https://www.wattpad.com/1112772393?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN.
Jan wani irin numfashi nayi tare da niman zuɓewa kasa, ya riko hannuna.
"Ke tashi matsoraciya kawai." Kiran wasu lauyoyi mata yayi tare da gaya musu maza su kai ni asibiti, idan kuma zasu iya taimaka min ba sai mun je asibitin ba.Amsawa suka yi da toh suka kaini Office din su, suka taimaka min na farka, sannan suka shiga bani ruwa, kasa sha nayi domin na gama razana, shiru nayi tare da jingina kaina da bango. Har ya fito, hankalin shi yana kaina, yana zuwa ya ce min.
"Tashi muje"Haka ya saka ni gaba muka nufi gidan shi, cire kayan shi yayi tare da saka wasu kayan, ya shiga min rubutu a jikin allon karfe, ya nutsu yana rubutun da tawwadar mai zafi,sabida tana tafasa ce ake rubutun dashi, yana gamawa ya wanke min da ruwan zamzam mai zafi dan har yana tiriri. Ya mika min fuskar shi babu alamar wasa yace min.
"Nasan kina addu'o'in neman tsari, amma sha wannan makiyan shi sun rub'anyan da! Ta ko ina aika zakina samu, dan haka nake kyautata zaton an fara bibiyar ki, maza sha ba mutum ba ko ifiritu yake, zai ganki ya barki sai dai a kare a makirci da munafunci ba boka ba ko malami ne, idan ya nace zai tab'a miki wallahi kwayar idanun shi tsiyayyewa zasu yi.Idan kuma aka dage na miki sharri hauka mutum zai yi domin da bakin shi zai magana."
Sai da ya gama min bayani, sannan ya bani wani Magani nasha, kafin na kwanta a dogon kujeran falon shi, bai tashe ni ba. Sai da aka yi azahar na tashi nayi sallah sannan ya mika min abinci.
Awaran madara soyayya sai yaji da dafaffen nama wacce aka dafa ta da madara, har karasa yadda daɗin shi yake, sai shinkafar da aka dafa da ruwan kwakwa. Ina gama ci. Ya kalle ni.
"Duba wayarki mutumin ki ya shiga kotu sau uku yana niman ki"
A kunya ce na dauki wayar na kunna, sakonni shi kawai suke shigowa, kiran shi nayi.
"Kina ina?"
"Ina gidan Abie kazo ka ɗauke ni""Toh gani nan"
"Kina son Mohan kamar yadda yake sonki" sunkuyar da kai nayi, ina wasa da cokalin hannuna... hira muka sama sama har ya iso, harara ta yayi sannan yace min.
"Kin kyauta min!"
"Zauna kaci abinci"
"Toh Abien Moonah" ya faɗa a zolaye, murmushi nayi na zuba mishi. A hankali yake ci yana kallona.
"Muna nake kika yi girkin nan ba? Domin nasan baki iya girki ba""Subhanallahi! Maimunari, dama baki iya girki ba?"
Taka Mohan nayi tare da hararan shi.
"Wash ta taka min kafa, Abien Moonah kaga zata cire min yatsu."
"Gulmar ka ya ja maka" ya faɗa mishi haka.
Wayar shi ya dauka bayan ya danna wata lamba yace.
"Akwai yarinyata zata fara zuwa daukar darasi Insha Allah Asabar da lahadi. Sauran ranakun idan ta taso aiki.zata zo""Abie har da Auta"
"Toh su biyu ne"
Hararan Mohan nake kamar idanuna zasu fadi kasa, mutum ya zama gulmammame,Haka muka sha hira sannan muka mishi sallama, bayan mun kuma hanya yake ce min.
"Yau naji kamar nayi hauka da aka ce min kin suma, ina meeting na fito muje na ajiye ki a gida sai na koma domin ni suke jira.""Toh Sarkin gulma"
"Eh na yarda"
Haka ya ajiye ni a gidan, na samu auta ta gama abincin, cikin tsokana nace mata.
"Kwashe kayan shirmen ki nan ba ci zanyi ba, naci me dad'i a gidan Abie na"
"Wallahi baki isa ba har dare shi zaki ci"
ŞİMDİ OKUDUĞUN
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Gizem / Gerilimlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....