BABI NA SITTTIN DA ƊAYA.

948 195 18
                                    

https://www.wattpad.com/1115269487?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=I5OLVif069AImr78w%2FlEumcHUFhhjB3GL%2BklLGDEG2mX72ge1I4j4pFlSrPzq7qgVMUX54J2flC9h4g6fi2m%2FvewJigtCSmbiskTJxpG%2BKNCCPD6AHygfMZwtAY2jz%2F0

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SITTTIN DA ƊAYA.

"Wato nice zai tozarta nice zai mai da ba kome ba, bayan faffutikar da nayi dan na same shi amma sake subuce min yayi, meye nayi mishi? Dama duk abinda yake fada min karya ce, dama ba zai tab'a tayani kuka ba, lallai yanzun na gane kuskure na."

        Sosai nayi kuka nayi bakin ciki tare da zama gurin, naki shiga cikin gidan domin kar a ce min ma nayi kuka dan na damu da Mohan, na san ina son shi amma ban zaci haka daga gare shi ba, wacece irin k'iyayya Ammyn take min haka da ta gwammace ta rabani da abinda nake so! Babu damuwa na bar mata Mohan ba zan kuma damuwa dashi ba.

      Dafa kafadana Mommy tayi bayan ta zauna.
"Bayan na tafi na barki zama cikin kad'aici yana daga cikin abinda Dr Khalid yayi yaki akan shi domin na tsani zama cikin jama'a, bana son magana da kowa. Kinsan yadda nake ji a lokacin. Ismail ya lalata min kome na, ya rabani da iyayena da kome nawa, uwa Uba na rabu da abinda na haifa, sau uku ina samun ciki da zaran nayi mafarkin abinda na bari zai lalace.

        Ina da yakinin hakkin abinda na bari yake bibiyata, ban wartsae da haka ba, kawai na fara fuskarta matsala daga Mahaifiyar shi, nasan yadda kike ji, amma ba zan iya cewa ga yadda naji ba, Maimunari nayi kuka na roki Allah ya dauki rayuwata da halin da nake ciki da Surukata, ta tsane ni dan ban haifa mata jiki ba,.gashi Yaron nata iya shi daya Allah ya bata, Maimunari ina gaya miki ne dan na yarda dake, amma a lokacin idan da zan ga mutuwa zan so shi sama da kuncin da nake ciki.

   Khalid sai da ya juya min baya sabida mahaifiyar shi, ba dan kome ba sai dan ya dakata farin ciki, nasha tambayar shi dalilin da yasa yake kin kulani. Murmushi yake kawai, domin karfi da yaji hajiyarshi ta dawo Paris, kuma haka yake kokarin ganin ya kyautatta mata amma baiwar Allah nan, bata fasa gasa ni ba. Haka na hakura da ita har Allah ya amshi rayuwar ta, ban tab'a fushi da shi ba, domin da ya fahimtar dani yana hana ne domin kar ta tsananin ta, k'iyayyar da yake min ya sani kara kaunar shi. Hajiya tayi fatan  taga abinda xan haifa sai gashi ina da cikin Benazir Allah ya amshi rayuwarta, kin san me? Tana da kirki amma saboda son da takewa D'anta yasata juya min baya, Maimunari duk tsanani yana tare da sauki, duk wanda kika ga ya zama wani toh kafin ya isa gurin waye shi.

   Na sha zama na duba wata irin ƙaddara ce take bibiyar rayuwata? Na zata kawai dan abinda ya same ni ba zan kuma fuskarta wani matsala ba, sai gashi bayan rasuwar Hajiya Khalid yan uwan shi sun kuma juya mishi tunani, su dai lallai yayi aure, a lokacin bani da wanda zai tsaya min sai Allah, nafi yarda da cewa hakkin abinda na bari yake bibiyata.

    A lokacin na kuma bazara rayuwar mutane, ba dan kome ba sai dan yadda nake kokarin na kyautattawa dangin Khalid haka bai saka sun kaunace Ni ba, idan har zamu je hutu Nijar haka xan hada musu shatara na arziki, amma ashe duk abinda nake  musu ba, bai musu ba su dai kawai Khalid ya auri yar dangi kin san yadda hankalina ya tashi, haka kawai suka kirkiro bala'i da tashin hankali a tsakanin mu, ina ji ina gani abu kadan zanyi ya fusata Khalid, gashi har lokacin Benazir nake goyo, gashi babu wani nawa, bani da kowa sai shi. Shima ya juya min baya.

    Munah ina ji ina gani  na zama mahaukaciya, karatun da yake biya min ya daina, dan inda nake  jin dadi ya katse min, sabida kawai yana son auren wata Yar uwars shi, ban kuma tsinkawa dashi ba, sai da aka gama kome ana jibi daurin auren ya gaya min, haka na saka shi a gaba nayi ta kuka, amma bai saurare ni ba,  haka suka yi al'amarin auren su. Ranar da ya tafi Nijar dakyar ya ajiye min abinda xan bukata na sati Uku, amma da ya tafi sai da ya share wata biyu, a lokacin na ga tashin hankali da damuwa, bani da kome sai da ta kai ina fita bakin hanya ina rokon abinda xan ci Ni da Yarinyana, sannan na kawo mana gida a girki.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora