🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA SITTTIN.
"Amma" rufe min baƙi tayi, bayan ta kashe karatun.
"Me yasa baki da Fahimta? Ki godewa Allah Kinji, abinda ya jarabce ki a kai kuma ki kara mishi godiya yana sane dake, karki yarda son zuciya ya saki, fadawa fushin Allah."Gyada mata kai nayi ina wasa da rigar jikina,sabida ina jin motsin abin cikina,
"Kina fushi da Abie har yanzun ne?" D'ago kai tayi tana kallona,
"Amma ai kina sonshi, tunda gashi har kina zaune a karkashin inuwar shi, kawai kuma shirya kanku ko kuma wannan abin ya shirya ku"Mikewa tayi sakamakon shigowar shi, tana faɗin.
"Allah ya shirya ki"
"Amin Ya Allah" ya faɗa bayan ya zauna yana kallona, cikin murmushin jin dadi yace min.
"Ga Budurwan da nayi sunan ta, Grace" kallon Mommy nayi wacce ta tsuke fuska,
"Don Allah? Na ganta Abie amma ai babba ce ko" na tambaye shi ina leka wayar hannun shi.
"Eh talatin da biyu fa"
"La ba wata babba bace, toh gaskiya zamu je mu ganta."
"Haba Kinga kuwa baturiya ce, sai a haifa miki kane farare"
Cikin zolaya nace mata.
"Mommy kece babbar kawar Ango, tunda nasan bai da abokai sai ke""Karki kuma saka ni cikin shirmenku" ta wuce fuuuu, aikuwa muka saka dariya, sannan nace mishi.
"Abie me yasa ba zaka gaya mata kana Sonta ba?""Ina jin tsoron ta ne"
Kallon shi nayi kafin nace mishi,
"Babu wani tsoro kawai ka gaya mata gaskiya, itama tana sonka fa"
"Da tsufana"
"Itama ta tsufa ai"
"Toh Allah ya sa mu dace"
***
Agadaz.Kallonsu tayi sannan tace mata,
"Kinsan girman baki uwa? Kinsan yadda Allah yake amsa bakin uwa? Da nace duk wanda ya shiga tsakanin Alhaji da Matar shi ban yafe ba shine kika kashe mishi aure yanzun kin dibo jiki akan Nuratu zata bar D'anta ya auri Kanwar Maimunari""Nahnah yarinyar da Shegiya ce? Sannan taya ma zan so ya had'a zuri'a da mayu, tunda ya sake ta yaron nan bai kuma samun sukuni ba, dan haka nake zargin kama mishi kurwa tayi"
Kallon tayi na wani lokaci, kafin yace mata.
"Idan har akan Shegiya ce toh ai kuwa Allah ne ya nufa zan haife ku a silar aure, har na auri buzu. Amma duk wanda yake cikin Zuri'ar mu yasan me ya faru a shekaru baya. Hmm Nuratu ki bashi yar ki Jalilah, Allah ya bada zaman lafiya""Nahnah wallahi Mohan ba zai zauna da wata mace ba, Maimunari yake so ki saka baki ta barshi ya dawo da matar shi."
"Wallahi ba zai sake ta ba, Insha ALLAH ba zai sake miki yar ki ba na rantse da Allah." Ta fada jikinta na rawa. Cikin takaici Nahnah ta kalle ta, kafin tace mata.
"Dalla rufe min baki, Ni nace kar ku raba yaran nan amma sake baki da imani shine kika saka ya wulakanta yar mutane. Wallahi ki saka ido kiga abinda Ubangiji zai yi dake tunda baki da imani" shiru tayi cikin yanayin na jin haushi domin duk inda taje niman auren Mohan,kin bashi aure ake."Ni dai ku taimaka min don Allah"
"Hmm! Allah ya gani ba zan yarda ya maida min Y'a bazawa ba, amma babu yadda na iya tunda Nahnah kin saka baki.""Toh nagode"
"Nuratu kiyi hakuri"Kamar mahaukaciya ta fado d'akin, tare da shake wuyar Hajiya Latifah, tana kai mata duka.
"Kun kashe min yarinya na, wallahi sai kun mutu kuma, ba zan yarda ba." Ta fada tare da rufe Hajiya Latifah da duka, sosai ta haukace musu, sai da maza suka shigo aka fitar da ita.
VOCÊ ESTÁ LENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mistério / Suspenselove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....