🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ASHIRIN DA D'AYA.
Cikin ihu da masifa yake bin bayan Mohan tare da niman riko rigar shi, amma zaratan sojojin da suke bin bayan MG Mohan suka cafke shi, tare da shiru suna jiran Umarnin shi.
"Ku kyale shi ya rayu. Na barshi ya rayu domin idan kuka dake shi sai ya leka lahira ya dawo." Ya fada tare da cigaba da tafiyar shi,
Ganin Almamoon baya motsi ya sashi karawa da sassarfa, yana kallon fuskar shi, hular kanshi ne ya zame, lallausar gashin sa da yake tufke baki wuluk wanda yake warware. Kallon shi yake yana kara mamakin yadda namiji dashi yake da uban gashi haka.
Yana fitowa ya ajiye shi a cikin motar su, kallon Fahad yayi tare da kallon bike din shi, sara mishi yayi sannan ya koma, gurin bike din ya ja machine din da gudu, yayi da suma suka rufa mishi baya. Tab'a bluetooth din shi yayi tare da cewa.
"Malam turo min wani likita daga barikin sojan maradi."Tab'e abin yayi tare da sauke wani irin ajiyar zuciya.
"Yallabai an tura masu wani motar da zata kwaso su.""Hmm" ya faɗa, yana me kallon zoben hannun Almamoon, a hankali yake me jin kamar ya rufe Ansar ku baki daya, amma bai san girman da yake dashi a duniyar Almamoon ba, sai ya farka.
Suna isa gidan ya sauke shi cak, har yana mamaki.
*Dube bakin shi da ya iya zungure min goshi, nan kuwa tsiwa ce zallah babu wani karfi dube shi kamar ba namiji ba*Ya fada a kasan ranshi, yana jin wani dariya yana niman kwace mishi, yanzun ma idan ya farka zai koma kamar da yadda zai cigaba da rena mishi hankali, dan yana son haukar yaron baki daya ya kam manta da batun shi din wani ne yayi ta shirme.
Shigowar wani likita tare da wasu mata biyu, suka fara aikin su a kan Almamoon, tashi yayi ya bar musu gurin. Can suka ci-gaba da aikin su, sai kallon juna suke musamman bayan da likitan ya gama nashi suka fara nasu. Abun mamaki ya basu. Me yasa haka?
Dan gulma sai da suka yi ta duba shi har cikin, tsoro ne ya kama su lokacin da Mohan yayi gyaran murya, da sauri suka bar shi. Juyawa suka yi. Likitan ya fara magana.
"Yallabai mun debi jikin shi, zamu bincika muga abinda yake cikin shi. Nan da awa daya.""Amma Likita mara lafiyan yana"
"Na Fahimta muje Insha Allah zamu kara dawowa, sannan na sami sauran birbidin maganin da aka shaka mishi zamu yi bincike akai."Suna barin gidan likitan ya balbale su da faɗa, yana gaya musu.
"Dan baku da hankali taya kuna gaban MG na soja zaku saka bakin ku a cikin maganar mu kusan waye shi?"Shiru suka yi dan sun san halin shi masifaffen ne, har suka isa asibitin, cikin abinda bai fi awa daya ba aka gama binciken. Yana karanta abinda ya kusan da sauri ya kira Dan Ba'are ya gaya mishi.
"Don Allah ku tawo da majiyancin nan rayuwar shi tana cikin hatsari"Zunzurutun tashin hankalin da dan Ba'are ya shiga kamar zai dira a maradi, dan haka ya kira Mohan a hanzarce.
"Yaron nan yana cikin hatsari a kai shi asibiti gani nan zuwa."Kashe wayar Mohan yayi mishi.
"Hello Hello! Kai kai katsaya mana" babu shiri ya dauki kayan shi bai tsaya wata wata ba. Ya kira wata wayar da take cikin Office din shi, ya faɗa musu abin da yake bukata, cikin kankanin lokaci suka hada mishi kome, yana fita ya daga Office gidan shi ya nufa, ya haɗa abinda zai hada,
VOUS LISEZ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystère / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....