🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_DambuSadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza...._*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya...._Gaisuwar wannan shafin naku ne baki dayan ku Makarantar BRRJI👏 Nagode sosai_
BABI NA SHA SHIDA.
Iskar bakin shi ya furza domin yasan dai duk abinda zai ayi almamoon namiji ne, dan haka ya juya tare da sallamar malamin, ya shiga cikin gidan. Yana me kara jin babu dad'i baki daya, ji yaƙe kamar yayi ta kurma ihu.
A yau yayi danasanin fara aikin soja, domin yana ganin kamar kasancewar shi a aikin ne ya ja mishi kaddararren wahala,haka ya taimakawa Mohan sannan ya koma bakin aikin shi dan bai ga dalilin da zai saka shi zama a jikin Mohan ba, tunda shi ya janyo haka.
***
Muna isa asibitin da gaggawa aka amshe ni, yana rike da gadon da ake turani har bakin kofar shiga dakin da za a duba ni.Tambayar shi nurse tayi yayi mata bayani, sannan ta shiga cikin dakin, suka mai da hankali akan duba lafiyar ta, rigar Jikinta suka nime tsagawa, likitan ya ce musu.
"Ku dakata ba sai an raba shi da kayan shi ba, idan aka duba daga wajen ma yayi."Inji likitan yana ƙoƙarin had'a alluran da zai mata, haka suka gama abinda zasu har suka sami nasarar farfaɗowa ta, amma take likitan yayi min alluran barci.
Lokacin da aka fito dani, mikewa Dan Ba'are yayi yana kallon su. Kamar me ciwon baki yace musu.
"Ya......ya.... Ya...."
"Yallabai da sauki ya samu barci, idan ya farka zuwa jibi zamu sallame shi"Gyada kai kai yake tare da kallon keken majiyanta, har dakin da aka kwantar da Almamoon ya shiga. Zama yayi yana kallon fuskar yaron, wanda kullum yake zagaye da saje, kusan ma dabi'ar shi, sajen har kusan kumatun shi. Yana barci kamar wani mage, ya samu auduga. Dan cuter face din shi ya kuma fitowa sosai, gwanin ban sha'awa.
A hankali ya shafa dan bakin shi nan (Ni kuwa nace bakin tsiwa ba🙄😩da bakar magana) haka yayi ta shafa bakin shi yana murmushi, bakin yayi mishi kyau dan karami kamar bana namiji ba, murmushi ya sake tare da shafa kanshi yana me kallon window dakin yana kallon mutanen da suke shige da fice daga asibitin.
Yana jin ina ma da ace Almamoon mace ce, da yau zai gabatar da kan shi sabida kar yayi sake reshe kama ganye, kuma idan ma bai yi haka ba, taya yana ganin dama zai wuce shi, murmushi yayi sannan ya zauna tare da riko hannun shi yana kara jin wani irin nutsuwa a tare da Yaron, haka kawai yake kara kallon nasibin yaron, yana kara jin yaron a cikin zuciyar shi lungu da sakon cikin zuciyar shi.
Wani irin bugun zuciya yake ji a duk lokacin da ya kalli fuskar yaron ji yaƙe kamar dan shi aka halicci Yaron,. Shafa kanshi yayi tare da jin wani sabon nutsuwa akan shi. Yaron baki daya yayi tafiyar bazata da rayuwar shi. Murmushi yayi.
---
Kallon shi tayi kafin tace mishi.
"Malam Ansar ko zaka kai Ni naga Mamoon ne zuciyata taki yarda da halin da yake ciki, ko zaka kai ni"Yadda ta damu sosai ya kalli Baba Mari kamar zai yi kuka, yace mata.
"Baba idan muka je ba lallai su barmu mu shiga ba, amma tashi muje"Babban mayafinta ta yafa, tare da bin bayan shi, har Jacader.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....