BABI NA SITTTIN DA TARA.

1K 219 36
                                    

HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SITTTIN DA TARA.

"Kina Fahimta! Ansar ba kaunar ki yake ba, mutumin yake kaunarki ba zai tab'a lalata miki rayuwa da farincikin ba. Bawai ina gaya miki haka a matsayin Aminin Mohan bane, a'a ina gaya miki haka ne a matsayina na dan uwanki, kuma abokin shawaran mijinki..

     Wallahi bai aiko ni domin na gaya miki, amma ita wannan ta sani, komi kashin damuwa idan ya gani a tare dake kamar zai zauce haka yake ji, ki duba takardan sakin da ya baki,wallahi bai tab'a kawowa zai sake ki ba."

Da sauri na shiga watsi da kayan na fito da takardan a kasar a kwatina.
Hannuna yana rawa, jikina sai bari yake na warware takardan.
*Ina son mata ta! Ba zan tab'a sake ta ba har abada*

Wani irin kuka na sake tare da kallon wayata da take kara, da sauri na dauka.
"Kece Mrs Mohan?"
"Eh nice!" Na fada ina toshe bakina.
"Toh ki kula domin shi bamu same shi ba, amma ana bibiyar rayuwar shi da ke, an saka a kashe shi. Dan haka duk inda yake kice mishi ya kula da rayuwar shi"

  Sake wayar nayi tare da jan mayafina na rufe kaina, sannan na fita ban iya kula su ba, duk tambayar da suke min. Bani da hankalin da zan basu labarin abinda yake faruwa.

Dan haka ina fita na hango shi yana tsayawa a bakin kofar shiga gidan mu, da sauri na isa inda zai bude kofar, ba bude tare da cewa.
"Basu maka kome ba? Fito kaji." Bai fahimci me nake nufi ba yana fitowa kuwa suka fara harbi,kwantar dani yayi tare da janyo wata jaka, ya ciro bindigar shi, ya shiga bin su yana harbin su. Sun samu sun gudu dan haka ya fito  tare da d'ago ni, hango wani mutum nayi. Yana tasowa ta bayan Mohan, a hankali na juya tare da Mai dashi daidai kofar gidan, sai ji nayi kaifin abu ya huda bayana har ya fito ta cikina.
"Hammah Mohan! Na gaya maka rayuwata fansa ce koda ni ba zan more ta ba? Na tab'a gaya maka ina raye ne domin kai? Hammah na, tun kana cikin laluran hauka nake tare da kai, wallahi billahi azim ina sonka da dukka rayuwata..." Na tafi zan fad'i yayi maza ya tare ni, shi kanshi mutumin da fuskar shi take rufe wani irin ihu ya kwala tare da cire abun fuskar shi.
"Hisham!" Na kira sunan shi. Ina jikin Hamma Mohan. Sai gyara mata kwanciya yayi a kirjin shi kamar baya gurin.

"Na gaya maka cewa, ni Mohan nake so!" Na fada a sanyayye.
"Ni shi nake so! Ina son shi baki daya da rayuwata, ko babu kome an kawo karshen rikicin ko? Ni matar Mohan ce, Ina son mijina sosai." Na fada ina share kwalla da ta zubo min.  Daidai zuwan motar yan sanda.
"Hammah na, karka mishi kome kabar shi da ciwon da ya jiwa ranshi ya ishe shi har karshen rayuwar shi."

  "Mohan a kaita asibiti mana"
"Ko an kaini bai zama dole nayi nisan kwana ba"
"Karki damu zaki rayu Wallhi" ya fada da mugun karfi ya nufin inda aka saka motar asibiti yana rungume dani.

Bayan tafiyar su, da kanshi yayiwa Yan sanda bayanin shi ya turo ayi kisan, dan haka suka makala mishi ankwa, suka nufi dashi Ofishin su.

     Hankalin Mommy yayi mugun tashi, dan haka suka nufi Asibitin  tunda suka iso suka sami Mohan, ya kasa tsaye  ya kasa zaune, sintiri yaƙe, ya shiga Nan ya fita nan hankalin shi a mugun tashe.

  Allah Sarki baby Widad tana kwance a jikin Abie hannun ta daya a bakinta tana ajiyar zuciya.
Bayan awa biyar likitocin suka fito. Tare da nufar inda Mohan yake.
"Mun yi kokarin mata aiki, amma gaskiya bamu san yadda zamu gaya maka ba, Matarka koda ta rayu bai zama dole ta mori kafaffunta ba, sabida wukar ta tsinka mata jijjiyar lakanta (spinal Code) abin da muka Fahimta a jikin wukar guba a jikin shi, shi kuma ya tab'a mata ƙwaƙwalwar ta, wanda ya tsayar da aikin zuciyarta. Gaskiya muna baku hakuri domin bai zama dole ta rayu ba."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant