BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.

1K 262 54
                                    

https://www.wattpad.com/1105333540?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wFWlz0rB5vLnDHBBsgwmy16HrEu27aKV%2BLrvZEc4HZOQhPxrhzXfAzebs68cEFXa4%2BKxqKR8E%2F8iKJMh4QpPwlUHdawDA%2FOu0EVnwQVQ5hDmkOaB8%2Bq4IYKg9xcPDk7D

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.

Kifa kaina nayi a kafadar shi ina kuka Sosai, kafar yana hannun shi. Kasa aikata kome yayi ya d'ago kaina.
"Kai ba irin sauran yara bane, kome kashin kuskure ya faru da kai babban tashin hankali ne, rayuwarka abar dubawa ce, ina bukatar ganin ka zama wani abu, dan haka duk dan iskan da ya kusanci inda kake sai na kashe shi." Ya kuma murɗa kafar sai da yayi kara nima na sauke ajiyar zuciya tare da kifa kai na a kafadar shi, dif na dauke wuta.

       A hankali ya d'ago kai na yana kallon yadda kwalla yake sauka ta gefen idanuna,  mik'ewa yayi ya kwantar da ni, sannan ya koma hada sauran maganin ya shafa min, tare da gyara min kwanciya na, a kujeran ya shiga dakin ya dauko duvet ya lullube ni sannan ya rage hasken dakin ya zauna tare da mai da hankalinsa kan aikin da yake yana waya da Dan ba'arensa wanda kusan rabin wayar bakar magana sukewa juna.
"Ina Mamoon?"
Juyawa yayi ya kalli yadda yayi wani lufff a cikin duvet, sai sauke ajiyar zuciya yaƙe.

    "Yana barci"
"Ok amma kana kula dashi kuwa? Kuma idan ya tashi ka bashi wayar mu gaisa mana" 
Datse wayar yayi tare da kashewa baki daya, yana jan tsaki,

        Kasa aikin da yake yi, yayi ya cigaba da kallon Laptop din shi, yana ma rasa me zai yi, mik'ewa yayi tare da mika, sannan ya koma saman kujeran da yake fuskar Mamoon ya kwanta.
..
Mafarkin mutumin nan nake, da ya kamani d'azun sai kuka nake ina kiran "Hammah na zo tafi dani" na fada ina kuka, dake barcin shi bayi nauyi ba, bude idanun shi yayi tare da tashi yana kallon shi, a hankali ya mike tare da zuwa gaban shi ya zauna a ƙasa, a hankali bakin shi yake karato ayatul kursiyu, yana tofa mishi a fuska, tare da shafa gashin kanshi, har yaji ya fara ajiyar zuciya.

          A hankali ya mike bayan ya koma barcin, rike hannun shi yayi tare da gyara kwanciyar shi, ya cusa hannun kasan kanshi. Tsayawa yayi yana kallon yadda yake marairaice fuska yake. Saukar numfashin sa yake ji tare da jin wani irin yanayi yana kara tab'a gangan jikin shi.  Da sauri ya zame hannun shi yana kallon shi.
   Kasa komawa kwanciya yayi ya nufi ban daki ya sakarwa kanshi ruwa, yana me dafa bangon ban ɗakin.
*Anya Yaron nan namiji ne? Anya mata maza ne? Mata maza ne mana baka ga akwai gashin baki ba? Mtseew!*  Yaja tsaki tare da kallon hannun shi, a hankali ruwan yake ratsa shi har ya samu nutsuwa sannan ya fito daure da towel, ya kwanta a gadon tare da rub da ciki, sabida yadda yake jin babu dad'i.

   A yanzun ya kai matakin da ya dace ya ajiye matar auren shi da iyalinsa tunda shi ba yaro bane, tunda ya haura talatin da bakwai, ya wuce a kira shi da saurayi sai dai tuzuru. Toh wacece zata dace dashi? Wacce mace ce zata iya jure bakin halin shi ba Sannun ba Nagode.

      Dakyar barci yayi gaba dashi.
***
Washi gari.

A hankali na mike tare da nufar ban daki nayi wanka da alola na fito na shirya, ina gamawa  yana buga kofar dakin. Fitowa nayi tare da kallon shi.
"Ina kwana Hammah"  share ni yayi tare da juya min baya na nufi falon. Rufe kofar nayi tare da gabatar da sallah, sannan na fito.
"Ka shirya?" Gyada mishi kai nayi, sannan kuma mai da hankali kamar bai da abin fada kafin yace min.
"Ga abinci" wuce shi nayi na zauna na fara cin abincin bayan ya kalli kafar. Ban tab'a kawo zai jifo min tambayar da ta sani kusan kwarewa ba, sai da na furza da shayin bakina.
"Kana son Cigaba da zama da jinsi biyu ne ko kana son tsayuwa akan jinsi daya?"
    Had'iye yawu nayi ina goge bakina. Ganin naki bashi amsa ya sashi mik'ewa, tare da nufar dakin shi ya fito da kayan shi. Yana kallon agogo kou bai gaya min ba nasan ya shirya.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant