idan Latifah tazo zamu san abinyi kafin ka koma Maradin."

Da mugun sauri ya d'ago kai, ganin fuskar abbu babu wasa yasa shi cewa.
"Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada kamar zai yi kuka.
"Zaka iya tafiya kayi wanka idan yaso sai ka turo shi ya amsa maka abincin ka."

    A hankali ya kara nutsuwa yana faɗin.
"Nagode Abbu" ya mike a hankali, ya fita, yana sauke ajiyar zuciya. Bai san lokacin da ya gwammace da ya zauna yayi ta gadin Mamoon har ya gama karatun shi.

     Ina gama gyara ko ina yana shigowa, jallabiyar ce a jikina me hula. A hankali ya tako har inda nake tsaye, ya zaunar dani. Sannan ya durkusa a gabana.
"Wata satin zamu koma Maradi, sama an karb'a maka excuse, toh yanzun zamu koma kuma sunyi korafin kayi wasa da wancan zango, dan haka na mai da hankali sosai ganin na dawo da kai Niamey amma Abbu yaki dan haka idan na gama hutawa zamu koma tare"

    "Amma nace ba? Kai ɗaya ne ki kana da wasu yan uwan? Naga kai kawai abbu ya damu dashi sai boye ka yake kamar wani abun da za a sace mishi" na fada ina mishi gatsine, tsaki yayi tare da mik'ewa yana faɗin.
"Ina da kane maza uku mata uku mu bakwai ne, amma nine babba."
"Auw shi yasa ka zama tikeke ashe haka abin yake? Toh Gskiya idan nine kai ba zan yarda a haife ni a farko ba sabida kar na zama tikeke irinka" na fada ina kallon shi. Girgiza kai yayi yana faɗin.
"Kai kan wallahi baka da lafiya kana bukatar likitan ƙwaƙwalwa ko zaka samu lafiya."  Kallon shi nayi kafin nace mishi.
"Babu kyau dai cin mutuncin mutane. Idan bai gaya maka gaskiya ba waye zai gaya maka sai kayi kuma"  wucewa yayi tare da barina ina ta mita yace min mara lafiya.
"Ina wayar ka?" Dai dai zai shiga wani daki.
"Oh toh gashi nan dai ban san ya zanyi dashi ba kuma na kasa kunna shi"  juyowa yayi ya zuba min ido.
"Wallahi idan ka b'ata wayar nan sai na cire a kudin aikinka"

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon