Ra'ayi....

1.1K 188 12
                                    

🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE...

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza

BABI NA SHA HUƊU.

Kura mishi ido nayi ina mamakin zafaffawar shi a gare ni, ai ko babu kome ban cancanci ya jagorancin zuciyar shi a kaina ba,  amma baki daya ya kasa fahimtar kome akai na.

       "Wai tsaya ni d'anka ne da zaka na sani abinda ban yi niyya ba? Ko kuma ajiyata aka baka ban sani ba? Inda kuma babu kome a tsakanin haka toh ka tsaya a malamina, bana son"
   Shanye da toka na harare shi,.domin ya fara wuce gona da iri.
"Meye kake nufi? Wato ban isa nayi magana akan ka ba? Dan ka shigo inda baka saba gani ba? Kwaɗayi y kawo ka mata maza? Ai kowa yasan kai mata maza ne"

   "Idan rai ya b'aci bai dace hankali ya b'ata ba, Almamoon tashi ka bar gurin" inji Malik,
Juyawa yayi ya kalle,

   Mikewa nayi ina kallon Malam Ansar, idanuna cike da kwalla. Sannan na wuce ban ce mishi cikanka ba, har zan haura step yace min.
"Almamoon karka manta waye kai?"
"Na sani! Na sani!! Ni din ruwa biyu ne shi kenan? Na san waye ni ba sai ka gayawa duniya waye ni ba, nasan matsayina da Matsala ta, don Allah ka daina cutar dani akan matsalar da kasan ba ni na halicci kaina da shi ba."

Tura Ni Malik yayi na wafce kafadana, tare da kallon Malam Ansar Idanuna yana cika da kwalla, kamar wanda aka rike min baki.

     "Nagode sosai" na fada tare da barin gurin ina me jin wani irin kuka, amma haka na hadiye, ina shiga dakin da Hamma Mohan yake na nime b'acin rai din na rasa, yana tsaye a jikin window. Ya zuba hannun shi dukka biyu cikin aljuhun wando shi, yana kallon movement na tsuntsaye, sanye yake da riga da wando masu bala'in kyau grey color, sai hadaddiyar gashin kanshi da ya sauka a dokin wuyar shi,he look gorgeous, gashi yayi wata irin tsayuwar da ba zaka tab'a dauka bayi  da lafiya ba. Motsin da yaji ne ya sashi juyawa, kafin ya koma kan abinda yaƙe.

            Daukar ruwan addu'o'in da yake sha nayi na mika mishi.
Sau daya ya kalle ni sannan ya kuma dauke kanshi yana kallon yadda tsuntsaye suke shawagi.
"Karb'a Hamma Mohan"

Dake babu lafiyan bai ko motsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa har zuwa lokacin da na isa gabansa, sai na ganni kamar irin a saka dan tsako a gaban giwa, duk sai na kasa tabuka kome, ina me mika mishi magani, ina kuma fatan ya sha, amsar maganin yayi sannan ya kalle ni, irin kallon nan na marasa lafiya.

           Kai hannuna nayi tare da tura mishi maganin bakin shi, gumtsa yayi sannan ya furza min a fuskana, sannan ya kwashe da kakkarfa dariya, yana kallona. Kamar na fashe da kuka, haka nake kallon shi.

       "Zaka gani ba zan kuma wasa da kai ba" na fada mishi ina jin kwalla na taruwa a idanuna,
Hankad'a ni yayi na fadi can sai da bayana ya amsa,kallonshi nake kamar zanyi kuka. Wato shi ko a jikin shi sai dariya yaƙe kamar zai shiɗe, haka na bar mishi gurin na fita na koma dakina, sauya kayana nayi tare da kallon kayan da ya zuba min maganin. Duk abinda zai min bai tab'a min ciwo ba, duk abinda zai min baya min zafi, asalima Uzuri na zab'i na mishi a rayuwar shi, domin kuwa ai bai da lafiya. Murmushi nayi tare da kallon kofar.

    --- A fusace ya bar gidan, zuciyar shi tana zafi, a bakin kofar fita Malik yayi mishi magana.
"Tsaya malam" cak ya tsaya,
"Meye matsalar ka da Yaron nan ne?"
"Tambaya kake nima sani?" Cikin isa da sanin waye shi yace mishi.
"Gidan nan cike yake da sojoji, tabbas akwai matsala idan ka kuskura kayi wani shirme mara fa'ida, tambaya na da kai na karshe meye matsalar ka da yaron ?"

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt